Still My Sister

8.9K 744 14
                                    

A cikin sati daya Aisha ta sake sosai a gidan Nura. A cikin satin nan sai da Nura a tabbatar ya cire fiye da rabin kunyar Aisha kamar yadda yayi alkawari, dan Aisha ita kanta har mamakin kanta take yi wai ita ce har zata iya shiga toilet suyi wanka tare da Nura. Babu abinda suke yi a cikin satin sai dai suyi sallah, suci abinci, suyi wanka sai kuma su baje kolin soyayyar su. Sai a lokacin Aisha ta kuma fahimtar hikimar Aunty na kin barin Zahra a gidan dan da tana nan kam da abubuwa basu gudana kamar yadda suke gudana a yanzu ba. Bayan sun cinye satin farko suka shirya suka shiga duk makotan su suka gaisa, suka kuma gabatar da kansu a matsayin sababbin 'yan unguwa, a take Aisha tayi kawaye sosai har sukayi exchanging numbers da alkawarin kawo mata ziyara suma. Bayan nan kuma Nura ya dauke ta ya kaita gidajen su Mami sukayi musu bangajiyar biki tare da karin godiya akan hidimomin da sukayi mata, Mami tace babu godiya tsakanin su ai an riga an zama daya.

Gidan Amir ne basu samu damar zuwa ba saboda basa nan daga shi har iyalinsa, anan Mami ta bawa A'isha labari asalin abinda ya faru da Amir bayan zuwansa Kaduna "ya samu iyayensa, and it is amazing, it is more than we hoped for, ashe Amir dan founder din H and H group of companies ne. I doubt in zai dawo Abuja da zama kuma yanzu, he belongs to Kaduna now, sai dai ziyara" sai ta gaya mata duk abinda ya faru in details (read *TAGWAYE*).

A'isha bata san tana kuka ba sai da aka gama labarin, sai kuma ta kama dariya tana share hawayen ta tana tuno kyakykyawar fuskar Amir, he is an amazing person with an amazing story and now he is having an amazing life, and she felt very happy for him.

Satin Aisha biyu a gidan Nura suka tafi Yola. Wannan shine zuwan Aisha Yola na farko kuma sosai taji dadin zuwan dan ta samu karba mai kyau daga 'yan uwan Nura, sai yanzu ta fahimci wani abu a tare da Nura, yana da zumunci sosai da sosai yana son yan'uwansa kuma yana kyautata musu, wannan yasa 'yan uwansa suke sonsa sosai kuma wannan son da suke masa shine ya shafeta, duk inda suka shiga kokari ake aga an faranta mata rai.

Innar Nura kam kunyarta take ji kasancewar Nura dan fari, dan haka inta zauna dakinta sai dai suyi zaman kurame, ita kunya Aisha kunya. Sanda zasu dawo Abuja kam sosai aka hada musu kayan tsaraba, baga 'yanuwa ba baga makota ba kowa so yake yaga ya farantawa Nura da matarsa, albarka kuwa ta ko'ina saka musu ita ake yi.

Da zasu tafi Aisha tace da Zainaba da Sa'adiyya kannen Nura su shirya su tafi tare tunda sunyi hutu, ai kuwa nan take suka kama murna suna tsalle, Nura kuwa sai hararar Aisha yakeyi ita kuma tayi kamar bata san yana yi ba. Sai da suka kebe yayi mata complain tace "to ai ba zama zasuyi acan ba, just for few days ne fa, kuma tunda muna da nisa in basa zuwa ta yaya zamu saba dasu?" Ya nuna mata shi dai kamar takura masa tayi amma kuma a idonsa taga alamar yaji dadi, yaji dadin cewa tana son 'yan uwansa har tana son ta saba dasu.

Basu dade da komawa Abuja ba su Aisha suka koma hutun sabon session, yanzu ta shiga year three, a lokacin ne kuma Nura ya sayi sabuwar mota. Kullum tare suke fita makaranta kuma su dawo tare, ko daga nesa ka hango Aisha da Nura kallo daya zakayi musu ka fahimci irin tsabagen kaunar junansu da suke yi. Aisha ma ta fara business dinta kamar yadda Mami ta shawarta mata kuma saboda yadda ta saukaka kudin sai ya zamanto nan da nan ta samu karbuwa a gurin mutane, kowa yaga kayanta yasan masu kyau ne sannan kuma ga kudin mai sauki sosai, ba cikin Abuja ba har states din da suke makotaka da su Aisha tana aikawa da kayanta, ballantana kano inda Aunty tayi ta shige da ficen da sai da taga ta kafa Aisha sosai a gurin mutane da yawa. Business din Aisha baya shiga karatunta sam, dan indai tana makaranta to bata daukar wayar data danganci business sai dai inta dawo gida ko kuma da weekend. Masu zuwa siyan kaya kuma har gida ko bata nan suna samun su Zainaba wadanda Aisha ta sakar wa komai na gidan su suke gudanarwa in bata nan kuma ta same su masu rikon amana sosai a bisa harkar gidan da kuma harkar sana'arta. Hutunsu yana gaf da karewa kenan akayi wa su Zahra hutu, nan take Aisha tayi ta naci tana tunawa Aunty alkawarin da tayi mata na kawo Zahra in sun sami hutu, da 'kyar, har sai da Nura ya kira Aunty da kansa ya taya Aisha roko sannan ta yarda cewa Hafeez zai kawo ta, Aisha kamar da zuba ruwa a kasa dan murna. Nura yana yi mata dariyar tsallen da take yi akan gado kamar yarinya yace "ke dai burinki shine kiga kin cika min gida fal da mutane" ta zauna tana haki tace "to ai su suna kasa, kai kana sama, babu ruwanka dasu in ba shigowa zakayi ba ko kuma in zaka fita".

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now