The Lucky one

8.6K 787 9
                                    

Ta sunkuyar da kanta kasa tana jin zuciyar ta na bugawa, Kamal is more than she ever dreamt of as a husband, amma kuma gashi a gabanta yana kuma yi mata maganar aure, ta dago kai tace masa "aure fa kace?" Yace "yes" ta hadiye yawu saboda makogwaronta da ya fara bushewa tace "me yasa za kace kana son aurena? Am not your type, kamar ka kafi dacewa da someone like....someone like Khadija, kuma kaga...." Ya katse ta "ban fa gane maganar da kike yi ba, you are not my type as in how? Saboda me kuma na dace da someone like Khadija?" Sai kuma ta kasa bashi amsa, ya tsare ta da ido yace "ina sauraren ki" tace "Khadija is beautiful, am not".

Ga mamakin ta sai taji yana dariya, ta dago kai tana kallonsa, sai da ya gama dariyarsa sannan yace "ke waye ya gaya miki cewa you are not beautiful? A ina kika ji wannan maganar?" A hankali tace "na sani, tun ina yarinya na sani, mutane da yawa sun sha gayamin cewa am ugly" ya sake katseta cikin mamaki yace "and you believe them? Because ni ban yarda ba, you may not have khadija's type of beauty but you are not ugly, kiyi min alkawarin ba zaki kara fadar irin wannan mummunar maganar a kanki ba, you are beautiful on the inside and the outside, wannan kuma shine abinda ya jawo ni gareki, na fara jin sonki a raina tun kafin inga fuskarki, bayan naga fuskarki kuma I only love you more, saboda you are exactly what I want as a wife. Ba zan boye miki ba, nayi 'yammata sosai, tun ina secondary school nake yammata har yau, kuma most if not all of them have khadija's type of beauty, dan haka na sansu, nasan yadda suke, most of them basu da hali, wanda ni a ganina shine abu na farko da ya kamata mutum ya duba in yana neman matar aure, society ta riga ta gaya musu cewa they are beautiful dan haka sun saka a kansu cewa they can get whatever thay want, wannan kuma ba halin mace ta gari bane ba, ban ce duk kan su ba, amma most of them haka halinsu yake, am telling you from experience. Abokaina da yawa sunyi aure, kuma da yawa sun auri mata masu kyau irin na Khadijah, amma after some few years a cikin kashi goma kashi biyar auren ya mutu, kashi uku kuma kullum suna cikin complain kashi biyu ne kawai suka yi dace. Ina so mu gina auren mu ni dake a bisa foundation mai kyau, ba wai mai kyalkyalin banza ba, foundation mai 'kwari nake so, wanda zamu gino tarbiyyar 'ya'yan mu akai. Kin amince?"

Ta ce "maganar aure fa kake tayi Kamal, I don't even know anything about you sai sunanka, kaima kuma haka, baka ganin ya kamata mu ajiye maganar auren nan mu fara fahimtar junan mu tukunna?" Yayi murmushi yace "kin ajiye maganar Khadija kenan ko?" Tayi murmushi kawai, yace "OK, ni idan da ace son samu ne da direct gurin abbanki zan tafi da maganar mu, saboda ni dai kinyi min a matsayin mata ta, amma tunda na lura cewa ni banyi miki ba har yanzu, to zan dakata da zuwa gurin Abba, zan dai nemi alfarmarsa yake barina ina zuwa zance gurinki har lokacin da zaki ce nayi miki din, amma duk da haka a ra'ayi na bana son doguwar soyayya before aure, gwara ayi soyayyar kadan in yaso in anyi auren sai a dora da mai ma'ana, kin fahimce ni?"

Kai kawai ta gyada masa, ya cigaba "Ni sunana Kamaluddeen Usman, ni haifaffen garin yola ne ta jihar Adamawa, mahaifana duk fulani ne dan zuwa na garin nan ne na iya hausa sosai, though har yanzu koya nake yi. Nine auta a gidan mu, wanda kusan duk maza ne. Abinda ya kawo ni garin nan ba wai karatu bane ba, akwai Yakumbo na, kanwar mahaifina, itace tayi aure a garin nan shekara da shekaru, cikin ikon Allah kuma sai ita Allah yayi ta bata 'ya'ya mata, to tun sanda aka haife ni ta dauki so ta dora min har a gida suke ce min ɗan Yakumbo. Bayan na gama secondary school dina a yola sai na fara sana'ar dinki tare da yayana a can, har Allah yasa na kware sosai nake yi, to daga baya kuma sai Allah yayi wa mijin ita Yakumbo rasuwa, ita kuma saboda sabawa da tayi da garin nan gashi 'ya'yanta duk sunyi aure anan shine taki komawa gida amma sai ta roki mahaifina akan ya bar mata ni in dawo gurinta dan in taimaka mata wajen juya dukiyar da mijinta ya mutu ya bar mata, tunda bata da d'a namiji. To wannan shine dalilin zuwa na garin nan. Ta rike ni kamar danta, suma yayanta sun rike ni kamar dan 'uwansu, sun sakar min dukiyar su gaba ki daya ina juyawa, ni kuma ganin haka shi yasa na bude shagon dinki nake yi in my free time, saboda in ringa tunawa kaina cewa dukiyar da nake gani fa ba tawa bace ba, abinda na samu a shago shine nawa. Yanzu dai duk 'ya'yan yakumbo sunyi aure saura 'yar autar ta Maryam, wadda yanzu take kokarin kammala secondary school dinta. Bayan na dawo nan shine na shiga makaranta saboda nima in dan yi degree din nan na zamani. To ashe rabon zan samu mata a can ne, na samu abinda yafi degree muhimmanci" ta danyi dariya shima ya taya ta, sannan yace "to saura ke, tell me who is Aisha Zayyan" tace "there is nothing to tell, am just me, anan garin aka haifeni anan na girma anan nayi karatu, babu wani abu, except that my mother died months ago" yace "ya Salam, am sorry Humaira, Allah yayi mata rahama" tace "Ameen" tana jin kamar hawaye zai zubo mata, har yau mutuwar Umma fresh take jin ta, gashi kuma yanzu abin farinciki yazo amma babu uwar da zatayi sharing with.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now