The Promise

7.9K 691 6
                                    

Ranar weekend ne dama, dan haka duk suna gida, Aisha tana kitchen tana girki, Umma da Khadijah suna palour a zaune, Khadija tana ta chatting dinta a waya. Abba ya shigo suka gaishe shi ya amsa yace "ina Aisha?" Umma tace "tana kitchen" daga haka ya juya ya fice, sai ihun Aisha suka jiyo daga kitchen, da sauri Umma ta fita ta tarar Abba ya saka Aisha a gaba sai jibgar ta yake tamkar Allah ya aiko shi, abinda bai taba yi ba, da kyar Umma ta kwace ta dan sai da ita ma ta samu nata rabon dukan. Aisha kuka take kamar ranta zai fita, Khadija kuwa ko fitowa tsakar gida ba tayi ba dan tasan abinda ya faru, tunda tana da labarin zuwan abokin Abba tun kafin yazo din.

Ana cikin haka suka ji sallama, yakumbo Sadiya, yaya ce a gurin Abba, su biyu iyayensu suka haifa. Tana shigowa da salati ta ajjiye ƙullin ledar hannunta ta karaso tana rike Abba. "Zayyan baka da hankali? Me tayi maka zaka kasheta?" Yana huci yace "gwara in kasheta in huta Yaya, da ace 'yar cikina ta jawo min abin kunya gwara ace babu ita a duniyar baki daya" Gwoggo tace "me yayi zafi haka? Wanne abin kunya zata jawo mana?" Sama sama ya bawa gwoggo labarin abinda ya faru da kuma rahoton da aka kawo masa, ta saka salati tana tafa hannaye "yau na ga abinda yafi ƙarfina ni Halima, yanzu yarinyar nan dama ashe munin ki ba'a fuska kadai ya tsaya ba, yanzu dama har zuciyar ki mummuna ce ke? To wallahi ki gyara tun kafin lokaci ya kure miki. 'Yar uwar taki zaki yiwa bakin ciki da Hassada? To mu dai wannan ba halin mu bane ba, daga kamannin har halin ba namu kika dauko ba"

Umma ta bita da kallo dan tasan abinda take nufi, amma da yake ita ba mai son rigima ba ce sai tayi shiru bata tanka mata ba. A lokacin Khadija ta fito daga palour da gudu ta fada jikin gwoggo tana kakalo hawayen ƙarya tace "gwoggo kinga abinda Aisha tayi min ko?" Nan gwoggo ta fara jijjiga ta alamar rarrashi tana cewa "rabu da ita 'yar arziki irin albarka, aniyarta ta koma kanta, shi munafunci ai dodo ne mai shi yake ci, gashi nan tun yanzu ta fara gani a kanta".

Aisha ranar har dare tana kuka, ba wai dukan da akayi mata ne ya saka ta kuka ba, bakin cikin sharrin da akayi mata ne, yanzu ta tabbatar da cewa ko ta fadi cewa ita ta rubutawa Khadijah ssce ba za'a yarda ba, cewa za'ayi bakin ciki take yi mata, wanda shine abinda yafi komai bata mata rai.

Ranar Monday suka shirya zasu fita Abba ya kalleta yace "ina zakije? Ai kin gama zuwa gurin abincin nan kenan har abada, da wani nikab dinki na munafurci" ya tasa keyar Khadijah suka fice. Aisha bata ce komai ba ta juya ta koma daki ta cire hijab dinta da nikab ta tsaya a gaban madubi tana kallon kanta, tana kallon abinda yayi sanadin da Abba yafi son Khadijah a kanta, sanadin da bata karatu a yanzu, sanadin kuma da yasa a yanzu aikin da ta fara so ta fara sabawa dashi shima ta rasa. Amma kuma babu abinda zata iya yi akan hakan kamar yadda duk masu kushe ta da yi mata ba'a babu abinda zasu iya yi akan hakan.

Da Mama taji shiru Aisha bata zo ba sai ta kirata a waya, Aisha tana ganin kiran taji hawaye ya taho mata, ta katse kiran dan ba zata iya dauka ba. Sai ga Mama ta kira a wayar Umma, Umma ta dauka suka gaisa tace "Aisha kuwa lafiya? Allah yasa dai ba rashin lafiya take ba" Umma tace "hmm, ai Aisha bana jin zata sake zuwa gurin ku" nan ta bawa Mama labarin duk abinda ya faru.

Nan take Mama hankalinta ya tashi tayi ta rantsewa Umma cewa karya Khadija take yi, Umma tace "na sani, amma yaya zanyi? Kiri kiri nasan Aisha ce da gaskiya amma babansu ba zai saurare ni ba" Mama tace "amma kuwa kin bani kunya, shi din waye da mace ba zata juya shi ba? Kuma yanzu shiru din da kikai kamar kin bawa ita Khadija lasisin cigaba da abinda take aikatawa kenan, idan ta lalace ai tare zaku yi kukan ke da shi". Aisha tana gefe duk tana jin hirar da suke yi, ranta yana kara yi mata zafi saboda tasan ummansu ba zata iya tabuka komai ba sai dai ta shiga daki tayi kuka.

Aisha ta tashi ta koma dakin su ta zauna tana lissafi, nan take ta yanke shawara, ta dauko wayarta ta kira number din Nura, har ta katse bai dauka ba, ta sake kira still bai daga ba, sai ta ajiye wayar ta kwanta a gefe, bata jima ba sai ga kiransa ya shigo, ta dauka da sallama yace "ranki ya dade, sai yau kika tuna da cewa na baki number ta ko?" Direct tace masa "Nura kace kana so ka zama friend dina ko?" Yayi dariya yace "ai na riga na zama ma, ke ce har yanzu baki sani ba" tace "to in da gaske kake ina so kazo gidan mu in an jima, akwai maganar da nake so muyi da kai" da sauri yace "Allah ya kaimu. Amma bansan address dinku ba" tace zata turo masa a text, daga nan sukayi sallama. Suna ajiyewa kuwa ta rubuta masa text ta tura masa.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now