Dr AbdulRazak

9.4K 743 19
                                    

An saka wa Khadija takunkumi, ta daina zuwa makaranta, zancen ma an hana ta fita, Abba yace ta gayawa samarin ta duk wanda yasan da gaske aurenta zaiyi to ya aiko iyayensa.

Wannan yasa Khadija ta tsinchi kanta a rayuwa tamkar a cikin kurkuku, da kyar wani lokacin take samu in Abba bayanan Umma ta barta ta ɗan fita, shima da sauri zata yi abinda zatayi ta dawo gida, kullum jinta take yi tamkar a prison, bata da walwala sam, kullum baƙin cikinta ƙaruwa yake yi musamman in taga Aisha ta shirya ta fita, gashi kullum Aisha sake samun buɗi take yi, Abba yana ta tara mata kuɗaɗen da Mama take bata.

Ita kuma Khadijah taƙi cewa da samarin nata su fito, duk kuwa da tasan a cikinsu akwai wanda ko gobe za'a daura musu aure a shirye yake dan akwai wadanda suke sonta da gaskiya, amma ita ji take a ranta duk basu yi mata da aure ba.

A wannan lokacin ne Dr AbdulRazak ya shigo cikin rayuwar su. Dr AbdulRazak babban mutum ne ma'aikaci a federal ministry of education. A wannan shekarar yana daga cikin wadanda aka turo daga ministry zuwa federal university dutse domin accreditation na wadansu courses. Tun kafin team din nasu suzo an riga an san da zuwan su dan haka an gama shirya duk abinda ake bukatar domin taryarsu, a cikin shirin da akayi musu har da na abinci wanda aka bawa Mama kwangilar yi musu abinci sau uku a rana tare da snacks da zasu ke ci in-between, ita kuma direct ta damka hidimar a hannun Aisha.

Babu bata lokaci Aisha ta rubuta menu na abinda zata yi musu, sannan ta ja Sa'adatu suka tafi kasuwa suka siyo duk abinda basu da shi kuma suke buƙata. Ranar da baƙin zasu so tun kafin su karaso har ta gama abinda ta shirya musu na lokacin ta kuma aika musu da shi zuwa masaukin su, haka ta cigaba da yi har suka gama kwanakin su suka tafi.

Bayan sun tafi ne sai ga sako daga VC zuwa ga Mama, kamar ranar nan wanda aka aiko ya kira Mama gefe sannan ya fara yi mata bayanin aiken nasa. "VC ne ya aiko ni Hajiya Maryam, yace yana yaba muku kwarai da gaske a bisa kokarin ku, baƙin sa sunji dadin abincin ku sosai wanda hakan yana daga cikin dalilan samun nasarar wannan accreditation din da muka yi. Sannan kuma a cikin su akwai wani maaikacin ministry of education wanda a yanzu haka akwai program da suke gabatarwa na taimakawa yara masu talent na musamman akan wani bangare wanda ba formal ba, kamar mawaka, masu zane, da masu girki. To jin cewa ƙaramar yarinya ce take wannan girke girken sai yace ayi miki magana kiyiwa iyayenta da ita yarinyar magana idan sun amince za'a saka ta a program din, za'a kai ta kasar waje tayi karatu akan girki, in ta dawo kuma za'a bata jari yadda zata hada ilimi da kuma talent wajen gabatar da girke girken ta. Ki tambaye su, idan sun amince accreditation team din zasu dawo nan da lokaci kadan zasu yi wa wasu departments din, in sun dawo zai ganta yayi mata interview"

Mama tun tana gyada kai sanda ya fara maganar har ta bude baki cikin jin dadi sannan ta saka hannu ta rufe bakin "alhamdulillah, alhamdulillah, masha Allah" sai dai duk murnar da tayi akan maganar bata gayawa A'isha ba tafi son ta fara gayawa iyayenta tukunna.

Da weekend suna gida gaba daya, Abba ma yau bai fita ba ya samu wani film yana kallo. Suna zaune a palour suna kallo gabadaya sai ga Mama ta shigo da sallama. Bakin ta kamar gonar auduga, Umma tayi mata sannu da zuwa ta bata gurin zama, bayan sun gaisa ne Umma tace "wannan fara'a haka Maryam, ni ma kin saka ni sai washe baki nake yi tun kafin in san dalilin fara'ar taki"

Mama tayi 'yar dariya tace "to Rabi'a ba dole ki ga bakina ya kasa rufuwa ba? Kinsan labarin da nake tafe dashi kuwa?" Umma tace "sai kin gaya min, kujerar makka aka baki kyauta?" Mama ta sake dariya har tana tafa hannu tace "wacce irin kujerar makka? Ai abinda na samu yafi min kujerar makka daɗi tunda dai naje na sauke farali. Akan ƴata Aisha ne, abin arzikin ita ya samu, kinga kuwa gaba ki dayan mu abin ya shafa" Abba yana jin haka ya saka pause a kallon sa ya juyo yana kallon Mama, nan ta kwashe duk abinda ya faru ta gaya musu.

Tunda ta fara maganar babu wanda ya katse ta, Umma ta zaro ido tana kallonta da alamar tsoro, Abba ya bude baki farin ciki fal a idonsa, Khadijah kuma baƙin ciki ne karara a rubuce a fuskarta, Aisha kam kanta yana ƙasa amma kirjinta sai bugawa yake kamar zuciyar ta zata fito.
Abba ne ya fara magana "kai Alhamdulillah, Wannan abu yayi kyau, ai tana dawowa tattarawa zamuyi mu koma Abuja, a can zata bude gidan abincin kuma in ta bude ai dole zata buƙaci mai kular mata dashi"

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now