Khadijatul Kubra

8.4K 820 43
                                    

Aisha ta sake wani murmushin jin dadin tace "of cause zan kaiki gurinsa. Amma kafin nan zan baki labarinsa. Sunansa Kamal. Shine mutum na farko daya fara nunamin pure soyayya a lokacin da kowa yake guduna, a lokacin da ni kaina nake kunyar nunawa jama'a fuskata saboda gudun wulakanci, shine mutumin daya fara kira na da kalmar beautiful, shine mutumin daya fara kallona beyond my ugly face into my beautiful soul. Shine mutumin dana fara so a rayuwata.

Humairah tayi murmushi tana jin son abbanta yana karuwa a zuciyarta. Ta zame ta kwanta a carpet ta dora kanta a cinyar Aisha, ita kuma Aisha ta fara zayyana mata for the second time labarin asalinsu ita da Khadija, da labarin haduwarsu da Kamal da kuma abinda ya biyo baya, sai kuma ta bata labarin abinda ya raba Khadija da gida, da kuma abubuwan da suka faru a gidan bayan tafiyar tata da halin da Babanta yake ciki a yanzu.

Danshin da taji a cinyar ta yasa ta fahimci Humairah kuka take yi, bata hana ta ba bata rarrasheta ba ta barta tayi kukanta danshi kuka yana sanyaya zuciyar mutum. Humairah ta juyo fuskarta tana kallon fuskar Aisha tace "all my life, nasan cewa Mamana is a bad person, amma kullum ina tursasa zuciyata akan tayi mata azuri saboda kullum ina sakawa a raina cewa tana yin rayuwar da tayi ne bisa dole, ba wai zabinta bane ba, kullum ina ganin kamar yanayin rayuwa ne ya kaita inda take ba wai ita takai kanta ba. Bansani ba ashe son zuciyarta da son kanta ne ya kaita. Bansani fa ashe wuka ta dauka ta dabawa mahaifina sannan ta dauke ni a cikin tsumman zanina ta tafi dani yawon duniya ba tare da tayi tunanin wacce rayuwa zan fuskanta ba, ashe duk wahalar na nasha nasha ne sabida mamana was so selfish babu wanda ta damu dashi sai kanta. Ashe mamana zata iya aikata abinda ta aikata miki? Abinda tayi wa babana? Abinda tayi min? Yes, she really is a devil".
A dakin da aka kwantar da Khadija ta fara dawowa haiyacinta. What a dream? A cikin baccinta tayi mafarki wai taga 'yarta, gudan jininta, wai taga Baby. Kuma a mafarkin nata wai babyn tare ta gansu da Aisha. Aishan ta, 'yar uwarta. Amma kuma Aishan ba wacce ta sani bace ba, wannan aishan madaddiyar mata ce mai zaune a hadaddan gida a abuja. A mafarkinta wai taga mutane biyun da suka fi kowa sonta a duniya, a mafarkinta wai taga mutane biyun da tafi zalinta fiye da kowa a duniya.

Inama ina ma! Ina ma dai mafarki zai iya zama gaskiya. Ina ma Allah zai bata chance din ganinsu ko dan ta samu ta roke su gafara, ko dan ta samu su yafe mata ko ta rage tarin zunubanta, ko ta samu sassaucin wannan muguwar rayuwar da take ciki. Ita tasan laifukanta ne suke ta hunting dinta, kuma tasan ba zasu taba barinta ta samu sassauci ba har sai ta nemi gafarar wadanda ta zulunta. Amma hakan ba mai samuwa bane ba, inta nemi gafarar Aisha da Baby Kamal kuma fa? Shida ta raba da duniya baki daya?

Wannan shine dalilin da yasa tana fitowa daga prison ta bazama neman Humairah, saboda tana ganin itace wadda tafi zalunta fiye da kowa a duniya, maybe, just maybe, in ta yafe mata zata samu Allah ya sassauta mata wannan axabar rayuwa.

Wani irin sanyi taji yana shigarta, ita dai tasan ba lokacin zanyi bane ba asali ma zafi akeyi yanzu, amma wannan sanyin yafi kama da sanyin hunturu. Sai a lokacin ta fara zama conscious of her surrounding, shimfidar da take kwance a kanta, kamshin da take shaka a hancinta. Ta bude idonta da sauri kirjinta yana bugawa. A wani daki ta ganta a kwance a kan gado, ta karewa dakin kallo, babu tarkace sam a dakin daga furniture's, curtains sai carpet a gaban gado sai ACn da take busa sanyin da take ji a jininta. Amma ko curtains din ka kalla kasan naira tayi magana a ciki. Ina ne nan? Me take yi anan? Waye ya kawo ta nan? Ta runtse idonta tana son ta saisaita tunaninta. A karshen mafarkinta taga hoton ta a gurin matar data kira kanta da Aishan ta, a lokacin ne kuma ta fara jin jiri yana dibanta. Ya Ilahi! Kar dai ace ba mafarki tayi ba? Ta mike zaune da sauri sannan ta zuro kafafuwanta kasa, ta lura da yadda kafafuwan nata suka zama odd akan carpet din. Kofa biyu ce a dakin, ta fahimci daya ta toilet ce daya kuma ta fita waje. Indai har ba har yanzu mafarkin take yi ba then Aisha da Humairah suna nan tare da ita a cikin gidan nan. Me ya rage mata kuwa in banda ta ruga taje ta nemi gafarar su?

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now