God's Choice

9.5K 831 28
                                    

Washegari Aisha ta tashi duk zuciyarta babu dadi, ga kirjinta yayi mata nauyi sakamakon kukan da tasha jiya, bakin cikin ta kuma shi Nuran data samu ya dawo tana sonta gaya masa matsalarta ya bata shawara shine ya wani kashe mata waya kuma bai kira ta back ba.

Tayi sallar assuba ta godewa Allah sannan ta roke shi akan ya bata hakuri ya bata ikon karbar kowanne zabi yayi mata dan tasan shine mafi alkhairi a gareta. Tayi wanka ta shirya sannan ta fita kitchen, ta tarar already Mami da Atika suna kokarin sallamar yara zuwa makaranta. Abdallah yana zaune akan stool sai surutu yakeyi ya hana Mami aiki, shi ba baki ba dan haka dole sai ta juyo ta kalleshi zata san me yake cewa kuma dole sai ta bashi amsa, tana juyawa zai dauki chokali yayi ta dukan worktop yadda dole sai ta juyo ta kalleshi. Aisha tana shigowa Mami tayi ajjiyar zuciya tace "ga mutuminki nan na barki dashi" Aisha ta jawo kujera ta zauna suka kama hirarsu, har da dariya suna tafawa dan yanzu ta kware sosai a yaren Abdallah.

Abdallah shi ya dauke mata hankali daga damuwarta, taji ranta yayi mata dan dadi har ta gama shiryawa ta fita makaranta, amma tana zuwa makaranta komai ya sake dagule mata, dan lectures din ma ba ganewa take yi ba, ga Nura yaki kiranta ita kuma pride ya hana ta ta kirashi but she desperately wanted to see and talk to him, at least to get things out of her head. Har suka gama lectures babu labarinsa, kuma tasan shi yake nemanta most of the times in yasan ta gama lectures. Ta sauke pride dinta ta kirashi amma har wayar ta katse bai dauka ba, taji haushi sosai, haushin kanta take ji akan me yasa ta kirashi.

Zainab na kusa da ita tace "ke kuma yau lafiyarki kike ta tsaki ke kadai? Me yake damunki tun safe sai wani cika kikeyi kina batsewa?" Aisha tace "bari kawai Zainab, ba zaki gane ba" Zainab tace "bazan gane yaƙi daukan wayarki ba?" Aisha tayi sauri ta kalleta, tace "yes, na gani ai shi kika kira yanzu bai dauka ba" Aisha ta sake yin tsaki ta mike ta fita, kowa ma haushi yake bata yau.

Amir yazo daukanta dutifully kamar yadda ya saba yi kullum. Ta taho ita kadai ta shiga motar ta gaishe shi, kallo daya tayi masa tasan akwai abinda yake damunta amma itama tana fama da nata matsalolin dan haka ta dauke kai, ya amsa yana studying fuskarta shima, ya tayar da motar suka tafi. Sai bayan sun hau titi sannan yace "yau ina dan rakiyar taki?" Ko kallonsa bata yi ba, yayi dariya yace "ko fada kukayi ne yau? Shine ni kuma za'a huce a kaina?" Ga mamakinsa kawai sai gani yayi ta saka kuka, kukan da take rikewa tun safe, da sauri ya saka signal yayi packing a gefe yana kallonta tana ta kukanta, ya dauko kwalin tissue ya mika mata sai da ta gama kukanta sannan ta goge hawayenta ta kalleshi da kumburarrun idanu tace "am sorry" yace "what happened?" Dama me neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, dama neman wanda zata gayawa matsalolinta take yi kuma Amir already know alot about her dan haka ta gaya masa komai, ta gaya masa zancen Hafeez da zancen Dr, ta kuma bashi labarin wayar da sukayi da Aunty da yadda sukayi da Nura.

Ya gama jin bayananta kaf sannan ya sake mika mata tissue dinta goge fuskarta sosai. Ya tayar da motar suka tafi sannan yace "thank you for compiding in me. Yanzu na fahimci dalilin da yasa har yanzu ban samu amsata ba" tace "I didn't answer you because I don't know what to say to you. It is not possible. Am sorry" ya gyada kansa yace "I understand" suka cigaba da tafiya sannan yace "So Nura have finally come out to light kenan. I told you yana sonki, kuma na tambayeki ko kina sonsa amma baki amsa min ba" ta girgiza kanta tace "Nura bai taba cewa yana sona ba" yace "ke fa? Kina sonsa?" Ta juyar da kanta tana kallon window tace "what does it mattar now? Abinda nake so da abinda bana so doesn't matter. Abinda nake fata shine Allah ya bani ikon karbar kaddara ta". Sai da yayi packing ta juyo tana kallon sa sosai sannan tace "so, kai fa? Me yake damun ka?" Ya dauke kai gefe kamar mai kokarin boye fuskarsa yace "kar ki damu dani, I will be fine" ta ki fita tana cigaba da kallon sa, tana jin zuciyarta tana breaking for him but he knew for sure that he is a tough one. Ya juyo yana kallonta ya sake cewa "I will be fine" ta gyada kai ta bude kofa ta fita.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now