Father's Love

8.5K 825 32
                                    

Aisha ta mike tsaye tana kallon Humairah sannan tace "Ina ta tafi?" Humairah tace "Dutse. Cewa tayi ta koma inda ta fito, Dutse shine tushenta dan haka can ta koma" nan take fuskar Aisha ta washe, hakoranta suka bayyana dan nuna farin cikinta tace "why didn't I think of that before? Khadijah a yanzu babu abinda yake gabanta sai neman yafiyar wadanda take ganin ta batawa, ke ce a farkon list dinta, sai ni sai Abba, sai Kamal wanda da ta dauka bashi da rai. Ta samu tawa, she tried getting yours, yanzu Abbane next, of cause can ta tafi" da sauri ta wuce Humairah wadda ta sunkuyar da kanta tana jin babu dadi abinda tayi wa mamanta, mamanta da babu abinda bata yi ba saboda ita, ji tayi babu abinda take so kuma kamar taga maman nata ta rungume ta ta gaya mata ta yafe mata ita ma kuma ta nemi yafiyar ta.

Daga inda take tsaye tana jiwo Aunty Aisha tana waya daga palour. "Assalamu Alaikum Abba. Barka da yamma" sai kuma tayi shiru tana jiran taji ya fara mata fadan me yasa Khadijah ta taho gurinsa bayan yace kar ta taho, amma maimakon haka sai taji ya kama tambayar ta ko ta kai Humairah gurin Kamal? Tace a'a, nan take ya fara fadan me yasa ba ta kaita ba? "ni na rasa number sa ne da tuni na kira shi yazo ya dauki 'yarsa, wanne irin jan rai ne wannan marar ma'ana? Mutum shekara da shekaru yana neman 'yarsa kuma yanzu an ganta amma a kasa sanar dashi? Kunyi masa adalci kenan?" tayi shiru, itama tasan bata kyautawa Kamal ba amma kuma tana so ta fara daidaita tsakanin Khadijah da Humairah ne, bata son ta kai ta gurin Kamal ya zamanto ta kara nesanta tsakanin su. Tasan in dai Humairah taje hannun Kamal to ikon Allah ne kadai zai saka ya bari Khadijah ta kara saka ta a idonta.

Tace "insha Allah Abba a cikin satin nan zan kaita Yola da kaina, but first things first, Khadijah tazo nan?" sai da yayi shiru kamar bai jita ba sannan yace "Khadijah kuma?" ba ta bashi amsa ba saboda yadda taji zuciyarta ta karye, duk wani hope data samu sanda sukayi  magana da Humairah ya fara narkewa yana barin jikinta, wani sanyi yana maye gurbinsa. Cikin rawar murya yace "Khadijan ba tana gurinki ba kika ce? Bana ce karta zo nan gurina ba bana son ganinta?" Aisha ta zauna a edge din kujera tace "Abba Khadija 'yarka ce. Yes she is my sister but she is also your daughter, your responsibility. Nura yace ta bar masa gida kai kuma kace kar tazo gurinka to ina zata je? Koma gurin wa zata je ai bayanka yake Abba. Yanzu ta bar nan gidan kamar yadda Nura ya bukata, mun dauka gurinka ta taho kuma gashi kace mana bata zo ba, to ina ta tafi kenan? Baka ganin in ta koma 'yar gidan jiya ba laifin mu bane ba? Mu da ya kamata mu kula da ita mune kuma muka sake tunkuda ta?"

Cikin in ina ya ce "Khadijah ai ba yarinya bace ba. Duk abinda tayi ko take yi tana sane, kuma kanta tayiwa ba mu ba, in ma ta koma ruwa mu tunda Allah ya gani munyi iyakacin kokarin mu a kanta, babu wanda ya isa ya shiryar da wanda Allah ya batar" Aisha tace "Abba wannan Khadijan ba wadda ka sani bace ba, wannan Khadijan is a changed person, ba zaka fahimta ba sai ka ganta da idonka, sai kaga yadda duniya ta mayar da ita. Bata da wani buri a gabanta irin neman gafarar wadanda ta bata wa. Ta bar nan tun safe, maybe tana hanya, maybe kuma ba nan ta taho ba, amma ni dai ina rokar mata afuwa a gurinka, ina kuma rokon ka bata dama ta roke ka gafara, kuma ka bude zuciyarka ka yafe mata ba domin halinta ba sai domin saka ran gafara daga gurin ubangiji baki daya" tana gama magana ta kashe wayar ta jingina kanta a jikin kujera, wani bari na zuciyarta yana bata hope din Khadija tana kan hanya wani barin kuma akasin haka.

Tayi tunanin kiran Aunty Bilki amma sai ta fasa, dan tasan cewa tun suna yara babu jituwa tsakanin Khadija da aunty Bilki, kuma ita tun zuwan Khadija gidan tun sanda taga yanayin da Khadijan take ciki ta yanke shawarar ba zata gabatar da ita a gurin dangi ba sai ta koma haiyacinta tukunna sannan zata kaita kowa ya ganta. Amma kaddara ta riga fata. Dan haka yanzu indai har Khadijah dutsen ta tafi da gaske dole kowa zai san zancen dawowarta. Dan haka ta kudure a ranta cewa indai ta samu Khadijah to zata shirya taro ta kira kowa ayi solving komai. Har Kamal.

Humairah tana jin duk yadda ta kasance tsakanin Aisha da Abba. Duk da bata jin abinda Abban yake cewa amma ta fahimci cewa maman ta bata je gida ba. She may be on her way kamar yadda Aisha ta fada but then she may not. Anya tayi wa mamanta adalci kuwa? Anya tayi wa kanta adalci kuwa? Anya duk a cikin labarinsu da akwai wanda yasha wahala kuma har yanzu yake shan wahala irin mamanta? Ta zauna a bakin gado ta rufe bakinta da hannayenta tana kokarin hana kanta rushewa da kuka, ta dauko handbag dinta ta fito da wayarta ta kira number din Al'ameen. Me yasa kullum in tana cikin damuwa shine mutum na farko da take gayawa? Yana dauka tace "Ya Ameen Mama ta tafi. Ta tafi ba tare da ko dumin jikinta naji ba".

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now