The Orphan

8.4K 748 44
                                    

Cikin Aisha yana wata bakwai doctor yaga girmansa yayi yawa dan da kyar take tafiya ya matsa mata lallai tazo ayi mata scanning, duk da dai yana kyautata zaton twins ne amma so yake yi dai ya tabbatar. Sannan kuma scanning din ya zama dole dan aga lafiyar cikin saboda gujewa samun matsala musamman lokacin labour.

Tana kumbura tana turo baki haka Nura ya lallabota suka taho akayi mata, alas, babies guda biyun ne kuwa. Sai a lokacin da Aisha ta ga babies dinta a screen sannan ta fara jin feelings game da cikin, tana kallonsu suna ta wasansu kawai sai hawaye, ko a haka ubangiji ya barta ya gama mata komai. Da kyar ta bari doctor ya kashe screen din wai ita bata gama ganin su ba. Sai a lokacin sannan ta bari Nura ya fara yi mata siyayyar haihuwa, ai kuwa kudi kawai yake narkarwa har sai data ce masa ya isa haka. Ta warware sosai yanzu babu abinda take yi sai addu'ar sauka lafiya da kuma nemawa yaranta albarkar duniya da lahira. Sai da cikin ya cika wata tara sannan suka je asibiti aka kunce bakin mahaifar sannan sai a jira labour ya zo da kansa.

Ranar da zata haihu tun da safe ta fahimci abin nesa yazo kusa amma bata gayawa Nura ba har ya gama shirinsa ya tabbatar babu abinda zata bukata sannan ya tafi makaranta tare da jaddada mata cewa ta tabbatar cewa slightest change in taji zata kirashi a waya, tayi masa alkawari yayi kissing dinta ya tafi. Yana tafiya ta duba jakar tafiya asibitin data hada ta tabbatar komai yana ciki. Tayo alwala tazo tayi sallar neman sa'a a gurin ubangiji, ta jera adduoi sosai a kanta, mijinta, babies dinta da al'ummar musulmi baki daya. Tana kan sallayarta har saida taji abinda hausawa suke cewa za'ki ya fara fito mata sannan ta tashi ta nade ta. A lokacin da haihuwa tazo miki an fi son ki kadaice kanki a gurin da babu mutane, babu hayaniya preparably ma ace babu haske sosai. Wannan yana taimakawa wajan saka nakuda tayi progressing da sauri. Mostly in mace ta fara labour to da zarar anzo kanta ana ta hayaniya ko kuma an kaita asibii inda yake cike da mutane da nurses suna ta hira ga sauran masu haihuwa wasu na ta kuka to mostly sai kiga haihuwar ta koma. Wannan animalistic instinct ne. Da zarar anzo kanki ana hayaniya to jikinki zai yi reading environment din ne as unsafe, gani zaiyi kamar da kin haihu wani bad thing zai samu baby din dan haka sai jikinki ya tsayar da nakudar har sai kin je inda yake ganin is safe. Mata da yawa zasu bada labarin sun fara labour sunje asibiti ciwon ya tsaya sai da suka dawo gida sannan ciwon ya dawo, to wannan shi ya saka advisable gwara ki zauna a gida a dakinki, in ma da yara ki tura su wani gurin but make sure wayarki tana kusa dake, sai kin tabbatar ciwon yazo sosai da sosai sannan sai ki kira a kaiki asibiti in haihuwar asibiti zakiyi, inta gida zakiyi ma ki tabbatar kin kirawo wacce zata karbi haihuwar ita kadai tazo gurinki. But NEVER attempt to give birth alone, it is very risky dan baki san yadda zata zo miki ba.

Da yake apartment dinsu a sama yake sai Aisha tayi ta hawa stairs din nan tana sauka, in taji ciwon yazo sai ta zauna har sai ya lafa sannan sai ta tashi ta cigaba. Wannan shi yataimaka mata wajan saurin budewa. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta koma apartment din su ta kunna wa kanta shower mai zafi tayi wanka sosai, sai kuma taji ciwon ya lafa mata, amma tana dawowa daki kafin ta saka kayan data tanada musamman saboda wannan ranar kawai sai taji ruwa kaman an bude fanfo yana zubowa, tasan me hakan yake nufi dan haka ta kira wayar Nura, kafin ya dauka taji wani azababben ciwo wanda ya saka ta yar da wayar ba tare data sani ba, tana jin muryar Nura yana ta hello hello amma babu bakin amsawa, dama haka haihuwar take? Dama haka ciwon yake? To ita mai yasa ma tayi cikin ballantana har tazo haihuwa? Yaushe hakan ta faru? In haka matan da suka haihu sukaji to su kuwa menene ya saka suke kara haihuwa? Ita dai daga wannan ta gama, wannan din ma tsautsayine, lol.

Ciwo Aisha take ji irin wanda bata taba tunanin akwai irinsa ba. Sai daya lafa mata sannan ta sauke numfashi. Ta sake daukan wayarta da niyyar kiran Nura sai ga kiran sa nan ya shigo, ta dauka tun kafin tayi magana yace "jikin ne Wifey?" Kai ta gyada masa tana cije lebe kamar yana kallonta, yace just hold on gani nan zuwa, five minutes" ji take yi kamar ta dora hannu aka ta rusa kuka, ita five minutes din nan ai infinity ne a gurinta, why can't he come in two minutes tunda ba nisa ne da makarantar ba. Amma sai da ciwon ya lafa sannan ta tuna cewa kafin ya fito daga makarantar ma aikine.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now