Epilogue

9.2K 729 65
                                    

Yes. Nasan labari ya iske da yawa daga masu karanta littafina cewa Allah ya albarkace mu da samun karuwar baby girl, hence my long silence. Wadanda suka kira ni a waya, wadanda suka turan sakon murna ta text ko ta whatsaap, da wadanda sukayi min barka a facebook da kuma whatpad, nagode, nagode, Allah ya bar zumunci.

Yes. Masu complain kuma na gani kuma nasan yawancin masu complain dinnan yammata ne da samari, don't worry, one day you will understand, zaku ce "ashe Maman Maama tayi kokari". Lol

But, Alhamdulillahi, this is the end of this journey. The long, long awaited last episode is here.
In kunga typos kuyi hakuri. Yayi tsaho da yawa ba zan iya editing ba.

Sai da Khadija ta zubar da wanka sannan suka tafi Abuja. Ranar Humairah ta hada jariran biyu ta ringa daukan su hotuna kamar ba gobe. Ta rasa ma wacce zata zaba a ciki dan ita kam Allah ya dora mata son babies.

Haka Abbas ya dauki Khadijah suka yi ta yawon zagaya dangi suna nuna musu little Aisha. Kowa yaga Abbas da family dinsa sai ya taya shi farin ciki dan kallo daya zaka yi masa kasan cewa yana cikin kwanciyar hankali, no longer lonely and sad. Dan shi kansa har mantawa yakeyi wai yana da wani bad background ballantana kuma tunda baya kusa da duk wanda zai tuna masa da asalin nasa.

A gidan Aisha Khadija ta sauka, duk da dai shi abbas ba haka yaso ba amma Khadijah could not miss a chance na zama tare da sister da daughter dinta, shima kuma yasan tayi missing dinsu dan haka ya barta ta zauna a tare dasu. Sai da sukayi sati daya a Abuja, lokacin itama Aisha tayi arba'in sannan suka hadu suka tafi Dutse tare da yayansu da mazajensu baki daya. A ranar sai da Abba ya shiga daki ya share hawayen dadin ganin yayansa kowacce cikin kwanciyar hankali da nutsuwa tare da familyn ta, kuma kallo daya zaka yi musu kasan irin kaunar da suke yiwa junansu. Komai ya wuce kamar ba'ayi ba, tamkar anyi ruwa an dauke, amma kuma some memories will never vanish sai dai suyi fading.

Satinsu daya a Dutse suka tafi Kano, anan suka kwana uku gidan Aunty Bilki sannan suka zagaya gidajen duk yan uwan Umma suka gaishe su. Aunty Bilki tana ta faman hidima dasu, tana ta tarairayar takwararta dan ba karamin jin dadin karar da Aisha tayi mata tayi ba. Amma kuma lokacin da suke yi mata sallama zasu tafi duk abinda ta bawa takwarar tata sai da ta bawa little Aisha, bata banbantasu da komai ba, wannan ba karamin faranta ran Aisha yayi ba.

Ta jirgi suka koma Abuja. Daga nan Khadija ta fara shirye shiryen komawa Taraba, but there was one last thing da take so ta kammala, one very important thing. Ana gobe zasu koma Abbas ya kaita palace tayi musu sallama. Akan hanyar su ta dawowa ta gabatar masa da bukatar ta. "Dear nace ko zaka shiga ka duba jikin Dr" ya bata wani sharp look sannan ya dauke kansa ya cigaba da tuki amma maganar ta ta taba shi. Rabon daya saka babansa a idonsa tun kafin yasan ko wanene shi, rabon kuma da yaji labarin daya shafe shi tun kafin ya bar garin Abuja, which was getting to a year. For all he knows zai iya yiwuwa ya mutu amma kuma yana ji a jikinsa cewa bai mutun ba, musamman saboda yasan idan har ya mutu dole zai sani one way or the other.

Jin yayi shiru yasa Khadija ta sake cewa "at least let him see his grand daughter, ko da kai ba zaka ganshi ba". Ya danyi tsaki yace "can you please drop the subject? I am not letting my daughter any where near him" jin haka yasa Khadija taja bakinta tayi shiru saboda bata taba yi masa musu ko abu ne yayi ba dai dai ba takan bi a hankali ta fahimtar dashi ba tare da tayi masa musu ba, dan haka yanzu ma sai tayi shiru amma da niyyar zata nemi wata hanyar da zata saka shi yaje yaga mahaifinsa.

A haka suka karasa gidan Aisha, nan take Abbas ya saki fuskarsa kamar babu abinda yake damunsa suka yi ta wasa da dariya da Aisha da familyn ta, yana ta tsokanar Humairah wadda ya mayar tamkar jikarsa, amma cikin ransa yana jin wani iri. Yayi niyyar yanke alaka ta har abada da mahaifinsa amma me yasa yake jin wani iri a ransa? Me yasa yake jin kamar yayi missing something? Did his father deserve to see his granddaughter?

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now