Together Again

7.7K 907 49
                                    

This is a story of two sisters. Aisha da Khadija. Born of same parents. Daya kyakykyawar daya kuma akasin haka. They started their life's journey together, inda iyaye da sauran al'umma suka dauki buri suka dora akan kyakykyawar, thinking she will have a bright future with a perfect husband, yayinda 'yar uwarta kuma ta fuskanci ƙyama daga al'umma hatta daga mahaifinta wanda yayi tunanin maybe sai dai yayi sadakarta dan babu mai aurenta. Abubuwa da yawa suka faru most if which are not good memories. Daga nan suka rabu. Kowa ta kama nata life journey din daban. A yau, after almost 18 years, sun sake haduwa. Amma kuma Allah almusawwiru ya juya lamuransu completely zuwa abinda ko a mafarki ba'a taba tsammanin zai faru ba sanda suna yara. Kyawu, dukiya, mulki da shi kansa ran da muke takama dashi duk na Allah ne ba namu bane ba, ya kan bamu ne dan yaga yadda zamuyi dashi, kuma yana karba a duk lokacin da yayi niyya. Ya kai/ke ɗan/ƴar Adam, me ya kai ki/ka takama da kayan aro? Kayan da ba naki/ka ba?

Cikin rawar jiki Aisha ta kara matsowa kusa da matar tana kare mata kallo, cikin rawar murya matar ta cigaba da magana. "Yarinya muke cigiya, tun daga gidan marayu na Lagos aka turo mu na nan shine su kuma suka bamu address din gidan nan suka ce a nan ake riƙon ta, sunanta Humairah" ta fada hawaye yana bin idonta, ta kara da cewa "my beautiful Baby. My Aisha_Humairah" sai kuma ta balle da kuka gaba daya.

Daga ji kasan cewa fadar sunan kadai ba karamin ta ba zuciyarta yake yi ba. Duk abinda take fada Aisha taji, sai dai yawu ya ƙafe gabadaya daga bakinta ballantana ta iya furta wata kalma. Da kyar ta iya hada kalma daya tace "Khadijah?" Da sauri matar ta dago kai cikin mamaki da ruɗewa, sunanta ne Khadijah, amma yaushe rabon wani mahaluki ya kirata dashi? Kuma a ina wannan hadaddiyar matar tasan sunanta? Ta yaya? amma kuma ba ta iya cewa komai ba sai kallon Aishan take yi, babu alamar recognition ko kadan a idonta. Humairah da take tsakiyar palo rike da hoto tana jiran amsar tambayar da tayi wa Aisha ta karaso gurin da suke ta sake maimaita tambayar "aunty Aisha ina kika sami hoton Mamana?"

Muryar da matar taji ya saka ta kalli Humairah da sauri, ai kuwa kamar wadda aka yiwa allura sai ta mike ta nufo Humairah,  saboda sauri, rama da kuma yadda jikinta yake karkarwa sai gata ta yanke jiki ta fadi, ta sake mikewa tana kokarin kamo Humairah wadda ita kuma ta yar da hoton hannunta ta kwalla kara ta ruga bayan Aisha ta buya tana cewa "aunty Aisha ki taimake ni mahaukaciya zata kamani" wannan kalaman su suka saka Khadijah durkushewa a kasa cikin wani irin gunjin kuka, Aisha da har yanzu idanuwanta suke a kafe ta matso ta kama ta ta mikar da ita tsaye, ta sake kiran sunanta "Khadijah? Khadijah ki kalle ni nice Aisha. 'Yar uwarki Aisha"

Khadija ta tsaya da kukan da takeyi tana kallon matar data kira ta da Khadijah ta kuma kira kanta da 'yar uwarta Aisha. A ina tasan tana da 'yar uwa Aisha? Ita dai a saninta ko Baby batasan da zancan Aisha ba ballantana har ta gaya wa mai rikon ta. Ta kare mata kallo tun daga kasa har sama. Ba ta da kiba amma kuma sam ba za'a saka ta a sahun ramammu ba. A idonta sai taga tayi mata kama da wata 'yar Nigerian films mai suna Genevieve Nnaji, sai dai wannan hancinta yafi na Genevieve din tsaho. Babu abinda yake tashi daga jikinta sai wani kayataccen kamshi. But still, her eyes look very familiar, and her voice too.

A hankali ta saka busashshen hannunta mai dauke da zako zakon faratan da suke cike da datti ta shafa fuskar Aisha, sai a lokacin hawaye ya zubo daga idon Aisha. Ta saka hannu ta rike hannayen Khadijah, Khadijah ta kai dubanta kan hannun Aisha. And she saw the scar, kwance a wrist din hannun Aisha na hagu. She remembered the last time da taga Aisha. Ranar data kwace mata miji. Ranar da aka daura aurenta da Kamal sunzo zasu gudu Aisha ta tari gaban motarsu. A lokacin ji take a ranta tamkar tafi kowa sa'a a rayuwa. A lokacin ji take a ranta tamkar tayi winning wani game ne. Tun daga lokacin ne kuma rayuwarta ta fara chanzawa. Ta tuno the last time da taji labarin Aisha, ance mata tana gidan aunty Bilki ta samu some kind of nervous breakdown wanda ake tunanin ya taba kwakwalwarta. Dan haka a yanzu she expects to see Aisha a gidan mahaukata tana karbar magani ba wai a Abuja ba in the body of some gorgeous lady, while ita din kuma ƴar ta tana mata ihun mahaukaciya.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now