The New Life

8.4K 823 30
                                    

Ba karamin dadi labarin Aisha yayi wa Khadija ba. Taji dadin cewar Kamal ya yafe mata, bata taba tsammanin samun yafiyar sa cikin sauki ba amma tasan albarkar Aisha taci. Sai dai kuma maganar tafiyar Humairah ta dagula mata sauran lissafinta gaba daya. Dan haka ta samu guri ta zauna a bakin gado ta zabga uban tagumi da hannu biyu. A bangaren Humairah kuma confusion ne a ranta, tana son Babanta sosai kuma tana son zama dashi dan suyi making up for the lost time amma kuma bata son rabuwa da mamanta da aunty Aisha, bata son rabuwa da Ya Ameen. Bata son ta sake wata sabuwar rayuwar all over again. Ta gaji da chanje chanjen gida, ta gaji da chanjin rayuwa, she wants to settle down. Dan haka itama sai ta samu guri ta zauna a kusa da Khadija tayi tagumi kamar yadda tayi duk suka zubawa Aisha ido tana kara gyarawa Humairah kayanta wadanda already dama a hade suke.

Humairah tace "kuma in na tafi yaushe zan dawo?" Aisha ta daga kafada tace "I don't know" Humairah tace "to makaranta kuma fa?" Aisha tace "akwai makarantu a can ai" sai Humairah ta fara sheshshekar kuka, sai da Aisha ta gama abinda take yi sannan ta zo ta durkusa a gabanta tace "look at me Humairah. Ni kaina bana son tafiyar ki amma ba zan iya hana babanki daukanki ba. Bana son shiga hakkinsa dan yana ganin mutunci na sosai kuma bana son inyi crossing limit dina. Yayi min alfarma daya bana son forcing dinsa yayi ta biyu. Kiyi hakuri ki bishi ku tafi, kije kiga 'yan uwanki da kakanninki suma kuma su ganki. Nayi miki alkawarin idan komai ya lafa I will try to reason with him amma yanzu ko na mishi magana ma ba zai gane ba zai dauka kwace masa ke nake so inyi. Ki je ki ga siblings dinki, am sure you will like it there" Humairah ta goge hawayenta tana jin wani sabon excitement a ranta, tabbas tana son ganin 'yan uwanta.

Sai da ta fita sannan Aisha ta zauna a kusa da Khadija tace "kema kukan zakiyi?" Khadijah ta girgiza kanta. Aisha tace "let her go. Let her enter this next level of her life kamar yadda kema nake so ki shiga" Khadijah ta dago tana kallonta tace "ban gane ba" Aisha tace "ina so ki bini gobe mu koma Abuja tare" da sauri Khadija ta girgiza kanta tace "Nura ba zai amince ba, bana so......" Aisha ta katse ta tace "Nura ya fahimci komai yanzu, dama abinda na gaya miki kenan tun a can, bayan kin taho mun zauna munyi maganganu kuma ya fahimce ni. Abinda nake so ke ki fahimta shine you don't have a future here in dutse, in dai har kina so ki samu future mai kyau sai kinyi burying past dinki which you can't do here. Ki zo mu tafi Abuja inda babu wanda yasan ki ballantana yasan abinda kikayi da. Ki zo mu koma can ki shiga islamiyya ki kara sanin ilimin addini yadda zaki kara kusantuwa ga mahaliccinki shi kuma ya kara bude miki kofofin rahamarsa" har yanzu dai Khadija girgiza kanta take tace "Yaya Aisha, kinyi min komai a rayuwata, kin dauki nauyina fiye da yadda ya kamata kiyi, ni kuma bana son in cigaba da zama nauyi a wuyanki nafi so inyi facing rayuwa independently. A yanzu bani da abinda zan cigaba da gina rayuwata akai, Abba kuma shine mahaifina shine nauyina ya ratayu a wuyansa, let him carry the burden kafin in samu tsayawa da kafafuwana nima"

Aisha tace "and how are you going to do that? Eh? Ta yaya zaki tsaya da kafafuwan naki bayan baki da komai? Kar ki manta takardar secondary school kadai kike da ita balle kice zaki nemi aiki. Come with me, let me share what I have with you" Khadija tace "I don't want you to share kudinki with me" Aisha tayi murmushi tace "waye yace miki kudi zan baki?" sai ta bata labarin zamanta a kano gurin Aunty Bilki da makarantar data shiga ta koyon dinki da saƙa, tace "sanda na dawo Abuja na fara yi kuma da yake garin manya ne ina samu sosai dan Mami ta samo min customers sosai, dana fara aiki ne kuma sai na zama bani da lokaci dole na hakura na daina sai nawa kadai nake yi. Wannan shine abinda nake so inyi sharing dake, my talent not my wealth. Idan kika bini muka tafi sai in koya miki mu ringa yi tare har ki kware ki ringa yi ke kadai" still Aisha taga Khadija kamar bata gama amincewa ba sai ta kara da cewa "besides, ku Ahmad suna bukatar auntyn su dan dama bana jin dadin barinsu a hannun 'yan aiki in bana gida, ga kuma Humairah, maybe babanta ya dawo da ita Abuja kuma itama tana bukatar Mamanta" da wannan Khadijah tayi murmushi ta sunkuyar da kanta tace "to amma sai dai ke ki tambayar min Abba" Aisha tace "sai dai muje mu tambaye shi tare, kema ai 'yarsa ce".

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now