God's Choice

9K 822 35
                                    

Mami ta sake cewa "ikon Allah. Lallai Aisha Allah yayi miki baiwar da ba kowacce mace yayi wa ba, baiwar samun mazaje har uku duk nagari kuma masu sonki tsakani da Allah. They are all good men, excellent men even. Kinga yanzu kamar shi Mahdi, Mahdi na san shi kusan shekaru goma sha biyar da suka wuce. Zan kuma iya cewa ban taba sanin wani mugun halinsa ba, in ma yana dashi ni dai ban sani ba. Kinga matarsa Amira is my best friend, tun jss one muke tare da ita har yau kuma bamu rabu ba, amma hakan ba zai hana in fada miki kyawun halayen Mahdi ba, saboda shawara kika nema kuma shawarar zan baki. Tun da akayi auren Mahdi da Amira bata taba zuwa ta ce min yayi mata wani abu na rashin kyautawa ba, kinga hakan na nuna cewa shi din mijin kwarai ne. Wannan kenan. Sai Amir, oh Amir, da ace ina da kanwa da tun kafin auren Amir da sai nasan yadda nayi na hadasu saboda kyawun halin Amir. Idan kina neman kindest, nicest and coolest guy to Amir ne, Amir is the best husband you can ever wish for. Ban san Hafeez ba, amma daga yadda kika yi min bayanin sa, a zamanin nan da idon samari yake a bude kuma kirikiri ya fada yace baya sonki amma kuma ya karba yace ya yarda zai aureki, da kuma alkawarin da kika gaya min yayi miki, zan iya concluding cewa mutumin kirki ne, kuma tabbas in kukayi aure dashi Allah zai saka muku albarka a cikin auren yadda ba zaku taba dana sanin biyayyar da kuka yi ba. Kuma nan gaba sai kunyi wa junan ku soyayyar da ko auren soyayya sai haka" ta mike ta cigaba da aikin gyaran kayanta.

Aisha tace "Mami kinyi magana amma har yanzu baki ce komai ba. You only confuse me more" Mami ta juyo tana kallonta tace "ba hurumina bane zabar miki miji Aisha, nawa shine in baki shawara, kinsan menene best choice a duk duniya?" Aisha ta girgiza kai, tace "Allah's choice. Ki bashi zabi, let God choose for you. Kin iya istahara?" Aisha ta gyada kai, Mami tace "kiyi istakhara, daga nan kar ki cewa kowa komai a cikinsu, ki koma gefe kiga yadda ubangiji zai yi ikonsa, at the end result din da zaki samu ke kanki sai kinsan cewa shine best".

Bayan Aisha ta koma dakinta ta jima tana tunanin maganganun da suka yi da Mami. Allah mai iko, wai ita Aishan da maza ko kallonta basa yi yau ita ce har take da choice din wanda zata zaba, kuma duk a cikin zabin babu na banza kamar yadda Mami ta gaya mata. Ta iya istahara dama amma ta dauko littafin hisnu muslim ta sake duba addu'ar. Sannan ta tashi ta kammala shirin baccinta tayo alwala tayi sallar raka'a biyu (an fi so a karanta alam nashraha da wash shams a ciki) sannan bayan ta idar sai tayi godiya ga ubangiji kuma tayi salati ga annabi (SAW) sannan ta karanta wannan addu'ar

(Allahumma inni astakh diruka bi ilmika wa astakh diruka bi kudratika wa as'aluka min fadlikal azim fa innaka takhdiru wala akdiru wa ta'alamu wa'anta allamul guyub. Allahumma inkuntum ta'alamu anna hazal amra kairulli fidini wa ma'ashi wa akibatu amri ajalihi wa ajalihi fakdirhuli wa yassirhuli summa barikhu li fihi wa inkunta ta'alamu anna hazal amra sharru li fidini wa ma'ashi wa akibati amri a jalihi wa jalihi fasrifhu anni wa rifni anhu wak dir liyal kaira haisu kana summa raddini bihi).

Tana gamawa ta shafa ta kwanta bacci ba tare da tayi wani abu ba. Haka ta cigaba da aikatawa kullum har tsahon kwana bakwai.

#shi ilimi kogi ne, musamman ilimin addini, abinda ka sani dashi za kayi amfani

Sati biyu bayan nan. Har yanzu Dr bai tunkari Aisha da maganar sa ba, itama kuma bata ce masa komai ba, bata ko nuna masa sunyi maganar da Mami ba. Abinda ta lura dashi a kansa shine, ya kara yawan kiran da yake mata a waya fiye da da, duk da dai inya kiratan yakan tambayeta ne kawai akan ko tana da problem ko akwai abinda yake damunta, wanda duk take amsa masa da a'a. Hafeez shima yanzu ya tsiri kiranta a waya, abinda da baya yi, shima kuma inya kiranta yakan tsokane tane sometimes suyi ta musu ko kuma suyi hirar gida. Shi kuma Amir a nashi bangaren ya mayar da zuwa daukanta daga makaranta al'adarsa, da kansa ya gayawa driver ya daina zuwa daukanta shi zai ke yi, kullum kuma kokarin kafa gwamnatinsa yake yi a gurinta, kulawa, kalamai, kyauta, amma shima har yau bata ce masa komai ba. Ta dauki shawarar Mami, zatayi shiru ta bar wa ubangiji yayi hukuncinsa.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now