Perfect

9.2K 792 57
                                    

Har Al'ameen ya gama wanka ya shirya bai daina murmushi ba, kawai haka nan yaji wani nishadi a ransa, Humairah, bai taba ganin doluwar yarinya irin Humairah ba, already ya riga yayi guessing me ya faru, tambayarta za'ayi ina taje jiya shine ita kuma zata gaya musu komai har zancan auren da yayi mata. She has the most innocent heart he has ever seen. Bata san karya ba bata san boye boye ba except for rayuwar ta ta baya. Yasan Humairah ta kunna masa wuta a gidan gabadaya, and before the end of today the entire family are going to know.

The heat is on, yanzu rigima zata fara and he is very ready to take it all. Iyayensa ne kadai ba zai sabawa ba, suma kuma zaiyi iyakacin kokarinsa wajan ganin sun fahimce shi sun fahimci niyyarsa. Yanzu ne zai fara facing challenges dinsa, challenge na farko shine ya karkato da hankalin Humairah zuwa kansa, make her fall in love with him. Kuma yayi alkawarin zaiyi amfani da duk baiwar da Allah yayi masa, kyau, kalamai masu dadi, kulawa, kyauta dan yaga ya karkato da hankalinta zuwa gare shi. Ya tabbatar ba zai dauki lokaci mai tsaho ba, saboda ya yarda da kansa, ya tabbatar babu wata hot blooded budurwa da zata iya resisting charm dinsa. Ya tuno da Khausar, he hated using her amma shi har ga Allah gani yake bashi da laifi, shi bai taba cewa yana sonta ba, wata magana data danganci soyayya ko aure bata taba shiga tsakanin su ba, ita kadai take abinta sai wadanda suke goya mata baya.

Tsaf ya shirya cikin shiga ta alfarma, cikin shigar sarauta wadda ta fito dashi a yariman sa sak. Kawai sai ya samu kansa da kallon kansa a madubi yana kara gyara wuyan rigarsa da adjusting hularsa, wani barin na zuciyarsa yana ayyana masa gwara ya gyara sosai in case ko zasu hadu da Humairah a hanyarsa ta fita, sai kuma yaji haushin kansa da kansa, wai yau shi Al'ameen ne yake dressing up for a girl? Abinda bai taba yi ba.

Yana fita palo 'yan uwa suka kewaye shi, har da masu yi masa guda kamar shine angon, cousins dinsa 'yammata aka yi ta zuwa ana daukan hoto dashi shi kuwa sai murmushin yake musu amma ji yake kamar ya rufe su da duka, dan dai akwai iyayensu a gurin ne da su kansu ba zasu kusanto inda yake ba. Haka yana ji yana gani Mami ta saka shi yayi ta zagaya manyan matan da suke gidan yana gaishe su, kowa ya ganshi sai yace "Masha Allah, Al'ameen haka kayi girma? Lallai mun kusa dawowa wani bikin" a haka suka hadu da aunty Aisha, yana kallon ta yasan tasan me ya faru jiya, ya gaisheta ta amsa masa da sakakkiyar fuska sannan tace "in an gama taro ina son magana da kai" ya shafa kansa yace "to aunty Aisha, nima da akwai maganar da nake so muyi dama".

Anyi daurin aure lafiya an gama lafiya, Daddy ya bawa uncle Amir waliccin Basma duk kuwa da cewa uncle Abbas ma yana gurin. Amir kam baki har kunne tunda shi yanzu yana both sides din dangin ango da kuma dangin amarya. Wannan auren ji yake kamar dan shi akayi shi. Al'ameen kam bai samu kansa ba har sai da kusan duk baƙi maza suka gama tafiya dan Daddy sakar masa komai yayi, yace it is high time ya fara shiga cikin mutane ya koyi mu'amala dasu. A gajiye ya shigo motarsa ya dawo gida, sai da yazo kofar gida sannan ya gode wa Allah daya kasance a cikin gida gurin Ummee za'a dauki amarya dan haka duk matan da suke nan sun tattara sun koma can, dan yadda ya gaji din nan baya son ya kuma encounter irin ta dazu. Ya lallaba ya shige dakinsa ya rufe kofa ya rage kayan jikinsa sannan ya kwanta, ya dan taba bacci kadan sannan ya farka wannan karon ma da mafarkin Humairah, kawai sai yaji ita yake son gani at least ko shiririta ta dan yi masa yayi dariya, but how? A cikin taron nan ta yaya zai ganta? Yanzu yasan suna can sunata shirye shiryen tafiya kano kai amarya dan yaji ance angon takanas yayo hayar jirgi just for kawayen amarya da abokanan sa. He can't imagine Humairah a cikin jirgi cike da 'yammata da samari, that would be a nightmare to her. Sai kuma wata idea ta fado masa, yayi murmushi ya zaro wayarsa yana neman number dinta daya taba karba a gurin Basma rannan da yana nemanta zasuyi lesson. Ya samu number din yayi dialing.

Humairah sam bata enjoying ranar yau. Tun da ta dawo daga dakin Basma sai taji ta kasa komawa can saboda tana jin kamar she is no longer welcome a cikin 'yammatan. Dan haka tayi kwanciyarta a dakin da suka kwana ta dauko wayarta tana ta kallon pictures din da suka yi a events din bikin. A haka Aisha ta shigo ta sameta, har Aishan tayi wanka ta shirya Humairah tana kwance, sannan ta tambayeta "ba zaki koma gurin Basma ba? Kika sani ko tana nemanki ki taimaka mata da wani abu?" Humairah tace "naje ai dazu, naga da akwai mutane da yawa a gurinta, bana jin tana bukatar komai daga gareni"

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now