The Truth and the Lies

8.1K 773 11
                                    

Tun daga ranar da Aisha taga Khadija a love garden, shikenan ta kasa sakawa zuciyar ta nutsuwa a kan 'yar'uwar tata, kullum cikin zulumi take, kullum cikin tunanin me zai je yazo take yi, kullum in basa tare da Khadija sai take ganin tamkar wani mummunan abin Khadija take aikatawa.

Kuma abinda yafi damunta shine gani take kamar duk abinda Khadijan ta zama laifinta ne, tunda tun suna yara ita ce take boye duk wani laifi na Khadija bata fadawa iyayensu, kuma ita ta rubuta mata jarabawar da har ta kaita jami'ar, komai Allah yana yinsa ne a bisa tsari, Allah ya san nufin Khadija shi yasa ya hana ta kwakwalwar karatu, dan haka Aisha take ganin bata takardunta tamkar yiwa Allah katsalandan ne, tunda ga abinda hakan ya jawo.

Kusan kullum sai taje love garden tayi ta dubawa ko zata sake ganin Khadija amma bata kuma ganin ta ba. A gida kuma kullum sai ta yi mata nasiha, amma daga bakar magana sai cin fuska shine amsar da take samu.

Ranar nan tace mata "wai ni Aisha ina ruwanki dani ne? Naga alama fa kwanan nan duk kin bi kinsa min ido, in zunubin nake aikatawa kabarin mu daya dake? Ki sakar min mara inyi fitsari ehe" daga nan Aisha ta fahimci Khadija karya take da tace mata zata daina, halinta ne a jikin ranta yake dan haka miji ne kawai ya dace da ita, mijin ma strong one wanda kuma take so yanda ba zata ke yin abinda zai bata masa ba. Da haka Aisha ta yanke shawara.

Rannan Nura yazo cafeteria yana ta yi mata zance kamar yadda ya saba. Yace "yanzu Aisha da zamu hadu dake a cikin gari fa bazan gane ki ba. A ce yadda muke dake ban taba ganin fuskar ki ba. Gaskiya ba kya kyauta min" ba tare da ta kalleshi ba tana ci gaba da aikin gabanta tace "yaya muke da kai? Ni in banda sunanka babu abinda na sani. In kana magana irin haka in wani yaji ai sai ya dauka irin wani friendship ne a tsakanin mu" ya dafe kanshi yace "kash, amma kin yanke ni da yawa, wato kina nufin ni ko layin friends dinki ban shiga bako?" Tace "you are my customer" yace "that's it? Customer ko? To mun ɓata dake daga yau, na ma daina zuwa cin abincin ki daga yau" tace "sauka lafiya, yadda ka fita da kafafuwanka haka zaka dawo da kafafuwanka" ya dan juya kamar zai tafi sai kuma ya dawo ya dora hannun sa akan kanta yace "Na dawo to" har Mama sai da tayi dariya.

Aisha ta jawo kujera ta zauna a daya side din tace masa "ni kuwa wannan yarinyar da muka gani rannan a garden ka santa sosai?" sai da ya danyi tunani kaɗan sannan yace "Khadija Zayyan. Na santa amma ba sosai ba, tana level one ne ni kuma kinga ina three, kuma art take yi ni ina science. Amma ina jin labarinta sosai a hostel gurin friends dina. Bamu taba magana ba saboda ba kala ta bace ba. Wani abun ne?" Aisha tace "rannan suka zo gidan mu ita da mamanta, ashe mamanta kawar Umma na ce, ina tayi mata kallon sani sai naji tace a FUD take karatu. Baka ganta ba nutsatstsiya sosai wallahi, kuma mamanta ma mutuniyar arziki ce daga alama duk basu san abinda take aikatawa a school ba. Yanzu me kake tunanin ya kamata inyi akai?"

Yayi tunani kaɗan sannan yace "it depends on yadda kuke da maman nata, kinsan waɗansu iyayen ba sa son laifin 'ya'yansu, idan kinsan maman zata yarda ki gaya mata gaskiya kawai, Allah zai baki lada kuma zaki kara danƙon zumunci a tsakanin ku, idan kuma kinsan maman ba zata yarda ba, to ina ganin kar ki nuna kinsan komai a kanta, dan zaki bata zumuncin tsakanin ku ba tare da kuma an sami gyara ba, in kika barta dan kanta ma wata rana asirinta zai tonu"

Aisha ta gyada kai kamar mai auna maganarsa sannan tace "amma yanzu kasan inda zan same ta? Ina gudun kada daga gani ɗaya in yanke mata hukunci akan abinda ba dai dai ba" ya ɗanyi dariya yace "wannan yarinyar komai kika fada akanta baki yi ƙarya ba, a hostel fa samarinta ba zasu ƙirgu ba, kuma dukkan su bana kirki ba, a malamai ma duk wani lecturer da yayi kaurin suna a neman mata sai ka ganshi tare da ita. Ita fa akwai lectures din da bama ta shiga kuma ta samu grade mai kyau".

Aisha taji kamar ruwan zafi yake kwara mata, nan take ta kara yadda da cewa abinda zata yi dai dai ne. Sun gama hirar su har ya fita sai kuma gashi ya dawo yace "zo ga mutuniyar ki a gurin cin abincin kusa da naku" da sauri Aisha ta fito kirjinta yana bugawa, ta bi Nura a baya zuwa gurin da yake opposite nasu, ta window ta hango ta, Khadijan ce dai, wata matsatstsiyar doguwar riga ce yau a jikinta, hatta shape din pant dinta ana hangowa ta cikin rigar, daga baya kuma wuyan rigar ya kai har tsakiyar bayanta, dan karamin mayafin da ta dora akan ta ya zame ya dawo wuyanta dan haka gashinta gabadaya a bude yake, fuskarta cike da kwalliya, wani in ya ganta zai dauka actress ce a cikin Nigerian film.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now