Not The End

15.1K 1K 123
                                    

Har satin biki ya kusa kamawa Al'ameen bai samu kan amaryar sa ba. Yabi yabi har ya gaji amma Humairah ta tattara shi ta ajiye a gefe. Ten days to the wedding day aka dauki amarya aka kaita Yola, a can za'ayi kamu tare da yini na mutanen Yola yadda ba sai an basu wahalar tahowa Abuja ba, sai few da ya zama dole su zo. Wannan ya kara tayar da hankalin Al'ameen dan haka dole ya nemi number Saudat a gurin AbdulShakur ya kira ta, tare da guidance dinta ya hawo jirgi ya taho Yola ya kuma je har kofar gida sannan ta fita ta shiga dashi dakin da ake saukar baki maza. Sai data sauke shi da duk abin bukata sannan ta koma gurin Humairah ta yaudare ta da cewa babanta yana kiranta a dakin baƙi zasuyi magana.

A tsorace Humairah ta taho, dan tana tunanin dalilin da zai saka babanta ya kira ta waje suyi magana duk da girman gidansu, dan haka tunanin da yazo mata shine wani laifin tayi yake so yayi mata fada amma baya so mutane suji. Ta ringa lissafo laifukanta tana tunanin wanne ne daga ciki. A haka har taje dakin. Ta shiga da sallama fuskarta da tsoro a rubuce a jiki, jikinta har rawa yake yi. Tayi rashin sa'a kuma kujerar da Al'ameen yake kai a kusa da kofa take dan haka ta data shiga bata ganshi ba.

Ta tsaya a tsakiya tana rarraba ido tare da kara yin sallama. Ya kare mata kallo fuskarsa dauke da nishadi dan shi bai taba ganin mutum mai tsoro irin Humairah ba, he had no idea yadda tayi surviving rayuwarta a baya, yadda take kwana a bakin titi da kuma karkashin gada. A hankali ya mike tsaye ya saka hannayensa a aljihun sa yayi gyaran murya. Ai kuwa sai ga Humairah ta juyo a guje unluckily for her sai gata a kirjinsa. Ta kuwa dage iyakacin karfinta da niyyar kurma ihu sai yayi sauri yasa hannunsa ya toshe bakinta nan take ta kama shi da kokawa idanunta duk sun rufe jikinta yana wata irin rawa. Sai daya saka iyakacin karfinsa sannan ya rike ta tsam a jikinsa, a haka har ta fara daina kokawar sannan a hankali yayi mata magana a kusa da kunnenta yace "shshsh. It is just me, Al'ameen. Am not going to hurt you, never." a hankali ta fara relaxing, numfashinta ya fara dawowa dai dai, sannan tasa hannayen ta biyu ta ture shi tace "ni ka daina yi min magana a kunne" ya koma da baya yana dariya sannan ya zauna a kujera ya dora kafa daya a kan daya yana kallonta. Ta zauna itama, reluctantly, a hannun kujerar da take farthest from him tace "me kake yi anan?" ya taso yadawo kujerar da take kusa da tata yace "gurin amarya ta nazo" ta juya kai gefe tace "wa kenan? Dan ni dai nasan bani bace ba" yace "me yasa kike tunanin bake bace ba?" tace "saboda ni dai I can't remember sanda nace ina sonka, ballantana in yarda in aure ka" sai kuma ta dawo ta zauna sosai a kan kujerar ta juyo tana facing dinsa tace "bansan dalili ba, everyone just assumes na amince da auren nan. Akwai friend dina a school da za'ayi auren ta after mine, tace min sai da aka kirata aka tambayeta ko tana son wanda za'a bata, amma ni babu wanda ya tambaye ni" yayi tagumi da hannu daya yace "what a pity, na tausaya miki amma. Kinsan shawarar da zan baki. Go look for Aunty Aisha, am sure she is close by, ki gaya mata kice 'ni fa bana son auren Ya Ameen' am sure in kika fadi haka za'a fasa, sai dai there is a catch, nasan kudin da suka kashe gurin shirya bikin nan ba zai zama asara ba to what will happen is, za'a samu wani a cousins dinki a hada ki dashi, nima kuma haka. Kin ga shikenan, we will get married, but not to each other" tunda ya fara maganar take kallonsa sai daya gama ta yamutsa fuska kamar wadda taga abin tsantsani, saura kadan yayi dariyar yadda tayi da fuskar ta amma ya maze saboda in akwai abinda yake sure akai shine cewa Humairah tana son sa, she is just too stubborn to admit to him.

Ta turo baki tace "na fasa fada musu to. Amma sai dai ayi mana gida biyu, naka daban nawa daban. Sai in tafi dasu Saudat da Amna su taya ni zama a gidana, kai ma ka nemo wanda zai ke taya ka zama" yace "done. Now let's talk about the wedding. Akwai abinda kike so? Kinga fa ko gidan baki je kin gani ba ballantana in da akwai changes din da kike so ki fada ayi tun da wuri" ta danyi shiru tana nazarinsa. Tasan done din daya ce mata ba har zuci bane ba, amma sai ta rabu dashi tace "ni babu abinda nake so, su Mami da Aunty Aisha sun gama shirya komai ai" Yace "OK. Tell me about the honeymoon, wacce kasa kike son zuwa?" ta bude baki cikin mamaki, damuwar fuskarta gabaki daya ta bace, tace "fita zaka yi dani kasar waje?" yayi dariya yace "yes Humairah. fita zamuyi, duk kasar ko kasashen da kike son zuwa" ta mike ta fara zagaye kanta a kasa alamar tunani, sannan ta dawo ta zauna idonta kamar zai fado waje tace "India. Oh my God. Inje in ga Rambir Khafur da Salman Khan oh my God da Shah Rukh Khan. Sannan sai Korea, please Ya Ameen ka kaini Korea inga Lee min hoo, song jong ki, da ji Chang wook" ya bata rai yace "oh, on our honeymoon din kike lissafamin mazan da zakije ki gani?" ta durkusa har kasa tana mummurza hannunta "please Ya Ameen please please" ya sake daure fuska "me nace miki akan Ya Ameen din nan?" kafin ta bashi amsa Safiyya ta shigo, nan take ta mike ta fara bata labarin zasu tafi India da Korea ita da Ya Ameen, nan suka zauna suna ta lissafo film stars din kasashen har Safiyya tana bata saƙo wajansu.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now