The Starting Point

9.7K 723 24
                                    

Sai da Aisha tayi wata uku a Abuja sannan transfer dinta ta gama kammala. A cikin wata ukun nan ba karamin sabo tayi da Mami da yarantaba, mai gidan ne dai baya baya saboda wani irin kwarjini ne dashi wanda indai har yana palon to Aisha bata iya zama, dan ma dai ba sosai yake zama anan din ba yafi zama part dinsa.

Abdallah shine babban abokinta, dan sanda aka bashi labarin ta dawo gidan da zama ba karamim murna yayi ba, nan take ya dage gurin koya mata yarensa kuma cikin ikon Allah sai gashi ta fara koya, abinda bata iya ba kuma sai ta rubuta mishi a takarda. Tunda Aisha take bata taba ganin yaro mai kwakwalwar Abdallah ba gashi dai ba zai wuce four years ba amma abinda ya iya ko wani dan ten years din sai haka. Iyayensa ma sun fahimci haka, dan haka suke bada himma sosai gurin karatunsa. Bayan Abdallah kuma sai Basma, ita kuma kawancensu da Aisha ya fara ne few weeks bayan zuwan Aisha gidan, tayi wanka ta shirya ta fito palo ta tarar da Basma tana kwance, ta daga kai ta kalleta tace "Aunty Aisha kinyi kyau sosai, ina ma dai in na girma in zama kyakykyawa irinki" maganar ta taba zuciyar Aisha sosai dan ita a idonta gani take babu wanda ya kai Mami da iyalinta kyau, amma sai gashi yarinyar gidan tana yabawa da tata halittar da take ganin bata da kyau.

Tun daga ranar suka dinke, har Atika ta fara mitar Aisha ta kwace mata Abdallah da Basma. Wanda bata fiya kulawa ba shine Al'ameen. Wannan is totally his father's son, ba Aisha kadai bama har ma'aikatan gidan basu fiye shiga harkar saba dan ko kallo basu ishe shi ba ballantana yayi musu magana. Bashi da wulakanci amma kwarjininsa yafi karfinsa. Wani lokacin Aisha takan yi mamaki in ta ganshi yana hira da wasa da dariya da kannensa, amma in ya bata rai duk sai suja baya, maminsa ce kadai mai iya masa wadda Aisha ta fahimci akwai shakuwa sosai a tsakaninsu, bayan ita kuma sai kakarsu wadda suke kira da Ummee, wadda Aisha ta fahimci cewa matar sarki ce kuma a palace din take da zama, dan most weekends yaran a gurinta suke zama sai dai Aisha bata taba ganinta ba.

Dr Mahdi da Amira sunzo bayan dawowar Aisha abuja, inda Amira tayi ta yiwa Mami mitar ta kwace mata Aishanta ai gidansu ya kamata ta zauna ba gidanta ba, suka yi ta wasa da dariya daga baya kuma aka bar maganar, kafin su tafi Dr ya kirawo Aisha gefe yayi ta tambayarta if she is comfortable and if she need anything, duk ta amsa masa da cewa bata da problem, amma duk da haka ya jaddada mata cewa duk abinda take bukata, ko menene ga number dinsa nan ta kira shi, kuma ya dauki kudi masu yawa ya bata yace saboda harkar makaranta, da taki karba amma ganin ransa ya baci sai ta karba tayi masa godiya.

Kullum Aisha suna yin waya da Aunty tana jin halin duk da ake ciki, kuma kusan duk wayar da sukayi sai auntyn ta gaya mata cewa ita bata son zamanta a abujan nan, tace "yanzu ga maganar bikinku da Hafeez, shi yana kano ke kina Abuja yaya za'ayi zaman auren kenan?" Aisha ta kan yi shiru ko kuma tayi dariya in tayi mata irin wannan maganar, dan ita ko a kanta bata kawo cewa zata auri Hafeez, kuma shi kansa Hafeez din bai taba yi mata magana wadda ta shafi wannan ba, auntyn ce dai take kidanta kuma tayi rawarta ita kadai. Ita kuma Aisha tana jin nauyinta sosai, bata jin zata iya yi mata maganar cewa bata son auren.

Tunda Aisha tazo bata taba fita ko ina ba sai ranar da aka ce mata zata fara registration, ranar kwana tayi tana zulumin yadda rayuwarta zata koma da irin changes din da zata samu, amma kuma deep inside her she was ready, she wanted to do that and nothing would change her mind. Nothing. Ranar da safe kafin Mami ta fita office ta shigo dakin da Aisha take tace mata "are you ready for school? Ni zan fita office, akwai abokin Sultan yasan kan makarantar sosai, nayi masa magana jiya na roke shi alfarmar yazo ya rakaki, ki shirya zai zo an jima ku tafi tare" tayi studying fuskar Aisha sannan tace "don't worry, he is the nicest guy I have ever known".

Tun karfe takwas Aisha ta shirya ta zauna zaman jira, shiru shiru har karfe goma, ta fiyo palo ta kwanta da jakar takardunta a gefe tana jira, a haka har bacci ya dauke ta. Cikin baccin taji ana magana, baba gaji tana cewa "ka ganta nan, har ta fara bacci bara in taso maka ita" taji muryar namiji yana cewa "rabu da ita kawai, bara in koma, dama aiki yayi min yawa na zame da kyar na fito" Aisha ta mike da sauri tace "na tashi, baba gaji kice masa na tashi" ya daga labulen yana kallonta yace "cigaba da baccinki kawai, I thought you are ready shi yasa na taho, ashe ke baki shirya zuwa makarantar ba ma baccin ki kike yi" Aisha taji ranta ya baci tace "I have been ready since 8 o'clock, inata jiran ka baka zo ba, Mami ce tace injiraka dama da bazan jira kaba" ya shigo sosai suna kallon juna.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now