Abuja

8.7K 753 26
                                    

A ranar Abba ya koma dutse, three days after that Aunty ta karbo result din hotunan Aisha, ta kira Abba ta gaya masa, sannan ta kira number wayar data gani a card din Dr Mahdi. Three missed calls bai dauka ba, sai ta rabu dashi. Sai can bayan magrib sai gashi ya kira ta, ta dauka da sallama suka gaisa sannan tayi masa bayanin kanta, yace "ohh na gane, maman Aisha ko?" Tace "eh" sai kuma ta gaya masa hukuncin da suka yanke ita da Abba na kawo Aisha Abuja, tace "sai dai muna so kafin mu taho da ita din a bamu breakdown na kudaden da kake tunanin zamu kashe saboda musan abinda zamu tanada, kaga in munji abin yafi karfin mu shikenan sai mu hakura ba tare da mun wahala ba" yace "in dai maganar kudi ce karki damu, shi wannan asibitin private ne amma kuma kudin da zaku kashe tamkar wanda kuke kashewa ne a government, sannan zaku sami best medical care anan fiye da yadda kike tsammani. Me asibitin ta bude shine ba wai don ta sami kudi ba sai don ta taimakawa marasa lafiya masu karamin karfi" Aunty taji dadin jin haka sosai, tayi masa godiya, ya gaya mata cewa duk sanda zasu taho ta kira shi ta gaya masa.

Washegari da daddare tayi wa abban Zahra maganar tafiya Abuja, dama ta jima tana tunanin yadda zata tunkare shi da maganar tunda shi ba mutum ne mai son yawan fita unguwa ba ballantana ayi maganar tafiya wani gari inda basu da kowa a can. Tana gaya masa kuwa ya bata rai yace "wacce irin Abuja kuma Bilkisu? Ji nake ke kika ce min Dr din nan yana iyakacin kokarinsa, to me yasa zakuce kuma lallai sai kun kaita abuja? Lafiya ba'a hannun Allah take ba? Duk sanda yayi niyyar zaki ga ta samu sauki ne ba wai a Abuja saukinta yake ba" yana gama magana ya juya mata baya alamar ya gama magana kenan. Ta jima a zaune a gaban gadon tana tunani, tabbas abban zahra yayi iya kokarinsa, tunda ta dauko Aisha bai taba complain ba, bai taba nuna gazawarsa ba ko kuma ya nuna cewa Aisha ba 'yarsa bace ba, duk harkokin asibitinta dashi akeyi, duk abinda ya siya wa Zahra sai ya siyawa Aisha, dan haka yanzu dan ya ki yarda da tafiyarta Abuja kai Aisha asibiti bai kamata tayi masa butulci ba. Amma kuma ita kam har zuciyarta ta amince cewa kai Aisha Abuja shine solution din problem dinta, haka nan kawai take jin kamar wata sabuwar rayuwa ce take jiran Aishan a Abuja, kamar wani chance ne Allah ya bata wanda bai kamata a danne mata shi ba.

Amma kuma ta zata yi? Mijinta ya hana ta zuwa babu yadda zata yi taje, to ko abban Aishan zata gayawa shi ya zo ya kaita da kansa? Amma kuma abba namiji ne ba zai iya kula da Aisha a asibiti ba, in tace gwoggo taje tasan zuwa zasu yi su rikice ba lallai ne ma ta gane address din asibitin ba, ko kuma taje tayi ta rigima da mutane a karshe ta salwantar da kudin da aka bata ta dawo ba tare da anyi achieving komai ba.

To yanzu ya zata yi? Wannan yarinya marainiya ce kanwarta uwa daya uba daya ce ta haife ta dan haka hakkinta ne ta kula da ita.

Har safiya bata yanke hukunci ba, sai da yamma ta rubuta text ta tura wa Dr Mahdi, tayi masa bayanin duk abinda yake faruwa na rashin wanda zai kawo Aisha Abuja, dan haka ta gaya masa cewa sun hakura da zuwa abujan zasu ke ganin sa a nan kano duk sanda ya samu zuwa.

Bai mata reply ba kuma bai kira ta ba har wata safiyar, har ta fitar da tsammanin ji daga gare shi sai kuma ga wayar sa ta shigo, ta dauka suka gaisa yace mata yaga sakonta abubuwa ne suka yi masa yawa shi yasa bai amsa mata ba, amma shi gaskiya hukuncin barin Aisha a kano bai yi masa ba, yace "idan kin amince, kuma kina ganin babanta zai amince ni zan kula da ita, abinda zakuyi kawai shine ku hado ta da wanda zai kawo ta gurina, ina da iyali da muke zaune tare dasu anan Abuja, in yaso sai ta zauna a gidana in ringa. kaita asibiti duk sanda bukatar hakan ta taso har lokacin da zata samu lafiya. Duk wanda zai kawo ta zai ga gidana kuma zai ga asibitin namu, duk sanda kuke bukata zaku zo ku ganta" aunty tayi shiru ta kasa bashi amsa, yacigaba "tunda kika gaya min yarinyar nan marainiya ce hankali na gab to rip jeeza daya ya karkata kanta, kuma kamar yadda na gaya miki her case is not as big as you think, cikin few weeks zakiga ta warke tas. Kuma na gaya miki cewa mai asibitin nan ta gina shine saboda taimakon masu karamin karfi, dan haka Aisha ba ita ce mara lafiya ta farko dana dauka na kai Abuja ba kuma ba zata zama ta karshe ba insha Allah" a haka yayi ta convincing aunty har tace masa "to shikenan Dr, zan sanar wa mahaifinta inji abinda zai ce. Mun gode sosai Allah ya biya da gidan aljanna" suka yi sallama ta ajiye wayar tana tunani, anya kuwa ta yarda haka kawai ta barwa stranger 'yar marainiyar Allah wadda ba isashshiyar lafiya ce da ita ba? Ta kira Abba ta gaya masa duk yadda suka yi da Dr, tace "ya kake gani?" Yace "ina ganin ni zanzo in dauke ta muje can tare, sai in ganshi in ga gidan nasa da ya fada, sannan in san ko zan iya yarda dashi ko akasin haka".

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now