Resolution

8.3K 736 10
                                    

Kallon shi kawai Mami tayi, tana noticing yadda idonsa yayi ja, kuma tasan wannan jan har cikin zuciyarsa haka abin yake. Ta mikar da Humairah tsaye suka fara tafiya sannan tace masa "ka saka kayanka ka sameni a dakin Daddy". Tana rufe kofa ya kalli jikinsa, he is almost naked, wani irin tururi zuciyarsa take yi masa, he has never been humiliated like this in his entire life, shi mutum ne da baya son hayaniya sam, baya son shiga harkar mutane kuma baya son a shiga tashi, he respect his privacy sosai, yana kare tsiraicinsa fiye da komai dan ba zai iya tuna ranar da wani, mace ko namiji ya ganshi babu riga ba, ballantana babu riga babu wando.

His younger siblings, his parents and that stupid stupid girl. What the hell was she even doing a dakinsa? Dakin da ko siblings dinsa sun san ba'a shiga in ba da kwakwkwaran dalili ba? Ta shigo har dakinsa unenvited sannan tayi masa ihu, ta kulla masa sharrin da shi yanzu bai san ta inda zai fara warwararsa ba. Inda ya dan ji dadi daya ne daya kasance family dinsa ne kawai suka gani, an he trust them to keep it within them. Amma su din ta ya zaiyi convincing dinsu cewa abinda suka gani ba shine abinda ya faru ba? Daddy shine babban tashin hankalinsa dan yasan bama zai tsaya ya saurare shi ba. Da sauri ya dauki jallabiyyar daya cire kafin ya shiga wanka ya mayar ba tare daya sama komai a jikinsa ba. Ya juya zai fita kenan ya lura da tray akan table kusa da wayarsa. Ya bude bowl din kan tray din yaga damammen oat ga madara a gefe da bowl din sugar. Shi ya manta ma ya saka Basma ta kawo masa oat. Ya rufe yana ayyana abinda ya faru, "I will kill that girl" ya fada yana fita da sauri daga dakin. Wato ita Basma saboda ta raina shi bai isa ya saka ta abu ba shine ya saka ta ita kuma ta saka wata yarinyar daban, mahaukaciyar yarinya ma for that matter. "I will kill them both" yayi deciding a karshe.

Yana fitowa daga dakinsa yaga shigar Basma dakin Bassam. Bata rufe kofa ba dan haka yaji maganar da take fada muryar ta cikin tashin hankali. "Bassam kaga Humairah? Ni ina gurin Haiydar tun dazu kuma na jiyo kamar ihunta, naje daki kuma ban ganta ba, na duba ko'ina ban ganta ba" Al'ameen yaja ya tsaya bai karasa ba, Bassam yace mata "am sorry Basma, but zaman yarinyar nan ya kare a gidan nan, ki koma daki ki fara tattara mata kayanta" tace da sauri "what? Me kake cewa? What happened?" Nan Bassam ya bata labarin abinda ya gani muryarsa can kasa yadda shi kansa Al'ameen da yake bakin kofa ba ji yake yi ba, dan dai ya riga yasan labarin da ake bayarwar ne. Basma tace "No, ban yarda ba wallahi, not Ya Ameen. Ba zai yi haka ba wallahi" Bassam yace "I know that, amma abinda ido na ya gane min kenan, and I don't know what to think. I just can't believe it, I don't want to believe it. Dama yarinyar nan was behaving suspiciously tun zuwanta gidan nan. Ni ban yarda da ita ba gaskiya. Tana da dabi'u irin na munafukai. Wa ya sani ma ko turo ta akayi. Mu mun san Ya Ameen is not like that, ita ce bamu sani ba dan haka ni abinda nafi tafiya akai shine sharri ne take son kulla masa." Basma tace "no. Ita din ma bana jin tana da wayon da zata shirya sharri irin wannan. I don't know what happened between them but am sure there is an explanation to all this".

Al'ameen bai cigaba da jin hirar tasu ba kuma bai bari sun ganshi ba ya kama hanyar part din Daddy, haka kawai sai yaji zafin zuciyarsa ya ragu, it is good to know that someone believes in you and can stand up for you no matter what yaji akan ka ko ya gani a kanka. Ya san akwai soyayya da yarda a tsakaninsa da siblings dinsa amma bai dauka ta kai har after ganin abinda suka gani yau sannan still suyi believing in him with out even demanding an explanation ba. Tunda har yan'uwansa suka yi masa wannan yardar, yana da yakinin zai samu yarda daga iyayensa suma.

A palon Daddy babu kowa sai TV tana yi ita kadai, amma Al'ameen ya san suna ciki. Ya zauna akan carpet ya dafe kansa da hannu biyu. He has never been humilited like this. He has never hated anyone kamar yadda yake jin hatred din yarinyar yana karuwa a zuciyarsa. Idan wannan storm din yayi passing zai binciki maganar Bassam na cewa yarinyar is behaving suspicious. In ma turo ta akayi tazo dakinsa tayi masa ihu to sai ta fada masa. Tun Al'ameen yana lissafa mintuna har ya koma lissafa hours. One hour ta wuce, ya tashi ya dauki ruwa mai sanyi yasha wai ko zai danji sanyi a zuciyarsa amma hakan bai rage masa komai ba. Ya koma ya zauna yana lissafa situation dinsa. Daddy wuta ne, dan wani lokacin ji yake daddyn nasa tamkar yafi wuta zafi, amma kuma komai tafasar da yake yi Mami tana controlling dinsa, dan haka a yanzu Mami ce option din Al'ameen, in dai ya samu Mami ta saurare shi kuma ta fahimce shi to tabbas zata shawo kan Daddy ko ba yanzu ba.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now