The Meeting 2

8.4K 840 42
                                    

Safiyar juma'a Mama ta shigo tana bawa Khadijah labarin su Aisha suna hanya, tana ta dariyar wai ance Humairah tun asuba tayi wanka saboda doki. Amma maimakon Khadijah tayi murna sai taji faduwar gabanta ya karu, ta zauna tana ta kallon agogo tana lissafin lokacin da ya kamata su iso. Lokacin taga kamar baya tafiya, da kyar azahar tayi, lokacin Maama ta kawo mata abinci taci sannan tayi wanka ta hau gyaran daki wai duk dan lokaci ya yi sauri, amma ina, da kyar la'asar tayi.

Tun safe dama Mama ta saka aka gyara wa Aisha part dinta sannan ta shiga kitchen da kanta ta shirya musu abinci, wannan tsohuwar soyayyar tsakanin Aisha da Mama tana nan har yanzu sai abinda ya kara gaba. Sai around 5pm sannan suka karaso. Lokacin da suka shigo Khadija tana daki kamar kullum taji shigowar mota sannan kuma taji hayaniyar su Mama. Ta mike da sauri taje window ta daga labule tana kallon su har suka yi packing suka fara fitowa su Mama suna ta musu sannu da zuwa. Humairah ta durkusa tana gaishe da Mama ita kuma ta dago ta ta rungume ta tana mata magana a hankali yadda Khadija bata jiyowa. Ji Khadija tayi she couldn't wait any longer. Ta fita da sauri ta wuce palour ta bude kofa sai kuma ta tsaya ta kasa karasawa, bata san wacce irin tarya Humairah zata yi mata ba considering yadda sukayi a Abuja. Amma suna hada ido sai taga ta saki Mama ta taho a guje bata tsaya a ko'ina ba sai a kirjin mamanta. Khadija ta sauke wata ajjiyar zuciya wadda ta taho tare da wasu hawaye masu zafi. Anya kuwa duk duniya akwai soyayya mai karfin wadda uwa take yiwa 'yarta/danta?

A hankali Humairah tace "Mama na yafe miki kinji? Duk abinda ya faru dani a sanadiyyar ki na yafe miki. Nima ki yafe min abubuwan da nayi miki a Abuja. Baki cancanci haka daga gurina ba Mamana" Khadijah ta dago fuskarta ta share mata hawayenta tace "it is OK my baby, na cancanci haka na cancanci fiye da haka daga gareki. I was a bad mother to you" Humairah ta katse ta tace "ba haka bane Mama. You were so good to me komai kika yi saboda ki kyautata rayuwata kika yi, duk halin da kika shiga saboda ni kika shiga" Khadijah ta sake mayar da ita kirjinta ta rungume tace "you are wrong, komai nayi saboda kaina nayi saboda son kaina nayi. Idan da saboda ke ne da sai in dawo dake gida cikin gatanki ba in barki cikin rayuwar kaskanci ba. I took away your childhood from you. Na raba ki da kowa na raba ki da komai duk saboda son kaina, saboda bana so in rabu dake because you are my life" sai kuma ta raba ta da jikinta ta rike fuskarta a hannunta tace "amma na miki alkawarin komai ya wuce, I will make sure kin samu duk abubuwan da kika rasa a baya ko da kuwa hakan yana nufin zan rasa ki" ta fada tare da fitowar wasu sabbin hawaye daga idonta. Wai hawayen mutum basa karewa ne?

A nan gurin Mama suka zauna suka huta suka ci abinci amma banda Nura, shi can part din su ya zauna wai ba zai iya zama anan ba (fillo). Sai ranar Mama taga Khadijah ta sake har tana magana tana cin abinci sosai. Bayan sunyi sallar Magrib ne Abba ya shigo ya tsaya a bakin kofa yana kallonsu daya bayan daya, twins suka tashi da gudu suka rungumeshi, Aisha tace da Humairah "ga grandfather dinki nan" sai Humairah itama ta mike ta doshe shi amma sai ya daga mata hannu, ta tsaya kawai tana kallonsa shima yana kallonta sannan yace "wai! Zabgi! Aisha wannan 'yar taki amma kwanon shinkafa take ci kullum ko?" duk suka kwashe da dariya, yace "ai ba abin dariya bane ba, wallahi to gwara kuyi mata aure da wuri ku huta tun kafin ta talauta ku, kuma yadda tayi saurin girman nan daga gani saurin tsufa zatayi, nan gaba in kun fita tare sai an fara tambayar wacece uwar a cikin ku" Aisha tace "yauwa yanzu magana ta fito, kai dai kawai kace kaga tsaleliyar budurwa kana so mu baka, to mun baka kyauta, sai ka gyara mata wancan spare dakin ta tare a ciki".

Humairah ta bude ido tana kallon Aisha tace "Aunty wai ni zaku bashi? Ni wallahi ba zan auri tsoho ba" ta fada tana bubbuga kafa a kasa, Abba yace "kaji tabararriya, an gaya miki nima yarda zanyi da wannan hadin? Salon a cinye min shinkafar wata daya a cikin sati daya? In kinga na yarda ma to taimaka miki zanyi dan kar kiyi kwantai" Humairah tayi narai narai da ido tace "wallahi ko kun aura min wannan ba zan zauna ba" ita har cikin ranta take maganar saboda sam bata taba sanin wani abu wai shi wasan jika da kaka ba. Khadija kam tunda suka fara kanta yana kasa tana wasa da carpet tana murmushi, tun da tazo gida yau ne rana ta farko da taga hakorin Abba.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now