The New Life

12.2K 954 133
                                    

Abbas

Tun sanda yaji ta ambaci sunan babansa sosai a bakinta yaji gabansa ya fadi, tun kafin kuma tayi masa bayani yayi guessing cewa sanayyar tasu bata alkhairi bace ba, wanan yasa yaji tamkar ta dauki bulo ne inchi goma ta buga masa a tsakiyar kansa. Sannan ya zauna yana sauraronta yana jin yadda take yin filla filla da duk kannin tubalan daya gina rayuwarsa akai tun ranar da aka ruguza masa waccan rayuwar daya faro tun haihuwarsa, aka rusa masa ita aka tilasta masa fara gina wata tun daga foundation, foundation din daya dora kacokam akan mahaifinsa, ashe bai sani ba foundation din na tokane, ashe bai sani ba foundation din na karya ne.

Har ta kai iya kacin inda take ganin ta gama ta tashi ta shiga gida bai iya yace mata komai ba, bai kuma iya daga idonsa ya kalle ta ba. To da wanne idon zai kalle ta? Da wanne harshen zai yi mata magana? Me zai ce mata? Ko bayan shigarta gida ma ya jima nan zaune yana kalon yadda shuke shuken da suke farfajiyar gidan suke juyi a kansa suna zagaye shi, sai daga baya ya fahimci ba sune suke juyawar ba kansa ne yake juyawa a tare da rayuwarsa gaba daya.

Da kyar ya mike tsaye ya dafe bishiyar da suka zauna a karkashinta, kawai sai zuciyarsa ta raya masa ina ma shine wannan bishiyar? Ina ma zasu iya exchange ya koma ita ita kuma ta koma shi? Da shikenan ya huta da zafin da yake ji a zuciyarsa.

Ba zai iya tuna ya akayi yaje gidansa ba, shi dai kawai ya ganshi ya shiga gida sannan ya ganshi ya shiga dakinsa ya rufe kofa sannan ya kwanta a kan carfet a nan bakin kofa yayi rigingine yana kalon silin idanuwansa a bushe babu ko digon hawaye. He wished yana da zuciya irin ta yayansa Sultan yadda zai farfasa dukkan wani abu wanda hannunsa zai iya kaiwa ko zaiji sanyi a zuciyarsa, amma shi ba haka yake ba, shi ba shaye shaye yake ba ballantana yaje ya huce haushinsa a can, sai dai ya rufe kansa away from everyone and everything har sai sanda zuciyarsata huce, which could be forever.

Haka kawai sai yaji sam bashi da shakku a duk maganganun Khadijah, sam baya bukatar jin side din Dr a labarin. To mai zaiji? A ranar bai bude kofar dakinsa ba duk kuwa da bugun da cook dinsa yayi tayi masa dan ya sanar dashi kammaluwar abinci, washegari ma haka har dare bai fito ba. Wannan yasa shugaban hadiman gidan ya yanke shawarar zuwa har gida ya sanar wa da Sultan halin da kanin nasa yake ciki. "Tun jiya da rana ya shiga daki ya rufe kansa baci ba sha har yanzu. Mu ko motsinsa ma bama ji. Gwara kazo da kan ka dan muna tsoron ko wani abun ya same shi bamu sani ba. Mu muna tunanin ma kuwa anya ba anjana ce ta aure shi ba?" Sultan ya daga masa hannu yace "ka koma gidan zan shigo in anjima koma menene zanji". 

Har lokacin da Sultan yaje gidan Abbas bai fito ba dan haka yaje kofar dakin yayi magana yace "Abbas ka bude kofa Sultan ne" amma shiru babu ko motsi, ya sake magana nan ma shiru, wannan yasa yaja da baya da niyyar ya balla kofar sai yaji motsin key sannan kofar ta bude Abbas ya bayyana a gabansa. Amma wannan ba wancan Abbas din bane mai walwala da fara'a da barkwanci, wannan Abbas din looked tired, broken and totally defeated. He looked tamkar an sauke masa duk nauyin duniya a bisa kafadunsa. Sai kawai Sultan yaji ya kasa tambayarsa abinda yake damunsa kawai abinda yake bukata shine yadda zai taimaka masa. Nasiha ya zauna ya rinka yi masa akan rayuwa sannan ya bashi shawara daya rungumi alqur'ani damin shi waraka ne ga dukkanin wata cuta kuma sauki ne ga dukkanin tsanani. Bai bar gidan ba kuma sai daya tabbatar Abbas din ya saka wani abu a cikinsa amma sai da suka kai ruwa rana tukunna har sai da sultan yace in bai ci ba zaije ya gaya wa Takawa cewa yana kokarin committing suicide in yaso sai yaje yayi wa takawan bayani da kansa.

Wannan yasa Abbas ya danci abincin kadan saboda duk duniya babu wanda yake gani da girma irin Takawa, har yanzu wannan soyayyyar da shakuwar da aka dora shi akai sanda yana yaro har yau tana nan a cikin zuciyarsa.

Sanda Sultan zai fita ne ya juyo ya kalleshi fuskarsa cike da tausayinsa yace "are you going to be alright?" Abbas ya danyi 'yar dariyar data tsaya a iya makogwaronsa yace "I don't know".

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now