The Payment

7.8K 751 16
                                    

Tun daga soro Aisha ta fara jiyo fadan Abba, daga dukkan alama kuma Khadijah yake yiwa, a ranta tace 'yau an hadu kenan, dama in dai bera yana yawo mage ma tana yawo dole wata rana za'a hadu' ta shiga ta gaishe shi bai amsa mata ba yana fada, ta tashi ta shige daki ta kai jakarta ta fito taji yana cewa "nace dake kuma ki fitar da miji inyi miki aure kinki, kince wai ke baki samu mijin aure ba, duk wadanda suke zuwa gurinki kice wai babu na aure a ciki? To in ba aure ba menene yake kawo su wajanki?"

Gwoggo tace "to ba sai ta tsaya dasu ba sannan zata fahimci halayensu? Taga wanda zata iya aura a cikin su? Ya za'ayi yarinya ita ba matar aure ba a ake yi mata kulle?" Abba yace "yaya baki san halin yarinyar nan bane ba, kunnenta kamar da itace aka yi mata shi haka take, bata jin magana ko kadan" gwoggo tace "ni dai banga rashin jin maganar ta ba, tun da nazo gidan nan lafiya lau muke zaune da ita. Ga yayarta nan data bata shekaru har biyu ita ba'a takura mata ance ta fitar da miji ba sai ita?".

Abba yace "Khadijah da Aisha ba halinsu daya ba" gwoggo tace "ita ma Aishan da ita ke da kyawun Khadijan da haka mazan zasuyi ta binta, dan dai bata da kyau ne shi yasa" Abba bai bata amsa ba sai ya juya ya kalli Khadija yace "na dai gaya miki, wata daya babu kari, ki kawo min mijin aure" Ta turo baki tace "to ai Abba kai ne baka tsaya kaji ba, ina ta so in gaya maka dama, akwai wanda zaizo ya gaishe ka, baya garine a Abuja yake zaune" gwoggo ta rangada guda "ayyiriri, kaga farar yarinya mai farar aniya, daga Abuja? Kai munji dadi wallahi, Allah ya kawo shi lafiya" Abba yace "to ina jiransa yazo, kafin yazo din kuma babu ruwanki da wasu, musamman wannan dan gidan Hakimin, in na sake ganin ki dashi shi zan aura miki" ya juya ya fita yana magana kasa kasa.

Yana fita gwoggo ta jawo Khadijah "ke wanne dan gidan Hakimin yake magana, ba dai mai kawo mana kajin nan ba?" Khadija tace "shine mana, ni mai zanyi da wannan, kinga katon cikinsa kuwa, kajinsa kawai nake so dama" suka yi dariya suka tafa ita da gwoggo kamar wasu sa'anni. Gwoggo ta juya tana kallon Aisha tace "ke yanzu kina jin kanwar taki tayi miji dan Abuja amma ba zaki taya ta murna ba" Aisha ta gyara zamanta tana kallon Khadijah tace "ina fatan ba wanda nake tunani bane ba?" Khadija ta dauke kai tace "shi din ne, sai akayi yaya kuma?" Aisha tace "yanzu kin manta abinda Umma tace miki akansa kafin ta bar duniya?" Khadija tace "ai Umma tayi amfani ne da abinda kika gaya mata, ba wai da gaskiyar magana ba, tunda aurena zaiyi ni banga abin bata baki ba, ki jira ki gani zaki sha mamaki" Aisha ta ce "Allah ya tabbatar da alkhairi" daga haka ta dauki buta tayi hanyar toilet tana lura da mugun kallon da gwoggo ta bita dashi.

Washegari tana cafeteria ta hango shigowar Kamal, kawai taji gabanta ya fadi sosai, sai kuma taji haushin kanta, menene haka kike yi Aisha? Ina ruwanki dashi, customer ne kawai ba dodo ba. Ta cigaba da aikinta, ya karaso kan kanta yace "good afternoon ma'am" ta kalleshi casually tace "good afternoon, how can I help you ?" Ya danyi shiru sannan yace "nine Kamal, da muka zo jiya tare da abokina Nura" tace "na gane ka ai, ya akayi? Abinci za'a kawo maka?" Yace "eh akawo min abincin ma" tace "me za'a kawo maka?" Yace "duk abinda kika ga yafi dacewa dani" ba tare data ce komai ba ta juya ta koma kitchen, shinkafa ta zuba masa da miya, da salad, ta hada da lemo ta bawa Binta tace ta kai masa, ita kuma ta cigaba da aiyukanta, tana jinsa yana tambayar Binta ina take amma taki sake fita, "He is just a customer" ta sake maimaitawa a ranta.

Tun daga ranar kullum sai Kamal yazo yaci abincin Aisha, amma sam taki sakin ranta dashi, haka kawai take jin sa da ban da sauran customers dinta. Wata rana sukan zo tare da Nura, wata rana kuma kowa yazo daban, in sunzo da Nuran ma sai dai ta kula Nuran amma bata kula Kamal. A lokacin ne kuma lokacin zuwan Dr yayi gurin Abba, tun ana gobe zuwan sa Khadija take shiri, ita ce har da zuwa gidan gyaran jiki da lalle, sai kace wata amarya, gwoggo ta saka ta a gaba ta lissafa mata abubuwan da zata ce masa ya kawo mata, gidan kowa da tsarabarsa, ita kuma Khadija ta zauna ta lissafa masa duk abinda gwoggo tace mata, ta kara da nata itama, babu musu kuwa yace zai kawo komai.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now