Kano

10.3K 777 9
                                    

A hankali Aisha ta juya ta koma dakin da suka fito daga ciki, babu Khadijah babu alamun ta, ta sunkuya ta dauki tray din abincin da ta kawo masa ta juya zata fita daga dakin sai kuma taji ta kasa fita ta ajiye trayn ta kifa kanta a kan kujera ta ringa rera kuka, menene laifinta a duniya, me tayi wa mutane suka tsane ta basa sonta, ita ba ita ta halicci kanta ba, da ace sanda za'a halicceta an bata zabi da sai ta zabi siffar da tafi kowacce kyau a cikin mata, amma ita ma kawai haka ta ganta, saboda haka Allah yake so ya ganta, kuma tasan wannan shine babbar jarabawarta a duniya.

Sai da ta gama kukanta ta rarrashi kanta sannan ta goge fuskarta ta dauki abincin ta koma dashi cikin gida.

A palo ta tarar da Abba da Umma suna hira, Abba yana jin shigowarta ya kwalla mata kira, ta shiga ta durkusa daga can nesa yace "ba dai har ya tafi ba? Har kun gama cike takardun?"

Ta sunkuyar da kanta tace "ya tafi Abba, tun dazu, yace an fasa maganar tafiyar tawa, yace zai kira ka a waya yayi maka bayani" Abba ya mike tsaye da sauri yace "ban gane me kike cewa ba, an fasa kamar yaya? Bayan naga takardun a hannunsa da sunanki a jiki kuma ki ce min an fasa?"

Bata bashi amsa ba sai hawaye da yake zuba a idonta, yana ganin ta fara kuka yace "me kika yi masa? Wani abun kika yi masa ko? Yarinyar banza yarinyar wofi, ana kokarin a rufa miki asiri ke kuma babu abinda kike so irin ki tona wa kanki asiri" Umma tace "Aisha me ya faru?" Aisha tace "wallahi Umma babu abinda nayi masa" Abba ya juya gurin Umma yace "ai ko menene tayi masa nasan da hadin bakinki, kece zaki shirya mata abinda zatayi saboda a fasa tafiyar, dama tun farko ai kin nuna ba kya so. Bara in kira shi a waya inji gaskiyar abinda ya faru, idan abinda zan iya bada hakuri ne ni sai in bayar, tunda ku ba abinda kuke so irin ku zubar min da mutunci na" ya dauki wayarsa yana bambami ya fita.

Suna nan a zaune sai ga Khadijah ta shigo, ga mamakin Aisha sai taga babu alamar kyalliya a jikinta, wanda bai sani ba ma zai iya dauka daga bacci ta tashi, tana shigowa ta bi Umma da Aisha da kallo sannan ta zauna tare da tambayar Aisha "lafiya naga kina kuka?" Aisha dan haushi ko kallonta ba ta yi ba, ta fahimci abinda yasa tayi mata abinda tayi mata, ita ma tayi bincike irin wanda Nura yayi kuma ta samu labarin halin Dr Abdulrazak na son mata, tasan kuma babu yadda za'a yi ya dauki Aisha yana kallonta.

Sunanan a zaune Abba ya sake dawowa, tun daga tsakar gida ya fara magana cikin gada murya "amma wannan mutumin akwai dan rainin hankali, shikenan dan yaga mu ba masu dukiya bane sai ya dauka wulakantattu ne mu?" Yana shigowa Umma ta gyara zama tace "me yace?" Yace "wai dan rainin hankali wai ya fasa daukan Aisha wai tayi kankanta, sai dai a bashi Khadija a madadin ta" da sauri Umma tace "wacce Khadijan? Ba dai wannan ba?" Yace "ita mana yake nufi, in shekaru ne ai Aisha shekara biyu ta bawa Khadija, ko dan ya ganta kamar kazar gidan mayu shine zai dauka yarinya ce. Yo ni ko daga dawanau aka sakoni ai ba zan bar Khadija ta tafi kasar waje karatu ba, yarinyar da makarantar jeka ka dawo ma sai hakura nayi na cireta na barta a gida ina kallonta ballantana ace in tura ta wata uwa duniya karatu?"

Da sauri Khadija ta sauko daga kan kujera ta durkusa a gaban Abba "abbanah na tuba nabi Allah, dan Allah ka barni inje, wallahi Abba zan nutsu inyi karatu, duk abinda nake yi a da na daina shi yanzu ai, ko kofar gida fa na daina fita tunda ka hanani" ya harare ta yace "ai kin riga kin shani na warke Khadijah, babu inda zaki dara ki bar kasar nan sai dai in da mijinki. Nace masa in zai dauki Aisha to, amma in ba zai dauke ta ba to mun hakura. Kalas"

Khadija har da kukanta, Umma tace "kayi dai dai Alhaji. To ni abin mamakin ma a ina yaga Khadijan, Aisha ko kinyi masa maganar ta ne?" Aisha ta dago kanta a hankali tace "taje gurinsa ai" da sauri Khadijah tace "na taya ta kai masa abinci ne" Aisha ta juya ta kalli Khadija tana mamakin yadda take iya yin karya kanta tsaye ba tare da tsoro ko inda inda ba.

Da daddare Nura ya kira Aisha a waya yace "so, how did it go? Yaushe ne tafiyar?" Tace "babu tafiya Nura, it is over before it even begins" sannan ta bashi labarin duk abinda ya faru, ba ta boye masa komai ba na daga makircin Khadija, har ta gama bai katse ta ba, sai da ya tabbatar ta gama sannan yace "kin san abinda nake tunani? I think all this is for the best,dama ni sam hankali na bai kwanta da tafiyar nan taki ba, you are a good person, tunda kika ga baki samu wannan abin ba then it is not Allah's choice for you. Yanzu ki tsayar da hankalinki ki yi kokari ki sake rubuta exams dinki, sai kiyi applying medicine din da kike so a nan, i am sure you can do it". Taji dadin maganarsa, dan haka tayi masa godiya suka yi sallama. Na rufe idonta tare da dora wayar akan kirjinta, a hankali ta maimaita abinda yace "tafiyar ba alkhairi bace a gare ni shi yasa Allah ya hana ni, Allah ka sada ni da abinda yake alkhairi gare ni"

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now