The New Bride

8.2K 804 67
                                    

Tunda aka tashi daga event din Aisha take jiran kiran Kamal, amma shiru, tana ta so ta kirashi ita amma kuma yawan mutane ya hanata, bata so aga tana waya da angonta ake tsokanarta. Khadija ranar bata kwana a gidan ba ma, da daddare ta shigo ta kuma daukan wadansu kayan da zata bukata ta tafi gidan Nafisa zata kwana a can, tace gidan ya cika da yawa ita kuma bata son takura. Sai wajan 11 duk ana daki ana ta hira sannan Aisha ta saci jiki ta fito tsakar gida ta kira number Kamal.

Sai da ta katse sau biyu sannan ya dauka, yace "Humairah" taji wani dadi a ranta saboda jin muryarsa da tayi, tace "na'am, ko kayi bacci ne?" Yace "na dauka ai kinyi bacci ke, tunda kunsha taro na san kin gaji" tace "a'a banyi bacci ba, ina son in kira ka dai kafin inyi bacci" yayi shiru for sometimes sannan yace "na kasa bacci Humaira, zuciya ta babu dadi" tace "anticipation ne, taron gobe ka saka a ranka shine har zai hana ka bacci" nan ma bai ce komai ba, ta sake cewa, "insha Allah za'ayi lafiya a gama lafiya" yace "Ameen. Kina yi min addu'ah dai ko?" Tace "eh ina yi maka mana, kullum in nayi sallah sai na yiwa duk wadanda suke close to my heart addu'ah sannan kuma inyi wa musulmai baki daya" yace "does that means I am close to your heart Humairah ko?" Tace "of cause you are, bayan mahaifana, sai kai da Khadija" ya danyi shiru sannan yace "nagode Humairah, na gode sosai da soyayyar ki gareni, kuma ina so ki saka a ranki cewa no matter what happens in our life, Kamal yana sonki, ina sonki sosai Humairah, dan bayan mahaifana da yakumbo ke ce ke da next position a zuciyata, kuma nasan zan cigaba da sonki ne har karshen rayuwata" ta sunkuyar da kanta tana wasa da 'yan yatsun kafarta tace "nima haka" yayi murmushin data jiyo sautin sa daga cikin wayar, yace "nasan da a gaba na kike da yanzu kin rufe fuskarki da hannunki, saboda kunya ko?" Ai kuwa sai ta rufe fuskar tata kamar yana kallonta tana dariya, yace "ina son kunyar nan taki Aisha, ina son komai naki, please no matter how much hard our life will become, don't change, kar ki bar zaluncin azzalumai ko cin amanar maciya amana ya chanza maki innocence dinki" tace "ni kam waye zai zalunce ni? Waye zai ci amana ta? Koma waye ban damu ba tunda ina tare da kai, ka fiye min komai a duniya Kamal, as long as ina tare da kai bana jin akwai abinda zai taba zuciyata" yace "and you will always be mine, you will always be my Humairah, forever and ever".

Sun dan jima suna hira sannan yace bara ya kyale ta taje tayi bacci, kar gobe ta kasa tashi, ita ma tace masa yaje yayi bacci kar gobe ya makara zuwa gurin daurin aurensa.

Washegari tunda Aisha ta tashi ta assuba bata koma ba, tana kallon anata shirye shiryen abincin baki da kuma abincin breakfast amma bata tashi ta taya su komai ba, kawai jin ta take babu dadi, wani irin missing ummanta take yi, taje can karshen daki ta hade kai da gwuiwa ta fara rera kuka a hankali marar sauti, wai yau za'a daura aurenta amma babu ummanta, ta ringa lissafo abubuwan da umman zata yi da ace tana da rai, gaskiya maraici ba karamin ciwo ne dashi ba musamman rashin uwa.

A haka aunty Bilki ta shigo ta same ta, ta zauna ta dafa ta taji jikinta har ya fara zafi tace "Aisha? Lafiya kike wannan kukan haka? Wani abin kike so?" Tayi shiru bata ce mata komai ba, aunty Bilki tace "ummanki kika tuna ko?" Nan ta gyada mata kai a hankali, aunty Bilki tayi ajjiyar zuciya tace "nasan yanzu da ace tana ganin ki da babu komai a zuciyar ta illa farin ciki, farin cikin yadda rayuwa take tafiyar miki, farin cikin cewa yau za'a daura miki aure a kaiki gidan mijinki. Babu abinda kowacce uwa take buri akan 'yarta irin wannan ranar, ranar da zata kai ta gidan mijinta lafiya lau. To ki saka a ranki cewa kamar ummanki tana kallonki ne kamar tana tare dake ne kuma zata rakaki har dakin ki, kinga kuwa ai ba zata ji dadi ba kuma in taga kina kuka. Nafi son ki zama mai godiya ga ubangijinki, ki ringa tuno abubuwan alkhairin da suka same ki a rayuwa sai kike godiya akan abubuwan da kika rasa, sai kiga Allah ya kara buda rayuwar ki"

Haka tayi ta mata nasiha har sai da taga ta daina kukan ta share hawayenta, ta saka ta ta tashi ta shiga wanka ta fito ta shirya tayi kwalliya dai dai misali da wani jan lace dinta mai adon fari da baki, dinkin yayi mata kyau sosai, tayi murmushi data tuno cewa Kamal ne ya dinka mata, ta yafa farin mayafi ta saka sarka da dan kunne na fararen stones, ta fesa turarenta sannan ta koma ta kwanta ta rufe idonta kamar mai bacci amma ba baccin take ba, tunanin sabuwar rayuwar da zata shiga take yi, tana jin tsoro a ranta amma kuma in ta tuna da cewa Kamal will be by her side sai taji ta manta da damuwar.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now