Two

377 30 1
                                    

Episode two
WAYE SHI(shaffik ko Ahmad)
Na: Bintnagz (Hasna mansur nagoda)
Wattpad @bintnagz

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"

**********

Da alhaji ahmad yaga abun habiba bashi da niyar karewa, hakan yasa ya salami Ibrahim ya kore shi yayi masa fata fata ko kusa ba'ayi rabuwar arziki ba dan sai da ya ci masa mutunci gaba da baya.
Tun daga ranar ita kuma ta shiga cikin wani yanayi da ya hada da laulayi da take fama da shi, aman safe daban na rana daban na yanma da ban, ga zazzabi ga ciwon kai kamar me, cikin lokaci guda ta zabge ta rame ta lalace, shi kuma alhaji ahmad ya zata duk cikin kewa ne da son da take yiwa Ibrahim, lokaci take bukata domin kuwa yana kyautata zaton duk yarinta ce irin ta habiba, kuma mallan bahaushe yace shi so jifa ne, da ka sunkuya sai ya wuce.

Abu yaki ci yaki cinyewa hakan yasa alhaji ahmad yasataba gaba ya kaita asibiti, nan akayi mata yan gwaje gwaje aka tabatar musu da cewa habiba tana dauke da cikin sati uku...
Nan take alhaji ahmad ya saki jiki ya fadi, kallo ya koma kansa, dama ya dade yana fama da ciwon hawanjin tun rasuwar azare, sai dai yana controlling dinshi...
Nan da nan aka bashi gado a asibitin, likitoci sukayi ta kokari a Kansa dan ganin an ceto ransa.
Bayan kwana daya ya farfado da shanyewar barin jikin sa na hagu.
Habiba da abba khalid sunyi bakin ciki kwarai da gaske, ama me fatan su shine allah ya bashi lafiya...
Habiba kuwa bata bakin cikin dan da ke cikin cikinta domin kuwa dan masoyinta ne hakan yasa take maraba da shi take son abinta take kuma kula dashi...
Bayan sati daya alhaji ahmad ya sami kwarin jiki, dan Alhmdulillah jiki yayi kyau sosai, dan har an salameshi sun koma gida, hakan yasa yace abba khalid ya kira masa Ibrahim, shiru shiru babu ibrahim babu labarinsa sai chan dare saiga Ibrahim ya sami karasowa, koda ya karaso babu sanu bare ya jiki haka Ibrahim yazo ya tsaya masa a tsaye yana cika yana batsewa, yasa aka yi masa kiran habiba sannan ya sa su a gaba ya kalle su yace, tunda sun zabi aure, sun nuna cewa aure suke so har a aikace sun nuna hakan toh ya basu izini, ba sai yayi musu dole ba ya yarda su auri junan su, ya kalli Ibrahim yace yaje ya turo masa maganatan sa a sa ranar aure.
Ya kuma jadada masa rashin adalcin da Ibrahim yayi masa a rayuwa, lalata bata kare ba har sai da yayi wa yarsa ta cikin sa juna biyu, a gidansa a karkashin sa.
Toh wannan shine hukunci mafi sauki da zai iya yi masa sauran saidai ya barwa allah.
Koda suka fito waje ita habiba sai murna take dan kuwa an amince mata da auren abun kaunar ta..
Ibrahim ya naga baka murna da zancen abba ne...
Bai ko juyo ya kalle ta ba yasa kai ya fice daga gidan...

Shiru shiru yau sati uku kenan babu Ibrahim babu labarin magabatansa  hakan yasa abba khalid da alhaji ahmad sukayi tataki har zuwa gidan su ahmad, aka kuwa tarbesu cikin karamci da mutuntawa...
Nan suka kwashe labarin abinda ke tafe da su, suka fada musu...
Da yake iyayen Ibrahim masu mutunci ne sun kuma kama girman su, hakan yasa suka jimanta abun suka kuma ce tabass zasu tsawatar wa Ibrahim kuma mako mai zuwa insha allah za'a tsaida ranar auren su, domin kuwa baza'a bata lokaci ba.
Sati na zagayowa aka saka ranar Ibrahim da habiba, dangin habiba kuwa sukace babu abin da zasu karba daga wajen su sai sadaki a haka aka yarje.
Da yake anso a boye lamarin cikin habiba hakan yasa aka danyi taro duk da ba na gani a fada ba, dan har saida mutane sukayi tsogumin yanxu duk kudin ubanta bazai nuna mata gata ranar bikin ta ba ashe dama son karya yake yi mata haka dai akayi ta cece kuce a dangi....
Ranar kai amarya aka dauki amarya aka kaita daya daga cikin kananun gidan alhaji ahmad dake kuntau, duk da abun da alhaji ahmad yake yi wa habiba ita bata ji bata gani soyayya ta ruga ta rufe mata ido, ya bata duk wani abu da zata bukata a rayuwa, a daren Kaita yace mata kada ta sake ta dawo masa gida da cewar tana neman wani abu daga wajen sa ko ya bata wani abu, ya kalli abba khalid yace ko kai khalid ban yafe maka ba idan har ka sake ka temaki habiba koda bayan raina. Ta ruga ta yi zabi wanda take ganin shine zabin rayuwar ta, sai mu barta ta nemi farincikin rayuwarta.
Abun ya mata ciwo gaskia ama gani take kamar bazata nemi wani abun ba ma a wajen su ma, tunda ta ruga ta sami abunda take so.
Daren amarci daren ake so ko wane amarya da ango su halara a gidan auren su na sunnah ama a daren ranar habiba ita kadai ta kwana.
Haka rana ta kuma tafiya shiru babu Ibrahim babu labarin sa, wayarsa a kashe bata shiga..
Sai a dare na uku ya sami shigowa.
Tana ganin sa ta tarbe shi cikin murna da shaukin sa ama me? Sai ya yana ta ya ture ta har takai kasa, ya kuma hade fuska kamar damamen tuwo, ta dago zatayi magana, taga ya fara zagaya gidan yana tabe baki...
Yanzu duk kudin ubanki ya rasa gidan da zai baki sai wannan, idan bai baki arzikin sa ba wa zai bawa tunda kekadai allah ya bashi, kwan haihuwarsa ya mutu.
Sai da ubanki yaga baki da amfani shine zai zo yana kananan murya yana wani cewa in aure ki.
Wato ya raina ni ban kai matsayin auren ki ba sai mai kudi??
Toh yanzu gaki nan dake da talakan duk daya tunda kin ruga kun tashi daga aiki, shashasaha...
Gafara ki ban guri ya kuma hankade ta.

*****************************************************
To be continued on Sunday insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Onde histórias criam vida. Descubra agora