Eighteen

167 19 2
                                    

Episode eighteen
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡYa sauke wani mugun lumfashi mai zafi mai cike da takaici yace toh meye haka, meke damuna, kodai sace ni akai aka dawo dani, wani malolon bakin ciki da takaici suka zo masa nan ya rasa yanda zai yi ya hadiye.

Ya kuma tambayar kansa toh wai kodai aljanun ne da shi da suke yi masa barna haka, suke kuma yi masa wasa da hankali.
Ya fito fallo ya ya kunna kira'ar karatun alqurani ya sami guri ya zauna.
Kan sa ya dau chaji dan ya rasa me ke damun shi, duk abin da ya dako sai yaga ba hakan bane bai ma yi ma'ana ba,?dan har tunani yake yi kodai kwakwalwar sa ta fara samun matsala ne, shin ko ya fara hauka ne da kwakwalwar sa ke fada masa ba dede ba.

Waya ya dauka ya kira Attahir ,bugu daya Attahir ya dauka, ganin yanda Attahir yayi masa magana kuma ya gane abun da yake fada ya tabatar da lafiyar kalau, haka sukayi sallah har Attahir na ce masa gobe zai shigo masa.

Washe gari da wuri ya tafi aiki ko da ya shiga yaga yaga yanda ake gudanar da al'amura da aiyuka yaga ba haka ya tsara ba, ba kuma hakan yake so ayi ba, dan wannan ba tasrin sa bane. Babu abun da ya bata masa rai sai yanda mutane ke masa fararan faran har da tsokanar sa har masu gadi da masu goge goge, wanda ya dace da wanda bai dace ba
Shi kuwa ya daure ya murtike fiska ya, abun na kona masa rai.
Yana shiga office dinsa ya kira sakataren sa yace ya fada masa abun da ya faru kwana biyu da suka wuce.
Shi dai kuwa yayi mamaki kwarai da tambayar ama ganin ogan sa ne kuma bai masa alamun wasa ba hakan yasa yace masa ai kwana biyu bai sami shigowa ba sai jiya yayi reporting...
Ya daga kai ya kalle shi yace kamar ya ban shigo ba kwana biyu da suka wuce a fusace har yana dukan tebir...
Shidai yayi kasa da kai yace yalabai ai abun haka yake dan sai jiya ka sami shigowa, sai dai idan ka manta ne....
Cikin baccin rai ya ce masa ya fita ya bashi guri, ba shiri ya fita summ summ.
Haka ya karaci ranar sa cikin kunci da tunane tunane kala kala, kowa sai dari dari yake da shi dan yanzu ne ya dawo yanda yake, dan suma sunyi mamakin sauyawar sa.

Koda ya koma gida a bakin gate yaga Habubakar yana tsaye yana jiran dawowar sa, yana ganin sa yayi saurin karasawa bakin motar tasa yace, Ahmadu tun danzu nake tsaye ina ta tumayar ka, ya kamata kayi sauri muje dan yanzu naga yan mata sun fara yin nan.
Wani wawan kallo shaffiq ya manna masa tare da fadin waye kai , waye kuma ahmadu ??
Habubakar yayi dariya yace kaga sarkin barkwanci ka shiga ciki ka sauyi kaya mu tafi a hanya mayi barkwancin...
Ya kuma manna masa wani sakaren kallo yacr kaga malan yi nan ka san inda dare yayi maka kar na sasaba maka.
Ya bude gate dinsa ya shiga ya rufo gate din ya barshi a wajen.
Shi kuwa Habubakar bai ji komai ba dan gani yake kamar wasa yake haka ya karaci tsayuwar sa a kofar gidan har ya gaji ya tafi.

Da yake Nadiya sunyi da ahmad duk yanma zasu dinga haduwa da a bakin rafi hakan yasa ta gama aikin ta da wuri, ta dan gyara fuskar ta tayi bakin rafi, tayi ta jiran zuwan sa bai zo ba har, dare yayi shiru. Hakan yasa ta koma gida ba tare da taji dadin rashin ganin sa ba.
******
Ya tun safe inna Tani ta tafi bini dan yanzu mako mako take zuwa karbar maganin mado, jiki mado sai kara tsanani yake yi baya umm bare umummm ga ba tafiya yana kwance kamar kayan wanki, dan ma inna tani tana iya bakin kokarinta a kan mado, dan yanzu har ta fara sa kadarar ta akasuwa tana siyarwa dan ta yi wa mado magani.
Kasan cewar inna tani batada lokacin kanta ma duk mado ya ruda ta shi yasa bata da lokacin zagi ko cin zarafin nadiya, saidai uwar bauta da take saka ta.

Tana tsakar gida tana linke kayan shanyar inna tani dana mado ta jiyo tarin mado daga daki, jin tarin yayi yawa yasa, tayi saurin tashi ta debo masa ruwa a randa ta kai masa, ga mamakinta sai taga jini na fitowa ta bakin mado hakan yasa hankalinta ya tashi ga tari yanayi kamar ya shake shi, ga jini yana tarayowa...
Hakan yasa ta kidime ta rude, tayo waje da gudu tana neman temako...

Rugar shiru ba kowa ga makotan su inna tani bata mutunci da su, ta kali gabas da yanma, kudu da arewa babu kowa hakan yasa tace bari taje wajen kakarta ko zata sami temako duk da inna tani ta hana ta zuwa.
Tana cikin gudu taga mota tayo kanta gadan gadan an dalle mata ido da haske, ko kakautawa ba'ayi ba hakan yasa tayi mutuwar tsaye dan har ga allah ta zata kade ta za'ayi, ta yi saurin rufe idon ta da tafin hannun ta...

Ya fito a fusace yace
Ke baki da hankali??????
Kinsha wani abu ne...????
Bai ga fuskar ta ba hakan yasa bai gane ta ba...
Ta zame hannun ta daga fuskar ta a hankali, ta kalle shi..
Bata mai kallo mai kyau ba shi yasa tace
Ahmad dan allah ka temake ni mado bashi da lafiya gashi ciwon yayi tsanani, sai tarin jini yake yi, gashi inna tani bata nan, idan ta dawo ta tarar da shi ya mutu cewa zatayi ni na kashe shi...
Cikin wani yanayi yake kallonta, ita ce yarinyar da ta fara kiransa ahmad...
Jin kansa zai fara sarawa yayi saurin cewa muje ina ne gidan ku??
Gidan mu, sai kuma tayi mamaki meyasa zai tambaye ta gidan su bayan ya fi kowa sanni ina ne gidan su.
Kawai tayi gaba...
Ganin zasu ci lokaci ne yasa yace kinga mu shiga mota..
Ta juyo ta kalle shi a tsorace, ta ga ba alamar fara'a ko wasa a fuskar sa hakan yasa tace toh dan ita ce mai bukata.
Suna shiga ya shiga gidan kai tsaye, ya kalli yanayin gidan cikin sakanni ya girgiza kai yace ina mara lafiya, ta nuna masa wata yar rumar kwano tace yana ciki...
Ya shiga yaga yanayin da yake ciki, ba shiri ya cicibe shi ya fito yace muje asibiti....
Asibittttttiiiiii.....
Ta fada da karfi cikin mamaki...
Ta zaro ido ta fara ama.....ama....
Ke ki shige mu tafi ni kar ki bata mun lokaci, wannan shi kadai ne taimakon da zan iya yi miki....

Tayi tsuru tana kallon sa sai yanzu ta kara gani banbancin su muryar shaffiq kakaura ce ga kuma jan ido, tabass wannan ba ahmad bane....

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now