Thirty eight

151 15 0
                                    

Episode thirty six
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)
"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

A gigicd ya bude ido, kansa ya ji yana dan mai zafi, ya dan yi mika, ya kalli agogon hannun sa, 11:30 na safe...ya tuna da nadiya, Nadiya ya fada a fili a dan firgice....

Juyawar da zai yi ya gan ta a gefen sa ta zuba masa ido, tana kallon inda dramar zata kare...
Nadiya...!!
Ohhh mun gama ko, gida muka nufah ko, yaude na cikia alkawari...???
Yayi smiling dinshi da duk duniya babu abun da take son ganin yayi in ba shi ba...

Ahmad ta fada a sanyaye....

Ya dago fararen idon sa wanda suka sha banban da na shaffiq wanda suke dauke da sonta, ya kalle ta.
Ta gama tabattar wa kanta komai, abun da take zargi hakan yake, Ahmad da shaffiq mutane ne daban daban da suke rayuwa a jiki daya, ashe karya ne da suka ce mata su yan biyu ne, tun da take a duniya bata taba ganin wannan alamari ba, dan ma tanada juriya, wa zai tsaya ya kalli rikidar Ahmad da shaffiq ba tare da ya tsorata ba.
Wasu hawaye masu dumi suka sakko mata, ta sa hannu ta share, ta hadiye wani malolon takaici tace, Ahmad sauke ni anan dan Allah, ta fada ranta a bace.....
Meyasa, kedai ki bari mu karasa nayi alkawarin zan maida wa inna tani ke da hannu na, zai fara yi mata barkwancin nasa da ya saba, tayi mai wani ihu cikin tsawa tace
NACE KA SAUKE NI ANNAN.....!!!
Ba shiri ya tsaida motar, cikin mamaki ya kalleta, ta hada uban gumi hawaye kawai idon ta ke zubdawa...
Nadiya....
Nadiya meya same ki...
Nadiya nayi miki wani abu ne da ya bata miki rai....
Bata jira jin mai zai ce ba kawai ta bude mota ta fice....
Ba shiri shima ya bita yana kiran sunnan ta....
Nadiya me ke damun ki, meya faru nadiya, gabanta ya sha ya durkusa yana hada ta da allah ta tsaya...
Ta share hawayen idon ta tace...
Har tsawon yaushe kake son boye mun
Har tsawon yaushe kake shirin munafurta ta
Ko da yake bukatar ku ta biya tunda kunyi wasa da ni,kun mayar da ni wata shashasha gara da bansan abun da nake yi ba, Ahmad wllh nafi karfin ku tunda duk dangi na ba mai tarihin aljanu bare bori, bazaku taba yin tasiri a kaina ba, insha allahu, aljani bashi da wurin zama a tatare dani, kullum neman tsari nake daga irin ku, allah ba zai taba baku sa'ar cin galaba a kaina ba....

Mikewa yayi tsaye dan ji yayi kansa na shirin juyawa, Nadiya kinsan kuwa abun da kike fada, shi kwata kwata bai kawo a ransa ta gane ba...
Ganin juwa na kokarin diban sa yayi saurin jin gina da wani itace...
Ita kuma ina har tayi masa nisa lokacin da ya bude ido a matsayin shaffiq......
Koda ya bude ido mota ya shiga bai tsaya ko ina ba sai kano gurin mahaifiyar sa...

Yana shiga yayi horn aka bude masa gida, kai tsaye bedroom din mummy yayi ya tarar tana toilet, ya fada kan gadon ta dan duniya duk tayi masa zafi, alamura duk sun dagule masa, kwata kwata ya kasa tara danuwar sa waje daya balantana yai maganin damuwar tasa, ji yayi duniya da rayuwar duk basu da amfani, wane irin almari ne wannan ke faruwa da shi ko acikin litattafai da kuma finafinai babu irin shi....
Tsuntar kansa yayi da fadin Alhmdulillah Alhmdulillah ba addadi dan bashi da abun da zai cewa allah Sai godiya....

Mummy ta fito daga alwalar da tayi,
A'aha saukar yaushe...
Dagowar da yayi ya kalle ta fuskar nan a chukune babu alamun rahama a cikin ta yasa ta tasorata tace, subahanallahi shaffiq, meke damun ka baka da lafiya ne...?
Wasu hawaye suka zubo masa kana ya bude baki yace,
Mummy allah ya isa bazan taba yafewa mahaifina ba, shine ummulabaisin din duk halin da nake cikin yanzu, mummy rahamar allah bazata taba kasancewa tare da shi ba idan har ina cikin wannan yanayin....
Subahanallahi shaffiq ka kuwa san me kake cewa, ka sha wani abu ne, mahaifi fa mahaifine shaffiq...
Wani sabon babin kuka ya bude, dayake uwa uwace ba kowa yake amsa sunnan ba, itama kanta ta tsunta tana zubar da hawaye, sunfi minti goma suna zubda hawaye, zuciyar shaffiq tayi zafi da nauyi matuka, ji yake kamar ya hadiye zuciya ya mutu, wannan bakin cikin duniya da mai yayi kama.
Mummy tayi hugging dinshi tana shaffiq kayi hakuri duk halin da kake ciki duk ni na janyo maka lefinane, nayi danasanin haduwa da mahaifin ka aman bantaba yin danasanin haihuwar ka ba, nabari soyyaya ta tude ni, na amince da mahaifin ka kafin aure, kaico na shaffiq ka gafarta mun....
Shaffiq ya dago idon sa da sukayi jajawur sukayi shabe shabe da hawaye ya kalle ta yace, mummy kinyi ciki na kafin ki auri mahaifina, ta gyada masa kai da kyar cikin kuka mai kunci, tare da share hawayen ta tace, shaffiq kayi hakuri, kayi hakuri dana, kayi hakuri shaffiq, nan ta kwashe labarin duk abin da ya faru a baya ta dada masa....
Sunyi kuka sunyi kuka, har suka godewa allah, sai da suka koshi ta tashi ta share hawayen ta tace shaffiq komai ya riga ya wuce hakan yasa muka gina sabuwar rayuwar mucikin inganci da ci gaba, yanzu ka tashi ka shiga kayi wanka ka fito kaci abinci, bana son sake ganin hawayen nan ko magana baya a idanun ka, kaji ko....
Ya gyada mata kai, ita kuma ta fice....
Sai da ya kusa daukan hour daya kafin ya sako, cikin pajamas din shi...
Babu wanda ya tanka wa juna cikin su mummy dai kawai abinci take kaiwa baki, da dan tasan me ke shiga cikin nata ba.
Glass din fresh milk din danke hannun sa ya danke a hannun sa, ya shiga cikin wani tunani mai zurfi, bai san sanda ya matse cup din glass din ba da hannun shi har ya fashe, jini da madarar duk suka hade,
Shaffiq lafiyan ka, akan me zaka yi wa kanka rauni, ya mike a razane dan shima ya tsorata, tashin da zaiyi yaji juwa na diban sa, kafin yayi balancing kanshi innnaaaa har ya fadi...
Mummy tayi kanshi da sauri tana kiran sunnan sa, shaffiq shaffiq cikin rudu, duk kiran da tayi masa bai fardado ba, balantana yasan me akeyi...

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now