Thirty three

126 13 0
                                    

Episode thirty three
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Bayan kwana biyu suka dawo, suka same ta a office dinta, tana zaune tana jiran su dayake sun dan makara.
Bayan sun gama gaisawa, ta kalli Attahir cikin wasa tace masa zaka iya zama kuwa yau, dan naga wanchan karon har aka gama kasa cewa komai kayi...
Shida shaffiq suka yi dariya...
Sai kuma tace ya taya ta kashe fitila toh....
Ta kunna table light dinta sannan tace, shaffiq maganin da na baka shi zai hada maka memories dinka da suka tarwatse waje daya, yanzu zaka shiga cikin kwakwalwar ka ka gano mana abun da ya faru shekarun baya da suka wuce, nasan zai maka wahala ama ka daure, babu wanda zai iya sai kai, kuma hakan shi zaisa mu gano matsalar ka....
So yanzu after the count of 3....
Tana kirga uku, tayi snapping yantsaunta biyu ya shiga kundin brain dinsa

Abba khalid ya ajiye ni a kofar gida mun dawo daga makaranta ni da Attahir.....
Na shiga gidan da gudu naji ihu da kukan mommy, as usual dama haka abba na yake sata a gaba yana dukan ta kullun, idan naje zan tare mata har ni yake hadawa yake duka, bani da wani buri da fata sai na girma nima in fara dukan abba na, hakan yasa nake ta hakuri ina addu'a allah yasa na girma...
Ko da na shigo gida ranar naga dukan ya kara yawa hakan yasa na dauka abun duka na hau dukan sa dashi..
Ko da yaji zafin dukan yana dagowa ya hankada ni na bige da bango jini na ta zuba...
Ban farka ba sai a gadon asibiti....
Cikin ikon allah da maganin da Dr Fauziyya ta bashi bai wani sami hatsaniya ba haka ya bude idon sa sumul kalau....

Kallon shi kawai suke yi, dan ita kanta Dr Fauziyya ta tafi nata tunanin...
Attahir kuwa wasu kwala yayi saurin sharewa tare da gyara zaman sa yana wayancewa.
Likita ta dan lumfasa kana ta jawo takar da ta yi rubutu, kana ta mika masa
Shaffiq you did very well yanzu, ga wannan gwaje gwajen kaje kayi, akwai EEG aciki akwai CT SCAN, da MRI sai kuma skull xray ka je kayi ka dawo mun da saka makon...

Cikin awa daya da rabi suka karbi results din gaba daya, dayake private lab suka je, ganin lokacin bai kure ba yasa suka koma asibitin.

Sai da suka jira ta gama attending patients dinta sannan suka bata results din...
Ta dauki lokaci mai tsayi tana comparing results din gaba daya tana nazari a kansu, tana jinjina kai, sai da ta kamala kana ta gyara zama ta kalle su duk su biyu sannan tace... 

Shaffiq kana da cuta ko da yake bazan kirata cuta ba zan iya kiranta da matsala a turance condition.
Attahir da ya kagu da jin wannan matsala ya katse ta da muna jinki dakta wace cutace wannan...,

Dissociative Identity disorder (DID) wacce aka fi kira da Multiple Personality Disoder.

Attahir ya kuma katse ta da me hakan yake nufi.....
Abun da ake nufi da DID shine mutun ya kiriki wani mutun ko wata hallita daga jikin sa, ma'ana ya raba kwakwalwar sa zuwa kaso daban daban...
Abun da ke jawo hakan kuwa shine, mutun zai kasance cikin matsananci hali, ko cikin damuwa da ya ke a dawame acikin ta, ko kuma wani abu da yake son yayi ama bashi da hali bare damar yin hakan, toh hakan zai sa ya kirkiri wani ko wata halitta daga jikin sa domin ya yi masa wannan aikin da bazai iya ba, ko ya futar da shi daga cikin wannan damuwar ko halin da yake ciki.

Abu na biyu da zai iya janyo hakan shine hatsari, ko buguwa, ko faduwa da yara kan yi suna kanana, duk dai wani abu da zai zama lahani ko illa gaurin kwakwalwa da tace a cure waje daya, toh kwakwalwar zata rabu zuwa kashi daban daban, wansu takan rabu gida daya har zuwa gida biyar takan kasu....
Sai kuga mutane suna ta fama da mutane daban daban a tare da su, ba tare da sun san me ke faruwa ba, sai kaga ana aljanu ne da mutun, yana da sarauniyar kaza, yana da kaza kaza duk atare da shi alhalin ba haka bane, wannan ce matsalar da sai sun zo asibiti za'a magance musu ita.

Attahir ya daga kai ya kalli shaffiq ta ya kasa cewa komai sannan yace toh likita me kike ganin ya janyo wa shaffiq wannan matsalar?

Toh gskia abin da ya janyo wa dan uwan ka hakan shine, abun da muke kira da trauma, a turance da kuma childhood abuse din da yayi facing, wanda ba lefin kowa bane sai lefin mahaifin sa.

Kasancewar mahaifin shaffiq mutun ne mai cin zarafin mata, da cin mutuncin mahaifiyar sa da yake yi, da abusing dinta da yake yi a gaban sa, a koda yaushe burin shi ya ramawa mahaifiyar sa ama bashi da wannan ikon,
Hakan yasa ya sami trauma duk ida yaga ana dukan mata sai ya sami panic attach, ko yaga mace tana cikin mawuyacin hali tana bukatar temako...
Kwatsam sai ranar ya yi karfin halin tare wa mahaifiyar sa dukan mahaifinsa, wanda ba shi yayi wannan yunkurin ba lokacin ya kirkiri Ahmad domin yayi masa wannan aikin, a lokacin shi kuma mahaifin ya hankade shi har ya bige...
Buguwar da yayi yasa kwakwalwar sa ta rabu biyu...
Ta zaro CT scan din ta nuna musu yanda kwakwalwar ta rabu zuwa biyu alhalin daya...
Awancen lokacin likitoci sunyi iya bakin kokarin su wajen ganin sun tsaida brain guda daya, har allah ya basu iko suka tsaida brain din Ahmad...

Kwatsam sai ranar ya sami panic attack a gero da ya dade bai yi ba kasancewar an ruga an tsayar da brain dinshi gashi kuma ya sami change of environment...
Ganin nadiya na bukatar temako yayi triggering brain dinshi mai temako, ya bude...
Daga lokacin ahmad ya kuma dawowa, SANADIYAR NADIYA!!

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now