Thirty seven

140 13 0
                                    

Episode thirty seven
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)
"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Yau kwana goma kennan, Ahmad na cin karon sa ba babaka sai soyayya suke zuba wa shi da abar kawunar sa Nadiya, nadiya ta kamu kwarai da soyayyar Ahmad kwarai da gaske da duk duniya bata taba zaton zatayi wa wani son da take yi masa ba, wani shauki da annuri na haske da ke tashi daga cikin zuciyoyin su idan suna tare zan iya cewa wannan na daban ne, basu taba tunani soyayya wata aba bace dake sanya nutsuwa a cikin zuciyoyin masoya ba, duk wata damuwa da kunci da Nadiya take shiga a baya wajen inna tani da mado toh yau allah ya wayi gari duk banu ita, daga ita har inna tani Ahmad yazame musu tamkar dan uwa, dan ita kanta inna tani alfari take da shi, ba wai dan kudin sa ba ko dan wani abu nasa ba, a'ah haka kawai wani son sa ya ratsa ta, da take masa kallon da shima.
Yau suna tafe a hanya shi da Nadiya sa, suna tafe yana tsokanar ta kamar yanda ya saba, ta zaro reshe ta bishi da gudu tana sai ta duke shi, shi kuma sai zule mata yakeyi yana gudu yana dariya...
Har ta gaji da gudun ta fara haki ta tsuguna, shima yana dariya ya zo ya tsuguna...
Ance mutun ya dunga cin abinci ko yayi kiba ama yaki ba dole ki dunga haki ba....
Ta tashi da sauri tare da rike shi tana, nakama ka nakama ka shi kuma dariya ta bashi da ya tashi ya sunkuce ta gaba daya ya daga ta kamar wata jariya, sama ya cilla ta ya chafe yayi hajijiya da ita ita kuwa ihuuu kamar ranta zai fita ta ruke shi gamm, sai faman hada shi da allah take ya sauke ta...
Zaki kara toh...
Wllh bazan karaba dan allah ka sauke ni....
Toh ai ke kika rike ni ki sake ni mana ji yanda kika cukukuyeni fah Nadiya...
Ba shiri ta sake shi...
Yayi dariya sannan ya sauke ta...
Ta dan harare shi...ta zumburo masa baki...
Ya bita a baya yana ya hakuri, haba matar...
Gobe zan kaiki company ko kin fasa zuwa...
Ta juyo da sauri tare da fadin Allah zani ....
Yayi murmushi ya gyada mata kai yace toh shikenan allah ya kaimu goben...

Murna kamar ta kashe ta sabi da yace mata zai kaita company taga yanda ake hada mayuka da turaruka, da sasafe ta tashi ta shirya, cikin bakar doguwar rigar da ya siya mata, ta yi kyau sosai abun ta, dan har sai da ta dan jira shima kafin ya karaso...
Ya shiga ya gaishe da inna tani sannan ya dauke ta suka tafi...

Da yake yau asabar kamfanin tsitt ba kowa  sai cleaners da masu gadi ama duk wasu ma'akata duk basa nan, duk sunyi programming machine dinsu sunyi timing dinsu sun tafi.

Chan ciki ya shiga da ita,wasu manya manyan engine da suke markada cemikals, suna juyewa cikin wani abubu, su da kansu suke aiki ba tare da wani ya ce musu ga abin da zasu yi ba,wani engine zai debo ruwan zafi wani kuma ya kawo powdered chemicals hama za'a zuba cikin wani engine din abun gwanin ban alajabi, sai kallo take tana nazarin abun lalle diniya ta cigaba, wayar sa tayi ringing yasa hannu a aljihu zai dauka, ita kuma tayi gaba tana ganin ikon allahn da bata taba gani ba..

Daukar wayar da zaiyi sauyi yanayi ya ziyarce shi, kansa ya juya cikin ciwo mai tsanani, duhu ya ziyarci idanun sa hade da taurari, luuu yazo zai fadi da tayi saurin tare shi cikin hanzari tana ahmad zaka fadi...
Kanta ya fado suka bigi wani inji mai kai ruwan zafi ya goce, jin karar ta yasa shi dawowa cikin hayacin sa, shi da ita duk a kasa, kansa a kan kirjin ta...
Ganin ruwan zafin nan na niyar kwarararo musu yasa ya zabura a fusace ya mike ya ja hannun ta suka bar wajen.....
Wani azahaben ciwo hannun ta ke mata, gashi ya rike hannun gammm har sai da suka fito haske...
Cikin kasai taciyar muryar sa ya ce Nadiya baki da hankali mai ya kawo ki nan wajen, kinsan kuwa hatsarin gurin nan, yanzu da zuwan zafin na ya zubo akan ki fa...
Wasu hawaye zafafa suka subo mata kan kumatun ta...
Ga zafin ciwo ga takaicin wannan mumunan al'amri da take fuskanta daga wajen shaffiq da Ahmad lokaci zuwa lokacin, wanna shine wajen karo na 4 kennan...
Idon sa ta bi da kallo, kwayar idon ta rikide ta koma ta shaffiq, komai ya rikide ya koma na shaffiq babu ko shakka shaffiq ne wannan...
Kukan yaci karfen ta, ba shiri ya sakar mata hannu ya bita da kallo...
Nadiya...ya fada kasa kasa....
Meya faru...
Sai a lokacin ya dubi hannun ta yaga jinin da ke zuba ga kuma uban kumburi da yayi...
Subahanallahi ya fada a rude...
Ya taba aljihun sa yaji akwai key din mota, ba shiri yace su tafi asibiti....
Har suka isa asibitin nan nadiya kuka take...
Tabass komai yazo karshe yau din nan dan ta gaji da wannan rainin hankalin na bayin Allahn nan...
Shi dai bai ce komai ba har suka isa baban kemis dake kan mararabar gero, inda allah ya takita ba karaya bace kwai dai buguwa ce hakan yasa, suka yi mata dressing din ciwon sannan suka daure mata hannun, suka kuma bata magunguna sannan.
Koda suka shigo mota kasa cewa komai yayi, ita ma sake saken yanda zata bullo masa da zancen take, ko aljanu ne su to yau ta zama rana ta karshe da zasuyi wasa da ita haka....

Shaffiq......, 'ta kira sunnansa'
Ya dago oilly eyes dinshi ya kalle ta, da duk jikin sa yayi sanyi, dan yau ko mai zaice yasan ba fita zai yi ba....
Ahmad ........, 'ta kuma kiran sa.....'

Wata kwala ta zo mata ido da tayi saurin sharewa tare da fadin meye hadin ku, meyasa kuke son yin wasa da hankali na dan allah, me nayi muku da na chanchanci haka....!!
Shaffiq kace mun abun da nake zargi ba haka bane, dan allahh, kace mun ba haka bane......
Kuka yaci karfin ta da ta fashe cikin kwala.

Hankali sa idan yayi dubu ya tashi, dan duk ta chaza masa kwakwalwa...
Wannan ne karo na farko da ya tsinci kan shi yana rokon allah ya rikida shi ya koma Ahmad dan baya so aji mutuwar saki daga bakin sa, kansa ya dauka ya buga da karfi jikin stirring din motar ko allah yasa Ahmad ya bayana...
Ahmad please! Ahmad please!!Ahmad please help me out!!! abun da ya dunga nanatawa wa kennan yana buda kanshi da stirring din motar
Diffffffff sai ya dauke......

*****************************************************
To be continued  insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now