Twenty seven

139 17 0
                                    

Episode twenty seven
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Sai da ya sha kukan sa ya gode allah ya tashi ya dako waya zai bugawa Attahir zai zo su tafi Asibiti dan wannan abun ya fara fin kafin sa...
Sai kuma ya duba yaga yanma tayi ko sun je asibiti babu wanda zasu tarar yanzu, hakan yasa yayi tsaki ya jefar da wayar ya mike tsaye ya hau safa da marwa shi kadai a gidan yana neman hanyar da zai bullo wa Ahmad. Duk yabi ya susuce, babu abun da ke tafiya daidai a rayuwar sa face ahmad ya bata masa, ko abu ya fada a wajen aiki za'ayi idan ahmad yazo sai yace ai ba haka za'ayi ba, yanda yake so haka za'ayi...

Ji yayi gidan ya masa kadan hakan yasa kawai ya zura takalmi ya fice.
Bakin rafin gero yayi, ya dade bai je wajen ba dan shi tun randa Nadiya ta wulakanta shi akan ruwa bai kuma yin wajen ba...

Wata yarinya ya hango sai shilo take yi jiki bishiyoyi guda biyu da ta daura igiyarta ta.
Tana shilo tana yan wake waken ta...
Ji yayi kafafun sa na daukan sa inda take a hankali, har ya karasa bata dago ba sai da ta ga inuwar sa ta dago da sauri...
Sai a lokacin ya kuma kare mata kallo,
Doguwa, fara yar shiririya masha allah,
Wani murmushi ta sakar masa cike da anuri da farin cikin ganin shi dan duk a zaton ta ta zata Ahmad ne...
Fararen hakawaranta da suka kuma haska ta, kyawun ta ya kara bayana, ya kara tafiya da tunanin sa, ta sha kwaliya kai bakace yar kauye bace face kayan da suke jikin ta da suka yi zubi da na yan kauye, sai da kuma yarinya ce dan da kyar idan takai 17 wannan yarinyar.

Ganin hankalin sa ya tafi chan yasa ta taso ta karaso inda take cikin farin ciki tace,
Tun dazu nake ta addu'a allah ya kawo ka, gashi allah ya karbi addu'a ta...
Ganin bai ce komai ba ta kafe ta da idanu yasa tayi masa fifita da hannun ta a ido da yasa yayi saurin kifta ido....
Ta kara yin murmushi tace tunanin me kake yi ne??
Sai a lokacin ya kamo nutsuwar sa yace bakomai a wayance tare da gyara tsayuwar sa.
Tsoron kar yayi mata magana mai tsayi ta gane ba Ahmad dinta bane, dan haka kurum ya tsinci kanshi da baya son ta gane ba shi bane.

Jin yayi shiru yasa tace, hau na shilla ka...
Nasan baka taba hawa irin wanna lilon ba....
Zaro ido yayi tare da fadin niiii😳
Tayi dariya tace eh mana....
Ni yanzu idan na hau wannan ai tsinkewa zai yi, saidai ke ki hau na shilla  ki...

Ta danyi shiru sai kuma yace hau mana,ta dan matsa kusa da shillon sai kuma tace bafa da karfi ba...
Yadan yi gajeran murmushi ya gyada mata kai..
Ta hau ya hau shilla ta...
Tsintar kansa da cemata wai me yake kawo ki nan ne ke kadai, ko tsoro bakyaji....

Tadan yi shiru kamar bazata amasa shi ba sai kuma tace abu biyu ne ke kawo ni nan...
Uhmm ina jinki meye abu biyun???

Na farko dai nan wajen shine waje daya da zan iya zuwa inji na tsira, babu mai takura mun babu wanda zai shiga sabga ta, nan ne kadai wajen da zan ware kaina daga cikin mutane dan ina so injini ni kadai.

Na biyi kuma kullun idan zan zo wajen nan sai nayi addu'a allah yasa na hadu da kai....

Haka kawai yaji zuciyar sa tayi sanyi akanta , duk wani zafi da zuciyar da shi kansa yake dauka idan yaganta yaji duk yayi sanyi, dan har ya saki jiki da ita kasancewar wannan shine karo na farko da ya tsaya ya saurare ta cikin nutsuwa.

Ta katse masa tuna ni da kai kuma fa???
Yayi saurin cewa ni....
Niii..... bakomai kawai ina zuwa nan ne...
Tayi saurin juyowa ta kalle shi tace masa ba wani nan.....
Ka manta abun da kace mun ranar nan???
Ya danyi turusss dan gudun kar ta kama shi sai kuma yace
Me nace??
Kace kana zuwa nan ne ka ganni idan bana nan kuma kaje gida, kai dai kawaibka fadi gaskia guri na kake zuwa ta fada tare da zumburo masa baki alamun shagwaba....

Mamaki ta bashi da tasa masa wani sasanyar murmushi a fuska ya bita da kallo...
Bai ce mata komai ba sai aikin kallon ta da yake yi...
Sai can kuma tace...
Ahmad meye dan kace wajena kake zuwa tunda nima nace saboda da kai nake zuwa.

Ganin ta dan bata rai cikin shagwaba tana kallon sa, yasa ya tsayar da lillon ya tsuguna kusa da ita, yana kallon ta cikin ido, kamar tayi kuka...
Gashin idon ta sun sha maskara dan har daya yana shirin sigar mata ido...
Yayi mata pointing idon ta, tayi sauri sa hannu ta murje idon kwali da maska duk suka bata idon ta koma wat dodo da it....
Yayi dariya ya sa hannu a aljihu ya zaro mata hankicin sa ya bata...
Ta karba ta goge ama koda ta gama duk ya sha kwali yayi baki...
Ya daga kansa sama ya ce dare fah yayi ya kamata ki tafi gida....
Ba musu ta mike....
Ta mika masa hannun ta...
Ya bita da kallo cikin mamaki tare da fadin me??
Hankicin naka zaka bani in wanko maka...
Ya danyi murmushi yace a'ah ni zan wanke kaya na, na hutashe ki,
Harta juya zata tafi sai kuma ta juyi ta kalle shi sai kuma tace
Ama kasan yau ka chanza.....
Gaban sa ya fadi tare da fadin ta gane ni a zuciyar sa?
Da kyar ya kirkiro murmushi yace...
Me kika gani....
Bakomai, yau bazaka raka ni ba??
""Auuu haka kuke yi ya fada a zuciyar sa""
Yayi saurin wayancewa tare da fadin ahh ai dana jira nake kiyi gaba sannan yanda zan biyi ki a baya...
Tayi murmushi tace dan ka tsoratani ko ai nasan halin ka,
Sukayi dariya baki daya suka jera tare ya raka ta har gida sannan ya wuce shima.

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now