Thirty

142 14 2
                                    

Episode thirty
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Wajen tadin su suka nufa a bakin rafi, ya hango lilon data kulla, yayi saurin cewa
Laahhhh Nadiya kinga lilo, zo muje ki shilla ni....
Tayi dariya tace kai Ahmad, kamar yau ka fara ganin shi, ko jiya ne ko shekaran jiya kai fah ka shilla ni, har nace ka hau kace bazaka hau ba karbya tsinke....
Yadan yi dummmm kadan " shaffiq ya kara zuwa wajen Nadiya a matsayin ni kenan"
"Lalle babu abun da zai hanashi cin uban shaffiq yau"
Ya taro yakin da ya fi karfinshi.....
Muje ka shilla ni ama a hankali kamar na ranar nan, ta fada cikin yanayin excitement.
Ya zuba mata kyawawan fararen idon sa, tayi masa fari tare da fadin muje.
Ba shiri ya bita ta zauna ya hau shilla ta a hankali, jin sunyi shiru yasa tace: tunanin me kake yi ne...
Yadan wayance da bakomai nayi shiru ne dan na shilla ki cikin nutsuwa..
Ya sa hannun sa cikin aljihu sa ya ciro wani dan kit ya zaro wata sarkar azurfa mai dauke da capital letter N a jiki.
Jin saukar hannun sa da abu a wuyan ta yasa tayi saurin daga kai sama ta kale shi, yayi mata murmushi yace ki rufe idon ki?
Ba musu ta rufe idon , sai da ya gama samata, har ya zagayo ya tsuguna a gabanta bata bude idon ba....
Yayi murmushi tare da fadin ashe kina jin magana....
Ta bude ido a hankali tana murmushi
Kalon kallo sukewa juna, tayi murmushi shima yayi, ta kifta ido shima yayi, chan kuma suka kwashe da dariya, tsabar nishadi.......
Sai kuma yayi shiru ya sami nutsuwa ya kira sunnan ta cikin sasanyar muryarsa mai cike da charisma,
Ita ma kyawawan idanun ta da kyakyawar fuskar ta zuba masa...

Nadiya ko ban fada ba kema kin san ina sanki ko? Ya karasa tare da yin smiling....
Nadiya inaso ki, ina son ganin farin ciki ki da nishadi ki a duniya, babu wani abu da nake so a duniya face in ganki kulum cikin walwala da jin dadi Nadiya.
Nadiya yanda nake ganin farin cikin ki yanzu, da wannan kyau kyawan murmushin naki, ina rokon allah ya dorar da shi ya cigaba da nunamun har karshen rayuwata.
Ji tayi jikinta yayi sanyi, kafafunta sun dau sanyi hannun ta sai uban gumi yake, zuciyar ta na harbawa daya bayan daya...
Ta kasa daga ido ta kalle shi, dama allah zai nuna mata wannan ranar, anya kuwa ba mafarki take yi ba..
Zuciyar ta ta dade da karbar Ahmad a matsayin masoyi ama gani take kamar hakan ba mai yuwa bane kawai zata wahalar da zuciyar tane domin kuwa ahmad yafi karfinta...

Ji tayi ya kamo hannun ta tayi saurin zare hannun ta daga nashi, ya hado da dayan ya riqe hannun duka biyu, cin murya mai sanyi yace nadiya ki kale ni mana...

Wani nauyin sa take ji da bazata iya hada ido da shi ba...
Ganin hakan yasa ya sakar mata hannu tare da fadin
Nadiya nasan kina sona, saboda haka ba sai kin ban ansa ba, saboda na sami ansa daga wajen ki tuntuni.
Zumbur tayi ta mike wai zata gudu, tsabar kunya ama sai ta harde, ta fada kanshi..
Ta karayin zumbur ta mike, kunya kamar ta tsaga kasa ta shige....
Ya bita da kallo kawai yana murmushi yanda duk tabi ta rikice.
Tana tafe yana binta a baya, sarkarta kawai take kallo tana smiling....
Lura da hakan yasa ya matso dadidai kunnen ta yace saura kuma ki cire.....
Kina cirewa muna batawa.....
Ya fada cikin wasa...
Har sukayi rabin tafiyar su bata kula shi ba, dan kuwa zuciyar ta sai sake sake take yi mata, toh me zata ce masa ita bama ta da abun fada.

Shan gabanta yayi yana yar dariya yace
Nadiya wai tunanin me kike yi...?
Auuu na gane ki, daga yanzu idan inason nayi maganin surutun ki , kawai ina son ki zan dunga cewa, shikenan sai bakin mai surutu ya mutu...
Ko kuma ba haka bane??
Nadiya bakya sona ???
Bai jira jin amsarta ba ya yi gaba, ya fara hawa kan wasu duwatsu, ita dai batace komai ba ta bishi da idanu, dan tasan wasan Ahmad shi kullun cikin wasa yake....
kan kice me har yayi nisa akan dutsen da ko hango shi bata yi sai ta daga kai....
Gani tayi yana dago mata hannu alamun zai durgo....
Ta bishi da kallo tana murmushi dan duk a zaton ta, ta zata wasa ne irin na sarkin wasan...
Tsale yake shirin yi dan kuwa yanayin tsalen nan sunnan sa mutuwa...
Dan yana yin tsale zai ganfara ya fada cikin duwatsu masu tsini da zasu iya fasa masa kai ko ciki...

Zuciyar sa ce ta raya masa toh kodai shaffiq Nadiya take so ba shi ba, idan har haka ne toh meye amfani sa...
Wannan tunanin ne ya debeshi, yaji yana shirin faduwa wa, jiri ne ya debe shi da ba shiri ya zame daga kan dutsen
Ihu ta saki, a gigice ta zura a guje tayi kan dutsen, bai karasa kaiwa kasa ba, ta danko wuyan rigarsa tana ambatar sunan sa...
Ahmad!! Ahmad!!.....
Garin janyo rigarsa har sai da ta yage, hakan yasa ya kara yi mata nauyi, ko jan sa bata iya yi, wani kuka ta saki mai cike da kunci da daci, tana kiran sunnan sa...
Da kyar ta kamo hannun sa ta janyo shi ya dawo kan dutsen ta kwantar da shi...
Sai haki take tana nishi ga uban kukan da take yi...
Shi kuwa ina tuni ya sami sauyin yanayi, kwakwalwar ta sauya ta koma shaffiq....
Kamar mara rai haka yake kwance a wajen, sai da ta gama sauke lumfashi sannan ta koma kanshi tana
Ahmad Ahmad shiru ba amsa dan ko motsa danyatsa bayayi...
Hankalinta ya kuma dugunzuma ya tashi,ta dago hannun shi ta saki ta ga ya tafi luuuu ba kwari....
Wasu hawaye taji sun zubo mata, ta fashe da kuka, kukan ta ne yasa hankalin sa ya dawo jikin sa...
Ta hau dukan kirjin sa tana wannan wane irin mugun wasa ne Ahmad, ni bana son irin wannan wasan , kai da bakin ka kace kaima kasan ina sonka...
Dukansa takeyi tana kuka, shidai yayi lamo yana saurarar ta kawai dan bai san hawa ba shi bare sauka...
Wanna ai ganganci ne akan me zakayi kokarin kashe kanka bayan ni kai ka hana ni kashe kaina...
Idan ban so ka ba wa zan so a duiyar nan ahmad, wa nake da shi bayan kai...
Kaima kasan na dade da kamuwa da sonka, dan allah ka tashi, ahmad ahmad!!!
Takai kunnen ta kan kirjin shi dan ta tabatar zuciyar sa na bugawa ko ta tsaya....
Jin ta akan sa yasa zuciyar sa ta hau dokawa goma goma...
Ita kuma jin bugun zuciyar tasa yasa ta dago a fusace tana wai meye hakan dan allah ka tashi mana....
Ta kuma kai hannu fuskar sa tana kiran sunnan sa cikin murya mai sanyi har tana rawa tace
Ahmad dan allah ka tashi wallahi ina sonka duk duniya babu wanda zai nuna mun sanka, da sanka nake kwana nake tashi, babu wanda sanso yanda nake sonka ahmad....

Kasa jure taba shin da take yi yayi, da hannun ta ta sauka a kanshi ji yake kamar an watsa masa ruwan kankara, tsikar jikan sa ke tashi har cikin kwakwalwar sa....
Gudun kar ta kara taba shi yasa ya bude idon sa a dasauri!!

*****************************************************
To be continued  insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now