Twenty six

149 12 3
                                    

Episode twenty six
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Har ya tafi yaji bazai iya tafiya ba sai ya sami wani makami da zai rike against ahmad dan yaga karshen shi hakan yasa ya daure ya dawo
Inuwa ta gani a kanta da tayi saurin mikewa har tana shirin faduwa.
Fuskar sa a daure tamau babu alamar murmushi a tare da shi ko farin ciki, ko alamun raini, idon nan yayi ja kamar me kansa sai hayaki yake futarwa...
Zai mata magana yaji kansa yayi wannan mugun sarawar da yake yi, kan kuce mai jiri ya debe shi, duhu ya ziyarce shi, ya fadi kasa ba shiri yana dafe kai...

Cikin rudun ganin yanayin sa yasa itama ta kidime ta hau kiran sunnan sa
Shaffiq! Shaffiq! Shaffiq!!!
Lafiya me ke damun ka, meya faru, baka da lafiya ne...
Ganin baya cikin hayacin sa hakan yasa tayi saurin mikewa zata je ta kira inna tani dan a temaka masa.
Motsin da taji yayi yasa tayi saurin juyawa taga ko lafiya
Mikewa taga yayi yana karkade jikin sa kamar ba shi ba, ya dago cikin murmushi da fara'a ya kalle ta ya kali inda yake yaga kofar gidan su Nadiya yake...
Nadiya ya fada cikin fara'a tare da mataowa inda take
Shaffiq lafiya, meke damun ka..??
Shaffiq kuma Nadiya kin fara manta ni ne...
Ahmad ne....
Cikin mamaki tace ahmad kuma, mai ya kawo ahmad nan....
Tsoro abun ya bata da tayi saurin cewa
Ahmad ne a cikin zuciyar ta
Ama tabass tasan shaffik ne ke tsaye a wajen nan yanzu.
Ahmad dama kaine ba shaffik ba?
Shima abun mamaki ya bashi, ya hango kedar kayan da ya siya mata, ya nuna su da hannu tare da fadin wadan nan kayan fah?

Tayi shiru tana binshi da kallo, dan bata ma san me zata ce masa ba
Shaffiq shaffiq me ya ce miki, me ya kawo shi nan, meya ce miki nadiya
Ya fada cikin rudu.......
Kallan sa kawai takeyi tana jinjina rainin hankali da rainin wayo irin na shaffiq...

Ganin da gaske yake yana tambayar ta

Kaman yaya me yace mun, yanzu fa muke tsaye da kai anan wajen, zaka ce mun wani ya tafi wani ya dawo ne...
Yanzu kace mun ahmad yace ka kawo mun waddan nan kayan...
Zaka ce mun ka manta ne? Ko baka san da zancen ba...
Muna tsaye anan wani ya tafi ne wani yazo ta fada cikin tsananin mamaki....???

Bai jira jin mai zata kuma cewa ba kawai ya bar wajen cikin hanzari....
Ta bi shi da ido tare da girgiza kai ta dau kayan ta shige ciki kawai
**************************************************
Huci kawai yakeyi ransa ya dugunzuma ya baci kwarai da gske, bai taba jin bakin ciki a zuciyar sa ba kamar yau.
Akan me shaffiq zai shiga sabgar sa me zai kaishi wajen Nadiya har da zai dauki kayan da ya siya mata ya kaimata, idan shi yayi wa haka zaiji dadi ne...
Waya ya dako, sai kuma ya chaza shawara ya dako kasa ya dauko computer din shaffiq ya kunna ya hau video tapping kansa....

"" nasan bamu taba ganin juna ba ama ina so in ginda ya maka sharadi shaffiq, shaffiq kasa ka sake shiga tsakanina da Nadiya, bale har kaje mata a matsayin kai ne ni.....
Ina ruwan ka da kaya na da zaka dauka ka kai mata, na taba shiga harkar ka ne ko na taba taba maka kaya idan kace kar na taba maka??
Na dai gaya maka wallahi ka kara zuwa ka sa wa yarinyar nan shaku a cikin zuciyar ta, mai raba ni da kai sai allah!!!
Ya ja tsaki ya yi saving video din ba tare da ya kashe ba ya tashi ya koma sama.

*****************************************************
Nadiya kuwa koda ta shiga ciki rumfar da take kwana ta shiga ta hau bude ledar kayan da aka kawo mata, kayan kwaliya ne na gani na fada, wani murmushi ta saki wanda ya bayana farincikin ta da murnarta, dan kuwa bata taba tunanin zata malaki irin wadanan kayan kwaliyar ba a rayuwar ta, yanzu duka wannan nata ne....
Rainin hankalin da shaffik yayi mata ya dawo mata, ta girgiza kai kawai ra ki bari abun ya dame ta, kawai ta washe kayan ta boye ta tashi ta shiga sabgar gaban ta.

Yau da la'asar nadiya tayo wankanta ta tsab ta dako kayan ta da suka fi ko wane kyau ta saka, ta janyo kwandon da ta zuba kayan kwaliyar ta, ta dako su, duk wanda ta dako sai ta kalli hoton jiki ta yi itama.
Haka tayi har ta kammala kwaliyarta tsaf, ta fito tayi dass da ita kamar na ita ba, kwaliyar ta zauna a fuskar ta da yake kayan kwaliyar masu kyau ne daga kamfani suke.
Tana gamawa ta fice ta tafi gidan su binto dan ta nuna mata kwaliyar ta ta.

A daya ban garen kuwa tun da ahmad ya gama yiwa shaffiq bidiyo ya kwanta bai farka ba sai washe gari da la'asar koda ya farka a shaffik ya farka....
Yayi mika ya yi adduoin sa sannan ya tashi ya shiga toilet, ko da ya kintsa ya sako kasa yana sa wani abu a cikin sa yaga computer dinsa a bude, ya janyo ta zai kashe.
Yana budewa yaga bidiyo din ahmad,
Innalillahi waina ilaihi rajiun yayi ta maimaitawa, ya kasa nutsuwa, zasu hawaye kawai yaji yana zubo masa daga ido wannan wace irin cuta ce ke damun sa haka, tun suna wa juna sako ta takarda yanzu abun ya zama har bidiyo yake masa, gashi kuma shine yake magana ba wani ba, wannan wane irin mumunan alamari ne, wa zai iya zuwa ya fadawa abun da ke damun shi, idan ma aljani ne wane irin aljani ne da baya jin addu'a....
Yasha zama ya bawa kansa hakuri ko aljanin zai hakura ya bar jikin sa ama har yanzu shi...
Shin wai WAYE SHI NE???

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now