Three

310 25 0
                                    

Episode three
WAYE SHI(shaffik ko Ahmad)
Na: Bintnagz (Hasna mansur nagoda)
Wattpad @bintnagz

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"

**********

Ibrahim mai ya same ka, wadanne irin maganganu ne waddan nan da basu da asali, Ibrahim kar fa ka manta mu masoyan juna ne...
Ta taso zata rike shi ya kara ball da ita har ta kifa,?shi kuma ya sa kai ya fice...
Tun da yasa kafa ya fita a daren jiya bai kara waiwayar ta ba sai wani daren, yana shigowa ko salama babu ya nemi guri ya zauna yana huci, kallo kawai tabishi da shi zatayi magana tace ina yake kwana ne da baya kwana a gida tunda sukayi aure ta ji ya jefe ta da waddan nan kalamen,
Ke dan ubanki, ubanki bai baki tarbiyar yiwa mijin ki sannu da zuwa ba, ina abincin da aka kawo daga gidan ubanki ko bazaki girka ba saboda na uban ki ne...
Jiki na rawa ta kwaso masa kayan abinci ta dure masa a gabansa..
Saida yaci ya koshi sannan yace ina mukulin motar da ubanki ya siya miki...
Ta kalle shi cikin mamaki tace abba bai bani mota na ama dai nasan zai bani, kaima ai zai baka...
Mtsssswww yaja tsaki ya fice...
Sai da aka yi sati guda bata kara jin duriyar sa ba, gashi yau ta tashi da wani matsanan cin ciwon kai da zazzabi, a fallo ya tarar da ita tana kwance tana tsumayar zuwan sa da yake kullun sai tayi zaman jiran sa ta kuma ajiye masa abinci, idan bai zoba sai ta dauka ta bawa almajirai.
Yana shigowa kamar kullun ba salama ya hau bude buden kwanika da yake yunwa ce ta koro shi, ke ina abincina ya fada cikin tsawa, ta nuna masa kan karamin table din da ta ajiye masa, ya bude yaji sanyi sai kuwa cewa yayi..
Ke dan ubanki ni zaki bawa abinci mai sanyi, an gaya miki ni dan aikin gidan kune ko kuwa ni akuya ne...
Ta dago da kyar tace wallahi Ibrahim baiyi sanyi ba ban dade da sauke shi ba idan kanaso ka sake dumamawa mana...
Wallahi zazzabi nake yi da ciwon kai, kayi hakuri dan allah...
Kan ta rufe baki ya bita da zagi
Zazzabi da ciwon kan sun ci uwar baban su, mai yayi mun zafi da ciwon kanki, malama kitashi kiyi abin da ya kawo ki..
An gaya miki har yanzu a gidan ku kike...
Wani malolon takaici yazo mata nan ta mike a fusace yace, kai Ibrahim ya kuma ishe ka ni na dora wa kaina ciwon ne, wai anya kuwa kaine Ibrahim din da nasani , me ke damun ka kasha giyar wake ne da zaka dunga ci mun mutunci haka kasan abubun da na sadaukar a rayuwata saboda na aure ka, sakayar da zaka yi mun kennan Ibrahim, kar ka manta fa ina dauke da dan ka fa a tare da ni...
Baka san dara jar aure bane, kar kasa nayi da nasanin amincewa da soyayyar ka a duniya....
Tauuuuuuu kake ji a fuskar habiba, dan ubanki kar ki sake nuna ni da dan yatsa, dan ni ba sa'an ubanki bane da bai san darajar mutane ba...
Ubanaaaa.....
Ya kuma katse ta da wani marin....
Ibrahim wai ka dena sona ne
Auren soyayya fa mukayi
Bai kamata ace hakan na faruwa tsakanin mu ba...
Auren soyayya... hmmmm
Auren sadaka, ko auren nemankai
Tunda baki da amfani dole ya nemi kai da ke...
Wallahi talahi sai na wulakanta mahaifin ki yarda ya wulakantani ya numa cewa talaka banza ne.
****
Haka rayuwa ta kasance tsakanin Ibrahim da habiba, wulakanci da cin mutunci da cin zarafi kullun kara karuwa yake yi dan har ta kai ta kawo da yanzu sata a daki yake yi ya zane ta san ransa da abu ya hada su ko batayi masa daidai ba.
Sai yafi wata baya gidan bata sashi a ido ba, motocci biyun da abbanta ya kawo musu duk yasa su a kasuwa ya siyar ya kuma cinye kudin ba tare da ya bata ko kwabo ba, in takaice muku labari harta gidan abbanta ya bata wanda suke ciki sai da ya siyar, yaje ya sama mata gidan haya mai daki daya ya sata a ciki.
Abun duniya duk ya ishe ta duk tabi ta rame ta kanjame ga ciki ya tsufa, gashi abbanta yace kar ta sake zuwa gida yi masa complain akan Ibrahim ita taji tagani ita kuma tace tana so, sabi da haka kar ta sake zuwar masa.
Haka take ta hakuri ga mugun kulle da yake mata ko kofar gida bata fita.

Da yake abba khalid yayi aure shima yau ta sami labarin cewa matarsa ta haihu hakan yasa ta dauki jiki ta tafi yi mata barkar haihuwa, dayake itama tana kula da ita sosai tana kuma share mata hawayenta, idan takai wa abba khalid kukanta, yakuma bata hakuri yayi mata nasiha akan ta daure komai mai wucewa ne a rayuwa.
Ai kuwa tana fita ya dawo, haka ya zauna zaman jiranta dan ya sauke mata ruwan azaba,
Tana shigowa ya yi mata maraba da ruwan zagi
Ke dan ubanki ni na baki izinin fita ne ko kuma zaman ubanki kike yi da zaki dunga daukar kafa kai tsaye kina fita...
Zatayi magana ya zare belt din jikin sa ya nada mata na jaki, jikinta duk ya farfashe....
Haka ta shiga daki tayi kukaka tayi kuka, har ta godewa allah...
Ita addu'ar ta daya allah yasa ta haife cikin nan lafiya kar ya kashe mata da dan idan ya tashi dukan ta ko ina yake mata...
A dare ranar nakuda ta ruske ta, tayi tayi ta haihu ama ciwo ya ci karfin ta da ko nishi da kyar take yi, gashi babu wani makoci ta data iya kira tace ya temaka mata ga dare yayi ita kadai a gida...
Da asubar fari ta haifo danta santalele, lafiyaye
Yaro yazo diniya ko abun rufa bashi da shi, balle kayan sawa.
Haka ta dauki tsofafin zanin ta ta nade dan a ciki ta gyara wajen ta kintsa kanta, sai dai me tun da ta haifo yaron nan jini ya tsunke mata, jin yake ta zuba kamar an yanka rago...
Da kyar ta samu almajiri ta shigo da safe ta tura kanti ayi mata chaji a kuma siyo mata katin dari tasa sannan ta kira abba khalid ta sanar da shi halin da take ciki...
Kafin yazo har abun yaci tura dan a sume suka dauke ta sukayi asibiti da ita.

*****************************************************
To be continued on Laraba insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now