Twenty-two

133 12 0
                                    

Episode twenty two
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Tana shiga inna tani ta sauke ta da
Ke dan uban ki yau sai kin gaya mun ina kika samo waddan nan mutane, bin maza kika fara yi, naji ance yan birninsun fara shigowa gero ashe su kike zuwa kina like wa ko??????
Nan tayi tsuru tsuru idan ta ya ciciko da hawaye, jikin ta ya hau bari,
Inna wallahi ba bin maza nake yi ba akan me zan bisu, wallahi mutunci ne kawai...
Mutunci a gidan uwarki, aka hakata mutunci tsananin namiji da mace dan ubanki...
Mado ne ya farka, yana kakarin a bashi ruwa, hakan yasa sukayi kanshi da sauri suka bar zancen.
*****************************************************
Bayan sati daya aka sallami mado daga asibiti, badan ya sami sauki ba da yake cutar mado bata tashi bace dan likitoci sun yi iya bakin kokarin su sun kasa gano mai ke damun sa, sai dai sun bashi magunguna da zasu in ganta lafiyar sa har tsawon lokacin da rai zai yi halin sa, idan kuma abun yaci tura toh su dawo asibiti.
A haka suka hakura suka fawalawa allah komai inna tani duk tayi sanyi ba abun da yake mata dadi duk duniya, dan bata fadawa mutane abun da likita yace sai dai azo dubiya kawai a tafi. Ga isuhu har yau bai dawo ba sai yau suka sami sakon sa na zai dawo bana da rani.
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ
Ahmad bai dade da komawa gero ba ya sauya ya koma shaffik, koda ya dawo dai dai , yaga ta'asar da ahmad yayi masa ji yayi kamar ya shake kansa ya mutu ya huta gaba daya,
Ya kwasar masa kudi makudai daga banki, ya siya kayan sakawa yan kanti kala kala, ga turaruka, da agoguna, ga dan kareriyar waya ya siya latest iphone 11 ya siya, duka kayan sa da zai ban-ban ta da shaffik sai da ya siya hata underwear sai da ya siya nasa. Dan bazai iya ci gaba da rayuwa da kayan shaffiq ba gani yake kamar ai shaffiq out dated mutun ne.

Abun yayi mutukar bashi mamaki fiye da ko wane lokaci, wasu zafafan hawaye suka zubo masa cike da bakin ciki, kamar ya hadiye zuciya ya mutu, wannan wane irin alamari ne da yake neman fin karfin sa, tabas bashi da maraba da mahaukaci, idan kuma ba hauka yake ba toh wane irin aljani haka yake faman dawai niya da shi??

Waya ya dauka zai kira mummy, yaga toh meye amfanin gaya mata ma dan tada mata hankali kawai zaiyi, gashi bashi da tabas din abun da ke faruwa da shi, idan ma aljani ne meyasa zai masa haka, tun yana karami basu kama shi ba sai yanzu da ya neman tsari daga gare su dare da rana kuklun cikin adduoin tsari yake.
Ya share hawayen sa ya tattara kayan ya ajiye a gefe .
Ya ma rasa me zai yi dan duniyar tayi masa zafi gaba daya, ji yake kamar ya bar layin mutane, dan shi yanzu ba mutun bane.
Ya shiga toilet yayo alwala yazo ya dunga jero nafilfili yana rokan allah yay yaye masa abun da ke damun sa.
Ranar karatun allurani ya kwana yana yi, yada koma aljanin ne bazai kucen shi ba.

Gari na waye wa ya dau motar sa yayi birni, kai tsaye gidan su Attahir yayi, bai ko je wajen abba khalid da umman su ba yayi bangaren Attahir.

Attahir yana kan tebir din karatun sa yana dannan computer
Ya shigo ko sallama bai yi ba ya haye kan gadon Attahir.
Attahir bai ce masa komai ba, ya ci gaba da abun da yake yi,
Sunfi minti 30 ahaka dan ya zata shaffiq ma yayi bacci.
Ya rufe laptop din ya juyo
Zaiyi magana ya ruga shi da
Attahir kwana biyu baka ga na chanza ba??
Eh ka chanza mana...
Ya miqe zaune yace ta ina ka ga na chanza?

Ya taso ya karaso kan gadon shima ya zauna yace
Na daya baka zuwa aiki, sai kaga dama
Na biyu idan na kira ka sai ka ga damar dauka
Na uku.....
Kaga tsaya wai ina ta so in tambaye ka, ama dai kasha dan wani abu lokacin da muka hadu da lawisa,
Shaffiq yayi shiru yace???
Wai tsaya dama mun hadu da lawisa?
Yaushe??
Attahir ya gyara zama yace au wai da gaske ka manta da munje wajen lawisa.
Eh wallahi bansan mun je ba, hasali ma ina taso inyi maka magana inji yaushe zamuje.

Toh munje uban mantuwa,har ka zake ka cika ta da surutu kamar kaine saurayin..

Yayi shiru yace Attahir kasan inda ake RUQIYA
Attahir ya baza masa ido ruqiya kuma??

Attahir tabass ina da aljanin a tare da ni, idan kuma ba aljani bane to Attahir na fara hauka.

Umm lalle gskia da alama ka fara hauka, ya mike ya bude drawer din coffee dinsa ya dako daya ya zuba a cup da ruwan zafi ya juya ya hau sha da yake shaffiq baya shan coffee.

Kai Attahir wallahi ba da wasa nake maka ba, ya mike ya koma kan kujerar da Attahir ya zauna.

Ya canza murya kasa kasa yace sunnan aljanin Ahmad, yau kimanin watan sa 4 ko uku a tare da ni...

Attahir ya zaro ido yana kallon sa, kai kasan me kake yi...
Da bakin ka kake cewa kana da aljani....

Kaga just keep quiet and listen to me Attahir...
Da komai nawa yake amfani, jiki na , kaya na , da kamata da komai na yake amfani, kai yanzu har kudi na yake tabawa, yaje ya siya wa kansa kaya kala kala da waya, kai in fact ya siya wa kansa duk abun da yake bukata.

Idan ina kauye sai dai in tashi inga anyi girki kala kala kamar restaurant, an kuma bata mun waje an birkita mun kaya an mayar mun da gida upsides down.

Harta kai ta kawo ta kawo yanzu mutane da sunnan sa suke kira na, a kamfani da tsarin sa muke amfani muke tafiya, dan zuwa yake yana abu amatsayin nine shi, kuma ni ban san ana yi ba.

Yayi abokai yanzu duk inda na zaga a gero da ahmad suke kirana.
Idan ya bayana ni kuma sai na bace sai ya tafi ni kuma zan dawo, a wannan lokacin yake samun yin duk abun da zaiyi ni kuma bansan anyi ba, sai na farfado zanga duk abun da yayi...

Attahir ya ajiye cup din hannun sa yayi ajiyar zuciya, ya jinjina kai yace...
Fairy tail dinka yayi dadi sosai, tashi ka tafi ni yanzu wajen lawisa zani....
Ya fada tare da mikewa.....
*****************************************************
To be continued  insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now