Nine

265 19 0
                                    

Episode nine
WAYE SHI(shaffik ko Ahmad)
Na: Bintnagz (Hasna mansur nagoda)
Wattpad @bintnagz

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Cigaban littafi

Sai karfe biyar da rabi ya shigi gida, yana shigowa ya shiga kiran mummy, chan ya yango ta reading room dinta tana karanta news paper tana korawa ta tea mai zafi..
My son ta fada cikin kasaita da mulki..
Sunu da dakwowa, allah ubangiji ka yi ma wannan da albarka, ta fada tare da dafe kansa...
Yayi dariya yace mummy har yanzu baki dena wanna adu'ar ba...
Kaji da, ni habiba baka so allah ya sa maka albarka...
A'ah ni ba haka nake nufi ba, gani nayi tun ina karami kike ti.
Kuma bazan dena ba ba...
Tashi kaje kayi wanka ka ci abinci, ina za'a kawo maka abinci sama ko kasa, yayi murmushi yace sama, tare da fita ya hau sama.
Yana shiga ya fada toilet yayi wanka , ya fito...
Allah yayi shaffik dan gaye acikin masu gayu duniya, babu abin da yake so sai gayu, shidai yaga yayi wanka ya kure adaka, dressing mirror dinshi kamar na mace, mayuka da turaruka kalakala ne a jere a kan dressing mirror dinshi harda lipbam...
Kaya kuwa kamar mace suma dan walldrops da drawers dinsa su suka cika dakin, balantana azo girin takalma, nan zaku saki baki, ga agogo kuma ga zobe duk shi kadai.
Shaffik dogon namijine faffada wanda ya murde jikin sa ta hanyar gyming dan babu ranar da zata fito ta kare shaffik baije gym ba, hakan yake kuma kara masa kwarjini a idon mutane.
Ba fari bane shi, saidai akwai dogon hanci da kyawawan fararen idon sa wanda ake kira da oily eyes cikin kyakyawar fuska masha allah wanda ake kira da black beauty 😁
Babban abin da shaffik ya tsana a duniya shine kazanta, baya kaunar kazanta ko mikalazaratin, dakinshi a rana sau uku ake share shi, toilet dinshi kuwa ko shiga yayi ya fito to sai ya wanke shi, kaya kuwa basa awa biyar a jikin sa da yasa yaje ya dawo zai shiga wanka ya cire su, ga uban tsari idan anan ya ajiye kaza toh haka yake son ganin kayan shi ko yaya kika chanza zai gane, shi yasa baya yarda kowa ya shigar masa daki, koda mummyn sa ce kuwa, mutun daya ke shiga dakin sa shine Attahir, shima dan sun zama daya ne, danuwansa ne ga koma abokata mai karfi da take gudana a tsakanin su.
Yana da wani irin hali na rashi shiga sabgar mutane, idan har baka sa da shi ba toh fah babu abun da zaisa ya shiga sabgarka, baya kaunar mata, dan kuwa gani yake mata nauyi ne a kansa, dan yana da zuciya mai taushi baya kaunar yaga ana cin zarafin mata ko ana zalintar su hakan yasa yake gudun hakan shi yasa shi da mata saidai nesa nesa.
Ba shida yawan magana idan har kaji shaffik yana hira toh mummy ce ko kuma Attahir amininsa dan uwansa kuma.
Su kadai ya aminta da ya saki jiki da su.

Bai gama shiri ba sai ana kiran magariba, hakan yasa kaya kawai ya fita masalaci yayi sallah yayo gida directly.
Yana dawowa ya zauna kan dinning table dinshi, mummyn shi ta shigo da plates din fruit a hannun ta, ta ja kujera ta zauna itama tana kallon shi yana cin abinci. Can yace mata ama mummy meyasa baki taba yi mun zancen filin ki ba. Tayi smiling tace, yanzu ai ka sani, and nasan zaka yi aiki mai kyau shi yasa na wakiltaka kai da dan uwan ka.
Yayi murmushi kawai yace toh, gobe idan allah ya kaimu zan biya ya wajen in ga yanda wurin yake.
Toh dan albarka allah yayi maka albarka.

Washe gari da safe ya fita aiki, karfe biyu suka fita shi da Attahir da kuma salih, shi ya shiga motar sa su kuma suka shiga motar Attahir.
Cikin awa daya da rabi suka isa kwayen gero.
Sun yi mamakin filin dan kuwa basu yi tunanin wajen yakai girman haka ba...
Shaffik ya kalli Attahir da salih yake cemusu ya suke ganin gurin.
Salih yace gskia gurin yayi dan wajen zaiyi suiting gini da za'a tasa.
Da yake ba bangaren shaffik bane shi chemical engineering yayi, su kuma suka yi architecture.
Nan dai suka tatauna, sosai dan gane da wajen da ginin, suka dako takardu suka danyi zannen su sannan, wayar Attahir tayi ringing yasa hannu a aljihu ya dako ya dauka, yana gamawa yace Abba ne i have to go, muje kawai gobe ma dawo...

Chan shaffik yayi wani tunani sai kuma yace kaga Attahir ku tafi kawai ni bara na duba water supply dinsu da kuma wutar garin.
Alright toh ba matsala.
Haka suka tafi shi kuma ya shiga cikin kauyen har ya karasa bakin rafin garin, gurin na sa bala'i tsafta dan gurin yayi masa shi mai cutar tsafta ma. Gurin duk bishiyu da korama, sai tsuntsays da ke ta kuka a wajen ga yanma tayi gurin gwanin ban sha'awa.

Chan ya jiyo wani ihu da ya razana shi, da yayi saurin juyawa, wata yarinya ce da batafi shekara 17 ta taho a guje kanta ba dankwali kafarta ko takalmi babu, kana kallonta neman macechi takeyi duk ta futa daya hayacinta, wani saurayi ne da baifi shekara 25 haka ba ya biyota daga shi sai singileti da gajeran wando, ya sabba wandon sa a kafada shima ko takalmi babu haka yake bita....
Kan kice mai kan shaffik ya fara juyawa, fuskar mummyn sa ya gano a fusakar yarinya, dukan da ubansa ya dunga yi wa mummyn sa yanda mummyn sa ke shiga rudani da neman mai taimakon ta ya dawo masa, dukan da baban sa yayi masa da har ya tura shi bango ya fasa masa kai, wahalar da mahaifiyar sa ta sa duk suka dawo masa cikin kai....
Kansa kara sarawa yake yi duk kwakwalwa sa ta chushe, ya dagula lissafin kansa, chan yaga duhu ya zo masa ido baya ganin komai sai duhu da taurari....
Chan yaji kamar yayi kamar sume yake, cikin sakan 30 ya farfado, yaga yarinyar nan tayi cikin ruwan nan, tauuuuu
Shi kuma mai binta na ganin hakan ya arta a guje ya koma.
Ba shiri shaffik yayi cikin ruwan nan shima.

*****************************************************
To be continued  insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now