Eleven

209 21 1
                                    

Episode eleven
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ
Cikin sakani kadan taga shaffik ya juye gaba daya ya zama tamkar ba shi ba, hakan ya daure mata kai zata yi magana yayi saurin cewa
Tafiya zanyi koh?
Alright fine bye...
Kan tace wani abu ya hau mota mai gadi ya bude masa gate ya fice ta bishi da kallo da baki bude...
Ga mamakin sa yaji yana tuka mota cikin kwanciyar hankali kamar wanda ya shekara yana tuki...
Sai dai me?
Bai san inda zai je ba...
Ya sami guri yayi parking...
Ya duba bayan motar yaga takardu da yawa yaga duk sketching din gini ne, ya danyi tunani yace duk inda akayi gini yake yi, chan yaji wayar aljihun sa tayi alarm, yayi saurin sa hannu a aljihi ya zaro wayar, yaga alarm ne da shaffik yasa na reminder na zaije kauyen gero karfe 10:30 na safiya.
Ba shiri ya gano kan lamarin ya seta gps din motar zuwa kauyen gero, duk da bai san meye geron ba ya ware.
Daidai site din ginin ya tsaya da yake nan ne destination din gps din ya tsaya
Saida ya gama karewa wajen kallo ta cikin mota sannan ya fito...
Mutanen gurin da masu aikin wajen suka dunga zuwa gaishe shi, suna masa barka da zuwa, waje yayi kyau sosai dan kuwa an sakar wa wajen kudi sosai dan gini yayi nisa cikin sati daya.
Shaffik ya saki baki ya dunga yi musu tambayoyi har sai da ya gane cewa ashe gini akeyi kuma shi yake supervising wajen. Shaffik mutun ne wanda magana ma wahala take masa inba dole ta zama ba, ama yau shine ya saki baki ya dunga magana harda wasa da dariya da maikatan wajen, suma abun ya basu mamaki kwarai da gaske, gashi yana abun kamar bai san da zaman wajen ba aduniya.
Bayan ya cika su da surutu ne ya danyi strolling dan yaga wajen, cikin tafiya yaga kamar yasan hanyar nan ya cigaba da tafiya har ya isa bakin rafin rugar da ke gero.
Ji yayi kamar ya zo gida dan kuwa, babu wani waje da ya sani mai kyau kamar wajen nan...
Yayi murmushi, ya tsaya yana kallon kyaun wajen yana jin dadin iskar da ke kadawa a wajen, kwakwalwar sa fayau babu komai a cikin ta saboda haka babu abin da zaiyi tunani, sai wannan yarinyar da ya fara haduwa da ita, ita ce mace da farko da ya fara ganin a duniya..
Ya lumshe ido yayi murmushi yace NADIYA dan shine suna na farko da ya fara ji shima.
Bude idon da zaiyi ya gani ta tana tafe tana rangwada, kamar iskar da ke kadawa awajen ta kwashe ta saboda tsabar siranta ta nadiya, da tulu a hannu tana tafe tana wake wake a zuciyar ta hakan yasa ko kallon wajen da yake batayi ba har ta karasa bakin rafin.
Tsayawa tayi ta tuna da fuskar wannan bawan allah da ya tsamo ta daga ruwan na. Dan har yanzu bata manta da shi ba...
Ta bayan ta taji ance yauma fada wa zaki yi...???
Ta juyo da sauri, ta kalle shi, ta zuba wani uban murmushi tace laaaaa dan ruwa...
Cikin mamaki ya nuna kansa tare da nine dan ruwa...
Tayi murmushi tace eh mana...
Meyasa na zama dan ruwa...
Saboda kai ba'a ganin ka sai a bakin ruwa, na yi ta neman ka ban gan ba sai yau, kuma a bakin ruwa, kuma ma dai babu mutane irin ka a cikin rugar nan tamu.
Ta danyi shiru, sai kuma tace, kadai kai dan birni ne, dan naga kayan ka na yan birni ne.
Kai yarinyar nan akwai surutu, ya fada a zuciyar sa tare da yin dariya....
Toh meyasa kike nemana...??
Kawai inaso in gode maka ne, ka temake ni..
Na zata ai kina nema na ne dan ki zane ni meyasa na cero ki dan kin shiryawa mutuwa a lokacin.
Tayi dan shiru ta tsuguna, bakin ruwan ta saka tulun ta cikin ruwan, shima ya tsuguna yana jiran amsar da zata bayar...
Ganin batayi magana ba yasa yace, Nadiya?
Ta juyo ta kalle shi sai kuma tace eh da hakan ma ama dai nagode.
Yayi murmushi kawai baice komai ba sai kuma cewa tayi
Ya akai kasan sunana?
Chanka nayi😁
Tayi dariya da dimple dinta ya fito, fararen hakwaranta suka bayana sai tace toh kai ya sunnan ka?
Ya dan yi jimmm dan bai san ma sunnan sa ba, gashi bai san wane sunnan zai kamo ba,yayi yayi ya tuna sunnan da yaji mummy ta fada masa ya kasa sai chan yace
Kema ki chanka....
Ummmm toh nadai san yan birini sunnan ku bazai wuce Habubakar ba, isma'ila ba ko faisal, ko amadu ba...
Toh ai kin kawo su da yawa sai ki zaba cikin wanda kika fada...
Tayi murmushi tace toh nadau Ahmad ne...
Na chanka???
Ya tafa hannun sa alamar tayi daidai tare da fadin ashe kema kin iya chanke...
Tayi dariya tace ashe malan amadu ne...
Ta mike zata dora tulun ta a kai...
Yayi saurin kwacewa, tare da fadin bara na taya ki...
A'ah bani abu na yan birni basu iya daukan tulu ba kada ka fasa inna Tani ta zane ni...
Maman ku...?
Ta danyi shiru sai kuma tace ehh...
Haka ta bar masa har suka kai inda ya kamata ta karba..
Ta karba tace ya kamata mu rabu anan kada Mado ya ganni ya fadawa inna Tani, tayi saurin karba ta shiga cikin lungun a guje ba tare da yace mata komai ba.
Yayi murmushi ya juya shima...
Mai makon ya koma site sai ya kuma shudawa cikin kauyen.
Wasu samari ne sunyi dan-dazo kana ganin su bata gari ne dan duk rige suke da gororin su, sai busa sugari sukeyi...
Ogan su yayo gaba sun biyo shi a baya sai uban hayaniya suke yi wai su yan daba.
Ogan nasu ya bangaji shaffik a kafada, yayi saurin dagowa suka hada ido...
Yana kolon sa ya gane shine saurin da ya biyo nadiya ranar nan...
Daya daga cikin su ya daga gora zai manawa shaffik a kai...
Mado yayi saurin daga masa hannu alamar su rabu da shi...
Hatara na birin ya fafa cikin kwaleliyar  muryar sa...
Sukayi gaba ya bisu da kallo....

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now