Seventeen

192 18 1
                                    

Episode seventeen
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Ji yayi bazai iya fuskantar abun da ya ke faruwa dashi hakan yasa ya baje akan gadon yasha baccin sa.
Dan ahmad mutun ne mai ko in kula da rayuwarsa, baya son abun da zai chaza masa kwakwalwar bare ya daukar masa lokaci.
Washe gari haka bai je aiki ba dan ba aikin sa bane wannan.
Bai tashi ba sai wajen sha daya, koda ya tashi haka ya fito waje, yaga habubakar da matti a waje daya daga cikin mutanen da ya hadu da su randa ya dawo gero, yayi ta musu hira ya gayace su gidan shi yayi musu girki iri iri, su kuma suka kwasa suna ta santi dan basu taba cin irin girkin ba, wasu ma kasa ci sukayi dan kwayanci, haka har akayi azahar suka fita suka raka shi masalaci sukayi sallah sannan ya dawo gida shi kadai, yayi kalo da games dinsa, bayan la'asar ya tafi neman nadiya.
Kai tsaye gidan su yayi ya jira yajira bai ba fitowarta ba, bai kuma jiyo haya niyad su ba, hakan yasa ya hakura zai koma ko ya nemeta wajen rafi.
Chan ya hango ta ita da bintu suna tafe suna tafi sun shekewa da dariya duniyar ta musu dadi.
Shima yayi dariya..... ya karasa inda suke
Ganin shi yasa bintu tayi saurin cewa ita ta tafi gida sai allah ya kaimu.
Ta juyi a fusace tace mallan ka dena bina dan allah...
Ya jujuya yana neman da wanda take sai kuma yace niiii...
Ta zumburo masa baki tayi wuce warta...
Ya bita a baya yana kallon ikon allah..,
Ta kuma juyowa tace kadena bina dan allah bana so inna tani ta ganmu tare ko a je a gaya mata...
Yayi kasa kasa da murya yace...
Nadiya wai me nayi miki ne, meke faruwa...?
Wai meyasa ma zaka dunga bin wadda baka sani ba...
Wadda ka wulakanta gaban abokanen ka, dan allah ka tafi...
Yayi ajiyar zuciya yace nadiya ni fa kike kora...
Ba ta jira jin abinda zaice ba ta shige gida.

Ya kwashi kafafun sa ya wuce gida....
Yana shiga ya fada kan kujera kansa cike da abun da Nadiya tayi masa, ama meyasa zatayi masa haka.
Ta ma ki ta saurare shi..,
Chan wani tunani yazo masa da yayi zumbur ya mike daga kan kujerar ya zauna, kar dai da shaffiq ta hadu ya numa bai santa ba, ya wulakantata.
Wayar mummy data shigo ta katse masa tunani..
Ya dauka jiki ba kwari tare da cewa mama...
Shaffiq meke damun ka da yau kwana biyu bakayi reporting a company ba...
Cikin yan sakani ya calcular shi da shaffik maman su daya kennan, dan babu ko tantama wannan ita ce mamarsa...
Shaffik magana nake maka fah
Mama gobe insha allahu zani...
Meya hana ka zuwa tun da...?
Kiyi hakuri zani gobe...
Baka da lafiya ne??
A'ah ya fada a hankali
Shaffik dan allah ka daure ka je gobe kaji dana
Ya amsa da to bawai dan yana son sansa suna shaffik ba.

  Washe gari da ya tashi ya dako wasu kananan kaya ya saka, shi bai yarda ba yayi shigar zuwa aiki, ya shirya cikin irin salon shirin sa ya fito ya tafi aiki...
Koda yaje mutane suka dunga yi masa batka da zuwa ama saidai sun ga ba daidai ba tare dashi, mutumin da zai sa suits yayi shiga mai kyau shine tazo aiki a haka, kamar zaije wajen abokanen sa.
Sa sakin fuska da gaisuwa harda yar tsokana..
Mutanen kasan sa kuw sunji dadin sauya warsa dan wasu daga tsohon branch dinsu aka dawo dasu nan...
Ahmad yayi aiki yanda yake so yakuma sa doka da dokoki dadi dadi son ransa da yanda yaga yayi masa wanda suka sha banban da na shaffik gaba daya.
Da yan ma da aka tashi daga aiki yaji baya son zuwa gida dan ko yaje bakowa shi kadai zai karaci zaman, hakan yasa ya shiga gari.
Sai da ya zagaye gero gaba daya a hanyar dawowar sa kuma ya hadu da nadiya da garken shannun ta ta dawo daga kiwo...
Yayi sauri yake yasha gaban ta ya kira sunnan ta...
Ita fah a dole ya mata lefi shi yasa ko saurarar sa batayi..
Nadiya nayi miki lefi ne?
Nadiya inna Tani ce ko mado?
Waya taba ki wai??
Wannan karon bata ce masa komai ba sai sannun ta da take kada wa...
Nadiya idan nine ki fada mun kiyi magana dan allah, nadiya kinsan dai haka kawai bazan ganki in share kiba, nadiya kece mace dana fara gani a duniya sunnan ki shi ya bude mun kunne, me zai sa na wulakantaki...
Cikin shagwaba ta zumburo baki tace toh waye☹️ in ba kai ba..
Nadiya dan uwa na ne..
Tayi saurin tsayawa ta juyi ta kalle shi..
Ku yan biyu ne....
Ya gyada mata kai eh hassan dina ne nine ussaini...
Tayi shiru ta matso kusa da shi ta kalle shi cikin ido, cikin mamaki da dan gajeren runani da tayi..,
Ta sauke lumfashi tace...
Sai na tabatar da hakan....
Ta yaya....
Dan uwan ka ya fiya fada, shi yasa daga mai magana ya hauni da masifa kamar zai dake ni....
Kuma jan ido ne da shi kai kuma idon ka fari ne....
Yayi dariya yace abun da kika gano kenan...
Kuma shi ya fiya zafi...
Toh kiyi hakuri ai bashi da lefi dan bai sanki ba bai taba ganin ki ba...
Eh haka ne kuma, tayi murmushi tace kayi hakuri nima abun da nayi maka...
Yayi murmushi yace ba komai nadiya ai biki sani bane....
Gaka sukayi hirar su sannan ya taya ta kada shanun gida, a hanya ya fada mata shima ya zama dan rugar su, dan kuwa ya dawo nan da zama, tayi murmar hakan sosai dan har tana tsokanar sa dan birni ya dawo kauye.

Yana shiga gida yaga an dauke wuta, gidan duhu gashi wayar shaffik ba chaji ga duhu ya rasa yanda zai yi dan baya son duhu ko kadan hakan yasa ya lalubo ya sako kasa zai kunna inji...
Bai kula ba sai ji yayi kummmm ya buga kansa da bango cikin duhu...
Zafin buguwar yasa kansa ya juye duhu ya ziyarci idanun sa da har sai da ya fadi...
Bayan yan sakanni ya farfado, ransa a bace...
Yama rasa me zaiyi gashi cikin duhu, kafin ya mike aka kawo wuta, ya koma ciki yaga fallon sa da kitchen dinsa kamar bola kamar gidan da akayi taro aka watse, ya hau sama da gudu yaga takardun sa da duka kayan sa a kasa, komai an baza a kan gado da kasa, maclean da brush da shaver a kan gado, toilet kacha kacha ko ina ruwa....
Ya kuma sakowa kasa yaga kitchen kamar wanda akayi girkin gidan biki, ga uban tilin wanke wanke, ya bude fridge yaga duka kayan daya taho da su sun kare.
Ya duba calendar yafa yau 15 ga wata alamun yau kwana uku kenan.
Inalillahi waina ilaihi rajiun 🤯🙆🏻‍♂️

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now