Thirty six

138 15 2
                                    

Episode thirty six
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)
"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Washe gari da sasafe Ahmad ya dau hanyar kano, cikin minti 45 ya isa kano sai da Attahir ya yayi masa kwatance sannan ya gane gidan sannan ya faka a kofar gidan yana jira ya fito.
Ko da Attahir ya fito cewa yayi shaffiq ya koma dayan side din dan tafiyar tasu mai nisa ce, kuma shi yasan hanya.
Ba musu ya fito ya bashi keys din motar..
Sai da suka shiga mota kana yace masa wace tafiya zamuyi ina zamu?
Dala zamu....
Dala? Me kuma zamuyi a dala Attahir....
Bai kula shi ba ya tada motar ya ja su suka dau hanya.
Sunyi tafiya ta kai ta kimanin minti 15 kafin Attahir ya juyo ya kalli Ahmad da ya baza ido sai kallon hanya yake yi, ya kuma baza hanci yana shakar fresh air, garin yayi lif-lif kamar za'ayi ruwan sama....
Ahmad, Attahir ya kira sunnan shi, ya juyo ya kalle shi...
Ahmad wai baka son ka san mai ke tsanin kai da shaffiq, baka taba tunanin me yasa kuke rayuwa a jiki daya ba bayan ku mutane daban daban ne......
Hakan baya damun ka??
Hannun sa ya zura ta window iska na kada shi yace...
Attahir bani da wata damuwa, idan har zan kasance tare da Nadiya, ba dan kowa nake tayuwa ba face dan Nadiya...
Ama baka tsoron nadiya ta gane cewa ku ba yan biyu bane, idan ta gane me zaka cemata...
Ya juyo ya watsa masa wani kallon tambaya, sai kuma ya hadiye tambayoyin sa ya juya kawai ya kalli titi dan baya son maganar.

Har suka isa kofar asibiti, basu kara yiwa juna magana ba, sai da Ahmad yaga asibiti suka shigo sannan yace, asibiti cike da mamaki...

Zai wa Attahir magana yaga inaaaa ai shi har yayi gaba ma...
Me wannan gayen yake tunani me??
Yayi wa kansa wannan tambayar, ya bishi a fusace sukayi ciki dan yanaso yaga ikon allahn da yake kokarin yi...
Dr Fauziya na zane tana clearing wasu takardu zata bawa massenger dinta yayi submitting dinsu a board suka shigo...
Bata musu magana ba har suka sami guri suka zauna sai da ta gama sannan tayi musu sannu da zuwa.
Tace da Ahmad ya karaso ya zauna kujerar da ke gabanta...
Ya juya ya mana wa Attahir harara sannan ya tashi yaje ya zauna ba dan ya so ba..
Attahir ya kalli likita da taso tayi dariya itama dan ta gane yanayi.
Ta dan kara yin wani murmushi da ya bayana kafin tace
Ahmad...
Ya kalle ta alamun ohh har sunana ma kun sani...
Sai kuma tace nasan baka san dalilin ka na zuwa nan ba, ama ina so ka kwantar da hankalin ka. sunana Dr Fauziya last week shaffiq yazo ya same ni da labarin ku, nan ta kwashe labarin kaf ta fada masa...
Labarin da shi bai san da shi ba bai san hakan ta taba faruwa ba, kansa ya daure ainun...
Abun da yayi masa dadi shine kokonton da yayi rayi a baya na Nadiya ce sanadiyar zuwan sa suniya...
Nan ta dako results sin test din su gaba daya ta nuna masa tayi masa bayani sosai , sannan ta yi masa tambayoyi ya dunga amsa ta kai tsaye ba tare da yasha wahala ba irin na shaffiq.
Memories dinsa na nan intact...
Ta fada tare da girgiza kai...
Ta tambaye shi baya jin wani abu idan zai sami sauyin yanayi, ya bata amsa da babu abun da yake ji shi kawai chanza wa yake...
Bayan ta gama yi masa yan tambayo ya bata amsa sai take ce masa..,
Ahmad ina so ka bani goyeb baya kaima domin mu sama muku masalaha...
Yayi murmushi alamun rashi gamauwa da rashin damuwa...
Ya gyara zama sannan yace
Kinga likita, rike maganin ki da masalahar ki, banaso kuma bana bukata...
Idan sauki da lafiya kuma kike nema toh gskia kinyi kuskure dan ni lafiya ta garauu...
Idan kuma shaffiq ya kuma kawo kansa nan wajen toh ki tabatad kwakwalwar sa kika tsayar ba tawa ba....
Idan kuma baki tsayar ba toh ni zan tsayar masa da ita.....
Ba shiri ya mike fuuuuuu ya fice.....
Attahir ya kalli Dr da ta juyo tana kallon shi yace yanzu ya za'ayi kenan Dr...
Ta sauke ajiyar zuciya sannan tace, gaskia he processes alot, emotions din shaffiq duk suna tare da shi, shaffiq bazai taba iya ci gaba da rayuwa ba a wannan situation din dan kwakwalwar Ahmad tafi tashi karfi nesa ba kusa ba....
Yanzu meye abun yi....
Abu na farko shine kula...
Dole sai an kula da shaffiq sosai dan ba'a san mai zai iya faruwa tsakanin su ba, sannan kuma an lura da yada abubuwa ke tafiya tsakanin su...
Idan muka ce zamu tsaida brain din Ahmad toh tabasss shaffiq zai iya nakasa, dan babu emotions a cikin ta, daga haka kuma zai iya generating wani personality din da zai masa hakan kaga anyi ba'ayi ba kenan..
Yanzu dai zamu bari mu ga what will go on tsakanin su daga nan zuwa 6months kafin mu san abin da zamuyi.
Ama wata shida baiyi yawa ba likita,
Kar ka damu insha allah hakan za'ayi.
Attahir yayi hucin iska yace toh shikenan likita allah ya kaimu, ya mike ya fice tare da yin godiya.....

*****************************************************
To be continued  insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now