Thirteen

217 18 0
                                    

Episode thirteen
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ
Cikin wannan yanayi shaffik ya cigaba da kasancewa, yau tsawon kwana hudu kenan, komai ya chanja masa, komai ya dauke masa ga kuma wani sabon suna da ake makala masa wai shaffik, ga chanjin mutane dan kowa kallo na farko yake yi masa, bakomai a kansa saidai kuma da an fada masa sai ya zauna.
Kowa kallon lamarin sa mamaki yake bashi ama sai dai kawai ayi shiru ba tare da an tanka ba ganin shine oga.

Yau yana aiki , ama tun safe bashi da wani tunani sai na nadiya, hakan yasa ya kudiri niyar sai yaje yaga nadiya yau.
Bai ko tashi daga aiki ba, ya fifo ya hau mota bai tsaya ko ina ba sai gero..
Yayi parking a bakin company dinsu sannan ya sakai cikin rugar gero, dayake har gida ya bita ba tare da tasani ba hakan yasa yayi gidan su kai tsaye....
Ya jira ya jira yaga fitowar ta bata fito ba yafi minti 15 a tsaye ama shiru babu kowa har yazo zai kwankwasa langalangan kofar gidan da sukasa suka katange gidan yaji jifa da kwanika,
Gwara na kashe ki nasan na kashe ki kafin ki kashe ni ki kashe mun da, dan uban ki meye da mado, duk rugar nan akwai mai son ki in ba madon ba?
Shegiya mai bakin jini shekara har goma sha 19 ama baki san da namiji na, babu wanda yake son ki saboda bakin kashi,
Ta kuma jefo ta da murfin tunkunyar karfe tare da fadin
Toh wallahi na gaji da goga kafada da ke a cikin gidan nan, ko gawar kice sai na kai dakin mado, idan yaso washe gari a kaiki.
Bari lamido yazo mako mai kamawa za'a daura muku aure...
Cikin kuka da bakin ciki da takaici tayo waje a guje, bata lura da shi ba tayi karo da shi, dayake ta rufe idanun da da hannun ta.
Ta dago ta kalle shi, cikin murya kasa kasa yace...
Nadiya .....a great
Wani sabon kuka yazo mata, ta fashe da kuka ya zura a guje,
Ba shiri shima ya bita...
Bata tsaya ko ina ba sai bakin rafi tana kokarin tundumawa.
Nadiya! Nadiya!! Nadiya!!!
Me kike kokarin yi, nadiya baki san hukuncin wanda ya kashe kanshi bane, nadiya bakisan wanda ya kashe kanshi bashida banbanci da wanda ya mutu kafiri ba.
Gwara na mutu na huta da wannan rayuwar...
Ta fada cikin kuka....
Ya karaso gefen ta ya tsaya...
Nadiya zaki mutu ama sai lokacin ki yayi, kowane mai rai mamaci ne ama allah bai bamu ikon daukar ranmu ba.
Cikin kuka ta kara fadin
Idan ban kashe kaina ba mado da inna Tani kashe ni zasuyi😭
Gwara su kashe ki da ki kashe kanki nadiya domin lafifin mutuwar ki a kan su zai kasance ba akanki ba nadiya.

Wannan shine karo na goma shabiyu mado na neman keta mun hadi, inna Tani kuma gani take hakan daidaine. Gani take kamar hakan shine dacewa ko burgewa, gani take kamar kyamar danta nake yi, wallahi bazan iya rayuwa tare da mado a matsayin miji ba, da na auri mado na kwamace na mutu wallahi...
Nadiya ki dena kukan haka, allah ubangiji yana jarabar ta fani da yawa a duniya, allah kuma yana mana haka ne domin ya jaraba imanin mu, jarabawa ce daga allah nadiya ki daure kici wannan jarabawar kinji nadiya.
Haka shaffik yayi ta lalashin nadiya har ta ta sako ta dena kukan.
Ya mika mata hankicin sa yace ta goge hawayen ta, ta karba ta goge
Tana cikin gogewa ya tambayeta ina mamar ta da baban ta...
Ta dago tace allah yayi musu rasuwa tun ina karama...
Ya gyada kai yace toh allah ubangiji yayi musu rahama, yanzu wajen innar ki kike kennan.
Ta gyada masa kai eh...
Nan dai sukayi ta yar hira har sai da ta saki jiki ta saki ranta.
Yayi mata murmushi, yace idan kina dariya kinfi kyau saboda haka ki cigaba da dariya kinji nadiya idan allah yayi duniya dan manzo ke ba matar mado bace kinji ko. Ki cigaba da addu'a.
Wai me yake kawo ka nan rugar ne wai??
Yayi shiru sai kuma yace....
TAIMAKO
TAIMAKO?
Eh taimako,
wa kake temako to?
Yayi murmushi ya nuna ta yace ga kina...
Wancen karon na temake ki, daga kashe kanki wannan karon ma haka...
Tayi dariya tace kai malan ahmadu ka fiya zolaya...
Sai kuma chan yace, maman mu ke gini a cikin kauyen gero, toh ina zuwa temaka mata ne??
Tayi murmushi tace toh allah ya temaka.
Ya raka ta har gida sanna ya koma wajen da ya faka motar sa.
Yana daidai jikin motar yaji kansa ya sara, yayi saurin dafewa ya jingina da motar dan yana neman faduwa, duhi ya ziyarce shi sai kuma chan ya mike abun shi.
Ya duba agogon yaga karfe shida saura, an kusa yin salar magariba, ya dubi kayan jikin sa yaga ai ya dade bai saka wadanan kayan ba ma , hasalima baya son kayan ama yau sune a jikin sa.
Toh meya kawo shi gero ma yau tunda yau ba aiki ake yi a wajen ba.
Yayi tsaki kawai ya shiga mota ya koma gida.
Koda ya koma yau ta kofar da ya saba shiga ya shiga, yayi saman sa direct dan bai biyo ta bangaren mummy ba yau...
Yana shiga ya tarda dakin kacha kacha, an hautsina dakin baki daya, kayan sa duk a kasa, ga kwalin lemo da kwanan abinci duk a kan reading table dinshi.
Komai a bude ga takardun sa dun an wargaza masa.....
Ransa yayi mugun baci dan babu abin da ya tsana kamar yaga an shigar masa daki an nata masa waje, shi yasa baya son masu aiki ko kadan a saman sa.
A zuciye ya sako yana kwalawa mummy kira
Mummy mummy....
Tana falo tana jin shi dan abun shi ya fara zama iskanci yau kuma mummy yace cemata bayan ya gama mama mama...
Yau kuma mummy na koma..?
Mummy waya shigar mun daki kinga yanda aka maida gurin upside down...
Komai a wargaje.....
Wa zai shigar maka daki, ni yau kwanana uku ban hau saman ka ba dan kafara ciwo take, larai da asabe kuma ko fallon nan basa shigowa idan ba ni na kira su ba, toh wazai taba maka waje inba kaiba.
Mummy nidai kizo ki gani wannan ya wuce hankali...
Ba musu ta bishi saman,
ile kuwa hakan take, ta kali wajen tace
Wannan kwalin lemukan jiya kazo ka dauke su daga kasa, har ina tambayar ka na firge dinka sun karene?
Wannan kwannan yau anan kayi breakfast dan zuwa kayi kace kana da abin yi a sama saboda haka sama zaka ci abinci...
Wannan kayan su kasa shekaran jiya
Wannnan wacen shekaran jiyan
Haka dai rayi ta gaya masa abubuwan da yayi da kagan sa, ta kuma tabatar masa da cewa shi yayi kayansa ba wani ne yayi masa ba.....
Ta sa kai ta fice ta bar masa dakin.....
Ji yayi kamar yayi hauka mai meke faruwa da shi ne, yaya abubuwa ke rikitashi haka yayi abu bai san yayi ba, wane irin cutar mantuwa ke damun shi....

*****************************************************
To be continued  insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora