Thirty nine

189 13 0
                                    

Episode thirty six
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)
"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

A rude ta dau waya ta fara kiran abba khalid dan bata san me zatayi ba, jin bai dauka ba yasa ta kira Attahir, shima bai dauka ba hakan yasa ta yanke shawarar kiran Dr habib tijani dr din da ke dubata, kafin ta kira shi wayar Attahir ta shigo.
Murya na rawa tace Attahir meya sami shaffiq ne, wani abu ya faru wajen aiki ne ko cin abokanen ku, nan ta kwashe labarin abun da ya faru ta fada masa....
Shima a rude ya fito daga gida yana mummy kar ki kaishi asibiti dan allah ina zuwa akwai inda zamu kai shi....
Cikin mintina kadan Attahir ya shigo, da yake tun a hanya ya kira dr fauziyya, duk da bata asibitin ama tace gatanan zuwa.
Lokaci daya suka karaso, ana zuwa aka yi emergency da shi, ganin yanda aka rikice kanshi yasa mummy hankalin ta ya kara tashi dan ita bata san meke faruwa ba.
Cikin lokacin kadan aka yi masa Brain CT, MRT BRAIN, FBC, CRP,EUCR,da sauran gwaje gwaje...
Bayan awa daya dr fauziyya ta foto tace, "madam we need to perform an emergency surgery on your son dan yana cikin matsala idan har bamu buda shiba yanzu, zamu iya rasa su duka su biyun..."
Duka su biyun...??
Shi da wa???
Dr fauziyya ta kalli Attahir da idan hankalin da yayi dubu to duk a tashe yake ya girgiza mata kai alamun bata sani ba...
Ta lumshe ido sannan tace, ba damuwa madam its an emergency case idan muka fito zan sanar da ke halin da ake ciki, ga wannan form din ki cika da kuma form din bill...
Abun da nake bukata da ke shine kawai trust me insha allah everything will be fine.

Tana mika mata aka fito da shi kan gado ana tura shi sukayi OR da shi....

5hours surgery akayi akan shaffiq da Ahmad, shima ba dan an gama ba Dr fauziyya ta fito ta sanar da mummy da Attahir halin da ake ciki...
Suna zaune bakin OR din sunyi jingin jingun mummy sai charbi take ja tana masa salloli, dr fauziyya ta fito tace tana son ganin su a office dinta....
Jiki ba kwari suka bita zuwa ofishin nata suka zauna...
Madam am sorry da zamu fada miki halin da yoron ki yake ciki yanzu, da nasan baki da masaniya a kan lamarin shaffiq da na takura masu sai sun sanar da ke...
Mummy ta share hawayen ta tace me ke damun shi likita...?
Shaffiq yana dauke da cutar Dissociative identity disorder wanda muke kika da multiple personality disorder...
Hakan ya faru sanadiyar abuse da trauma da ya samu a shekarun baya da suka wuce, shi yasa yake amsa suna biyi, wato shaffiq da kika sani da kuma Ahmad...
Ahmad da shaffiq mutane ne guda biyu da babu ko abu daya na su da ya zama daya, sai dai suna raba jiki daya ama kwakwalwa kowa da tasa, shi yasa kike ganin akwai abun da shaffiq ya sani wanda Ahmad bai sani ba, wanda Ahmad ya sani shaffiq bai sani ba..
Ahalin da ake ciki yanzu shaffiq ne ya shiga emotional stress wanda ya janyi masa shiga wannan halin...
Kamar yanda ma fada musu solution guda daya ne wanda za'a dakatar sa kwakwalwar daya daga cikin su..
Yanzu muyi iya bakin kokarin mu muga mun tsaida kwakwalwa guda daya wanda bamu san ko ta waye ba, yanzu zamu jira farfadowar sa muga wanda zai farfado....
Tana kaiwa nan ta mike, ta dau waya ta fice...
Mummy ta share hawayen ta ta kalli Attahir tace Attahir meyasa kuka boye mun, ni fa mahaifiyar sa ce, ko ban masa komai ba ai na yi masa addu'a, baka tunanin nima ina damuwa da wannan sauyin yanayin nasa da nayi zata mantuwa ce tayi masa yawa....

Mummy kiyi hakuri shaffiq ne yace kar mu sanar da ke kar hankalin ki ya tashi, haka dai yayi ta bata hakuri har aka fito da shaffiq daga dakin tiyata....
            ****************************
Yau kwana biyu kennan, suna jiran farfadowar shaffiq ko Ahmad, ko motsi bayayi sai nunfashibda yake yi da oxygen...
Mommy na gefen sa tana yi masa tausa, tana tofa masa yan aduoin ta, Attahir kuma ya tafi gida ya kawo musu breakfast.

Yan yatsun kafar sa ya fara motsawa a hankali mommy na ganin haka tafara godewa allah...
Chan ya fara kokarin zare oxygen din hancin sa...
Mummy ta taya shi,
ya cire ya bude ido a hankali....
Ta kira sunnan shi a hankali shaffiq
Jin kansa a dadaure yasa yayi kokarin mikewa,
Mamaaa, ya fada da kyar...
Mama ta kuma maimaitawa, wasu hawaye suka zubo mata ta rungume shi tana, Ahmad Ahmad dana...
Am sorry Ahmad, kayi hakuri ka yafe mun dana....
A daidai lokacin dr fauziyya ta shigo
Suna hada ido ya razana ya mike ya funcike drip din sa pluses oximeter da nasal oxygen da ke jikin shi...
Ransa a bace ya mike ya bige mummy har tana shirin faduwa, ya fara nuna Dr fauziyya yana wannan matar!!wannan matar!!wannan matar!! wannan matar so take ta halaka ni, wallahi ba zai yuwu ba, bazan zauna ba idan har matar nan na nan, wannan matar so take ta tsayar mun da rayuwata, bazan taba sadaukar wa da shaffiq da rayuwata ba, bazan sadaukar ka da Nadiya ga shaffiq ba....
Kansa ya dauka ya dunga bugawa a bango yana kokarin salwantar musu da rayuwa baki daya....
Mummy ta fizgo shi ya hankade ta ta fadi kasa, dr fauziyya ta karaso ya dau tray din magungunan ya jefa mata a fuska, duk abun dakin da ya gani sai ya yi jifa da shi yana ihu.

chan ya hango wukar da mummy ta yanka fruits da shi dazu, ya karasa wajen a guje ya rarumota....
Ba shiri mummy ta mike cikin hawaye tana no Ahmad Nooo, dr fauziyya tayi waje da gudu dan a shigo a kawo musu a gajin gagawa.....

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon