Twenty nine

118 13 0
                                    

Episode twenty nine
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Fuskar shaffiq a cukune, suka fito yaja wani tsaki yace wallahi da nasan likitan nan babu abun da zai iya yi mun da nasani ban saki baki na yi masa bayani ba, yanzu zai dauke ni kamar wani mahaukaci...

Attahir ya kalle shi yace, kaifa matsalar ka kennan da bamu ganshi ba da yanzu ai bai hada mu da ita wannan likitan ba, tunda kaji yace akwai irin wannan cutar a littatafai akwai ta kennan kuma insha allahu za'a magance ta, kaidai ka kwantar da hankalin ka.

Attahir ni kawai zan hakura maybe wannan jarabawa ce kawai allah ya dora mun, zan cigaba da addu allah ya bani ikon cin wannan jarabawar.

Kaji ba, wata matsalar taka karaya, ance maka cuta mutuwa ce, koma meye babu cutar da bata da magani a duniyar nan, ni a gani na ma idan kuka zauna kuka fahimci juna kai da Ahmad zaku sami zaman lafiya bazai dunga shiga sabgar ka ba, zaku ji dadin rayuwa, gayen bashi da matsala...
Shaffik ya bashi yani wawan kallo kai baka da hankali ko, kar nayi maka addi'a da nace kaima allah ya dora maka.

Kaga Attahir bama haka ba, shi fa Dr din nan yace shi bai taba ganin irin wannan ba, yanzu kana da tabass din idan mun ga wannan likitan zata gane kan wannan cutar ita...
Nifa kawai zanje na gaya wa mummy idan yasi ki Germany muje maybe su zasu iya...,

Attahir ya matso kusa dashi ya dafa kafardarbsa yace danuwa mu dai fara gwada wannan likitan first,....
Kai wallahi gwara ahmad din ma a kan ka, bashi da kafiya sa taurin kai irin naka...
Shaffik yazo kai masa duka yayi sairin janye jiki ya zare mukulin motar daga hannun sa yana dariya yace shiga muje ni kar muje kayi mana accident a hanya.....
A gurin aiki ya ajiye Attahir shi kuma ya wice gida dan gaida mummy.
Sai da magaruba ta gabato sannan yace zai tafi dan har mummy na ce masa ya maida gero kamar daganan zuwa nan, yayi murmushi yace mummy ai ba nisa, yanzu zakiga na isa....
Ta dage da ya tsaya yayi sallah ama yace mata zai tsaya a hanya yayi, haka ta hadi shi da kayan ci da sha da har zai ce bazai karba ba saboda yanzu bashi da matsalar abinci sai kuma kawai ya karba dan kar ya samata shakku.

A masalacin bakin titin gero ya tsaya yayi salar magariba, da yake yayi wani mugun sauri cikin minti 40 ya iso.
Ko da ya shiga mota zai karasa gida ya hango ta cikin duhu sai sauri takeyi kamar zata tashi sama....
Zanin ta da ya bingile sai harde ta yakeyi ga isaka na neman kwashe ta tsabar rama, sanye take da riga da zani duka daban daban sai dankwalin tsofafin da ta daura ta saki jelar dan kwalin, mayafin a hannunta riko shi sai ledar hannun ta da tayi mata nauyi sai faman kokawa takeyi da ita.

Haka kawai yaji yana son temaka mata, har ta zo ta wuce ta gaban sa bata shaida shi ba sai da ya yi mata horn sannan ta juyo da saurin ta..
Da yake duhu ya ruga ya fara bata tantance su ba hakan yasa ya zuro kai ta kalle shi da kyau sannan ta gane shaffiq ne,
Ba ko tantama tace lahhh shaffiq ashe kaine...
Abun ya bashi mamaki yanda take banbanta su kai tsaye haka.
Daga ina kike....
Inna tani ce ta aike ni sauri nake yi gashi duhu yayi cewa zatayi yawon banza na tafi kwara nayi sauri na tafi...
Tafiya ta soma yi dan ji takeyi kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gida dan gudun fadan inna tani...
Horn ya kara sakar mata da ya gigitata, tayi saurin juyowa idon ta dauke da alamun meke damun ka nace maka sauri nake....
Shigo na rage miki hanya...
Bata ko juyo ba tace masa a'ah Nagode....
Ta cigaba da tafiya...
Wani horn din ya kara sakar mata, gudun kada ya tara mata mutane yasa ta matso kusa, fuskar ta a daure wannan karon, bai ko kira jin mai zata ce ba yace shigo mu tafi....
Bata musa ba ta shiga suka tafi....
Bai taba ganin ranta a bace haka ba sai yau dan ko hada ido bata bari suyi dan ya shiga hakinta....
Nadiya, ya fada cikin kakaurar muryar sa...
Bata ko dago ba tace Na'am
Wai ya ake kike gane mu ne??
Tayi shiru kamar bazata amsa ba sai kuma tace
A jikina nake ji....
Jikina ke bani...
Ya danyi tunanin sakani sai kuma ya watsar da zancen, tare da fadin kinyi kokari.

Basu kara cewa komai ba har sai da ya ajiyeta bakin lungun su.
Ta fito tace masa ta gode sai da safe...
Yayi mata murmushi kawai yaja motar sa ya ware.
Yau kome ke damun wannan gayen, yau shine har da murmushi, mutumin da kamar sai ya ganta yake kara turbune fuska ama yau shine da sakin fuska.
Ta girgiza kai kawai ta shige ciki.
*************************************************
Yau kwanan shaffiq uku kennan da komawa Ahmad, tun ranar da suka dawo daga asibiti ya rikide ya koma ahmad, gashi jibi ne appointment dinsu da Dr Fauziyya
Kullun sai Attahir ya kira shi dan yaji waye zai dauka sai yaji ahmad ne, kawai sai dai ya wayance yace ai ya kira su gaisa ne....
Yanzu ya zasuyi idan har ranar zuwa asibiti tayi kuma shaffiq bai dawo ba????

Yau tun yanma yana gidan su Nadiya wajen inna tani, ya ke sun dade basu zauna sun sami doguwar hirar da suke yi ba.
Gaskiyar magana shine Ahmad na karuwa sosai a wajen inna tani, labarukan da dana kauye da al'adu da gangin su babu hirar da bata yi masa da yake shi mai magana ne ita ma mai magana hakan tasu tazo daya, dan yanzu ahmad dana take ce masa sama da kasa, shima duk yanda zai bi ya zauna lafiya da inna tani ya sani hakan yasa ake zaman lafiya, duk wannan bala'i da jarabar tata duk sun rage, ga jikin mado ma da yayi sauki sosai Alhmdulillah.
Sai da suka gama hirar su sannan shi da Nadiya suka fito, suna tafe suna hira, ya tsokanar ta tana dariya, dan yanzu har ya koya mata tsokana, hirar tasu duk chali chali ce da tsokanar juna da dariya.
Duk wata hanya da Ahmad zai biya wanzar da farinciki da nishadi a zuciyar Nadiya ita yake bi, burin sa guda daya a dunya shine yaga Nadiya kullun fariciki da dariya.

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant