Thirty five

137 11 0
                                    

Episode thirty five
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Sai da aka kwana 4 kana Ahmad ya bayana, koda ya rikede, babu abun da ya dawo masa sai faduwar da yayi a kan duwatsu yana tsokanar Nadiya, daga nan bai kuma tuna abun da ya faru ba.
Wani malolon bakin ciki da takaici suka zo masa nan da ya kasa hadiyewa, ya rufe ido cikin takaici tare da fadin wai ya za'ayi yayi maganin gayen nan ne...
Ji yake dama shaffiq mutun ne da zai kama shi yayi masa shegen duka ya kora masa warning din kar ya kuma ganin shi da Nadiya, shi yaga wannan bala'i.
Ya tashi a fusace ya hau sama ya fara kokarin saka kaya dan ko wanka bazai iya tsayawa yi ba dan zuciyar sa Nadiya kawai take ambato.
Wayar sa yaji tana ringing yayi saurin karasawa inda take ya dauka Attahir ne, dama ya kan kira dan yaji wazai dauka dan cika alkawarin Dr fauziyya.
Yana dauka ya gane Ahmad ne
Abokina kwana da yawa, wallahi dama yanzu nake shirin kiran ka, Inji Ahamd
Nima ina ta neman ka fatan dai komai lafiya ahmad...
Lafiya wallahi...
Attahir akwai maganar da nake so mu tatauna,
Toh shikenan ba damuwa....
Dama nima akwai inda nake so ka raka ni, zanzo gobe insha allahu ko kuma ka shigo kai sai mu wuce daga nan...
Ahmad ya amsa da ba damuwa insha allahu gobe zai zo kano.

A kafa ya taka ya je gidan su nadiya, inna tani ya tarar a tsakar gida tana dura manja a cikin kwalba,
A'ah a'ah lale lale...
Ta fada cikin murnar ganin shi...
Yanzu kuwa na gama cigiyar ka na jika shiru kwana biyu...
Yayi murmushi ya karasa kusa da ita kan tabarmar da take ya zauna yana fadin wllh Inna abubuwa ne sun fara yawa.
Nan ya gaishe ta ya karbi kwalbar manjan ya fara dura mata, suna hira.
Yayi ta waige waige ko zai hango ta ama bai ganta ba.

Chan ta shigo da reshen darbejiya a hannun ta riqe riqe yana ja dan ya mata nauyi,
Dagowar da inna tani tayi tagan ta da darbejiya...
Zaki ci ubanki ne wallahi shegiya yar banza wada ba'a isa a aike ta ba batayi shirme ba, dan uwar ki jego nake yi da zaki debo mun darbejiya, ita na sa ki debo mun, bama haka ba dan uwarki ina kika tafi tun dazu da sai yanzu kike dawowa da abun da bashi na aike ki ba.
Ta mike a zabure ta hau kwala mata mificin da ke gefen ta, Ahmad shima da saurin sa yazo ya shige gaban inna tani yana bata hakuri...

Ya hakuri dan allah inna, mancewa tayi, kinsan dan adam da matuwa, kiyi hakuri dan allah kiyi mata afuwa bazata kuma ba.
Ya bita da lalashi har ta huce ta koma bango ta jingina tare da fadin sai ki koma, ganyan nonon kurciya nace miki, in banda tsabar dakikanci da takwalanci inna bishiyar nonon kurciya tayi kama da darbejiya, yau kika fara ciro mun reshen..
Ta fita a guje dan kar ta kuma binta da wani dukan , shi kuma ahmad yace inna kiyi hakuri, bari na bita kar a kuma yin wani shirmen, shima ya fita.

Tana kofar gida ta tsuguna tana faman rera kuka...
Ya tauguna shima gabanta tare da fadin haba nadiya kar ki bata wayon ki mana...
Ganin bata da alamar sauraron shi hakan yasa ya rabu da ita sai da taci kukata ta koshi sannan ta dago suka hada ido fuskar ta duk hawaye shabeshabe...
Yayi murmushi ya kai hannun sa zai share mata tayi saurin kaucewa, ta tashi ta sa bakin dankwalinta zata gobe...
Ya kwace da sauri shima tare da fadin,hanuna bai fi dankwalin ki tsafta ba, ya fada tare da yin murmushi.
Yasa hannu ya share mata hawayen ta a hankali cikin nutsuwa tare da fadin nadiya, dan allah ki dena yin kuka a gabana, wallahi hawayen ki tayar mum da hankali suke yi, ko nima so kike na saka ki a gaba nayi ta miki kuka, ko kuma na dunga taya ki kuka.
Ganin ta bude fuskar da ta rufe yasa yace, toh kiyi mun alkawarin ba zaki kara ba...

Ta dan dage tayi murmushi ta e bazan kara ba, a hankali..
Me kika ce???
Bazan kuma ba ta kuma maimaitawa ciki ciki.,
Ya kara matsowa daf da ita yakuwa cewa ni banji ba...
Saukar lumfashin junan su suke ji, da kamshin turaren shi da ke kashe ta, tayi saurin dagowa ta kalle shi , kanta kawai take kallo cikin kwayar idon sa, idanuwan sa dauke da sonta da kuma shaukin ta.
Nadiya ya fada cikin tatausar muryar sa, gabanta taji ya soma doka wa da yasa tayi saurin ja baya...
Bazan kara ba nace ta fada da karfi ta..,
Dariya ta bashi, da suka yi dariya baki daya...
Cikin dariya yace toh mu tafi kar inna ta fito ta yi mana fada...

*****************************************************
To be continued  insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now