Fifteen

207 19 1
                                    

Episode fifteen
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Ginin galaxy manufacturing company yau ya kammala guri yayi kyau na gani na fada kai kace a turai kake, ginin ya dada fito da gero kwarai da gaske, an ruga an kamala komai na tsare tsare da shirye shiryen bude company.
Waje ne da za'a dunga hade hade chemicals din sarafa turaruka, man shafawa da sauran kayan kwaliya itin na mata. Shi yasa wajen yaji injina na gani na fada masu inganci da wadata, da yake bangaren shaffik ne hakan yasa yayi rawar gani sosai wajen ganin harkar ta kamala.
Idan aka gama producing daga nan manufacturing industry dake gero sai a dauka a kaishi marketing store din su da ke kano daga nan sai su kai galaxy mart , sannnan suyi distributing dinshi to whole sellers, haka ake exporting dinsu zuwa kasashe daban danan, duniya babu inda galaxy products bai zaga ba.

Yau ake gudanar da taron bude galaxy manufacturing company, a gero aka gudanar da taron, filin gurin aka samu aka samu aka kawatashi, aka tsarashi yayi kyau sosai wajen, mayan motoci kawai ke shigowa garin gero suna layi, haske da walwali kawai ke sheki a wajen, manyan baki ta kowane jaha sun gabata a wannan taro.

Yan kauyen gero kuwa yau sunga aljannar duniya, basu taba ganin taron jama'a irin wannan ba.
Da yake yau inna tani tun safe ta tafi birni wajen wani malami da taji labarinsa a birni ta bazama, ta bar wa nadiya jinyar mado hakan yasa tun safe tana gida bata san me ke faruwa a waje ba.
Shaffik da Attahir sun sha suits din su iri daya sun sha kyau sai walwali suke yi, tsayawa bayanin kyaun da PR habiba tayi kuwa bata lokaci ne dan kuwa, ta sha kyau iya kyau.
Attahir yazo ya bude taro da addu'a, bayan ya bude taro da addu'a, shaffik yazo ya bada takaichachen tarihi galaxy company, da dn jawabinsa, bayan nan PR habiba tazo tayi dedication description ta, malaka wa shaffik company din gaba daya, branch din ya zama nashi gaba daya. Dayan brance din kuma ta malakawa attahir gaba daya.
Attahir ya zama CEO din branch A shikuma shine president din branch B...
Fuskokin su cike da farinciki da nishadi, sai karbar gaisuwa sukeyi ta ko ina, haka aka kamala taro kowa sai sa alheri yakeyi.

Suna zaune kan dinning table suna cin abinci shaffik yace da mummyn sa
Mummy me yasa kike son surprising dina ne?
Ta kalle shi tace dana idan banyi surprising dinka ba wazanyi surprising. Ina son ko matuka dana, komai nawa da na malaka naka ne, dan kai nake rayuwa, dankai nake abun da nakeyi yanzu, dan inga ka sami rayuwa ingataciya...
Yayi murmushi ya rasa me ma zaice sai cewa yayi i love you too mummy.
Ama mummy zancen brance din gero baki gani zurga zurga zatayi mun yawa?
Kinga far 1:20 mints ziwa da dawowa every day its going to be tough.
Ta guara zama tace shaffik baka da matsalar wannan...
Ta kira asabe tace ta dako mata wasu mukulai akan mirror dinta, na daki.
Ta shiga ta fito tazo ta mika mata....
Ta karba ta mikawa shaffik da ya saki baki ya kalle ta, ya karba cikin mamaki yace wannan fah?
Penthouse dinka na nan a bayan company kafin ka karasa rugar fulanin da ke gero...
Mummy kauye.....
Shaffiq mai kauye yayi??
By the way sai kaje zaka ganewa kan ka, abun da na tana dar maka....
Ama mummy me yasa zan zauna a kauye, ke kuma kina nan...
Ta kamo hannun sa tace kwantar da hankalinka dana duk da kana da aure da ba zaka yi kewa ta ba, saboda haka kayi kayi kayi aure kaji dana, sannan duk abin da kake bukata akwai shi acikin penthouse dinka, zan hada ka da asabe ko larai daya daga ciki ta dunga yi maka yan aikace aikace, duk sanda kake so zaka iya dawowa gida, idan ma baka son zaman cen zaka dunga dawowa, yanda kaga yafi maka sauki da kuma wanda ka zaba shaffik.
Ya sauke lumfashi yama rasa me zai ce, sai kawai cewa yayi ni bana so...
Meye baka so?
Asabe ko larai ni kadai zan zauna...
Toh shikenan dama ai ka saba zama kai kadai....
Ba wai dan zuciyar sa ta amince da abun da mummy tace ba, ama kawai dan yana so ya faranta mata dan kuma karbya bata kunya dan kuwa abu ne da ta ruga ta tsara dan tayi surprising dinshi bai kamata ya bujure mata ba.
Nan ya dau mukulin ya tashi ya hau sama abun sa.

La'asar din lahadi da ta zagayo shaffik ya hada medium akwatin shi, da dukanin sauran abun da zai bukata , da side dishies din da mummy tayi mai wanda zai sa a fridge idan yaje dan babu abun da shaffik yaki jini kamar girki....
Ya sako kasa ransa dai ba yabo ba falasa, ya sako, sai da suka gama shan evening tea din su sannan ta raka shi har bakin mota ya dau niyar kauye gero.

Da yake tafiyar nawa yayi cikin awa daya da rabi ya isa garin gero, ya karasa penthouse dinshi, shi da kanshibya bude gate dinshi ya shiga dan yace da mummy baya bukatar wani mai aiki a gidan, dan gudun mutane da yakeyi.

Makeken gidan ne yanda kasan zubin hotel haka aka dangara wannan gida, abun ka da ya saba ganin gidaje masu kyau kuma yasan mummy sa bazata yi abu mara kyau ba hakan yasa ko mamakin gidan bai yi ba.
Gidan ba wani fadi ne da shi ba sosai ama ya tsaru cikin tsarin wanda suka san kan tsarin gida, sama da kasa ne gidan ama duk saman ta falon kasa ake shigar shi.
Kasan ya kunshi study room dinshi, bed room daya sai makeken kitchen da toilets biyu da makeken falo da yaji kayan lantarki, da kayan zamani.
Saman kuwa yafi haduwa da anan aka fi zuba dukiya da duk wani abu da mummy tasan danta zai bukata da zai debe masa kewa, dan har gym tayi masa a sama dan mutun ne mai san motsa jiki shi yasa yake masha allah.
Yana shiga ya dauki kayan da ya taho da su ya saka a fridge, ya dawo fallo ya danyi kallon tv dinsa sannan ya hau sama yayi wanka ya sa kayan motsa jikin sa dan bashi da abun yi.

Yana zama kan chest press machine dinsa yaji kansa ya sara, yayi saurin danke kansa da hannayen sa biyu, wani irin matsananci ciwon kai da ya ziyarce shi ta farar daya, yayi saurin tashi ya laluba ya koma falo ya zauna chan duhu ya ziyar ci idon sa, sai kuma dub ya dauke, ya bude ido.
Ya mike yayi ajiyar zuciya ya saki wani murmushi da ya bayana jin dadin sa, yace na fito finally...😁

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Kde žijí příběhy. Začni objevovat