Twelve

218 22 2
                                    

Episode twelve
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Sai da shaffik ya gama yawace yawacen sa sannan ya, ya koma cikin site.
Wayar aljihu sa yaji tayi ringing yayi saurin dakowa ya kalli screan din yaga ansa Bro Attahir...
Bashi da idea din waye Attahir ama hakan ya dauka yasa a kunne...
Yaaa dan uwa yau ne fahh....
Yayi dumm sai kuma yace, yaune me?
Kai dalah dan rainin hankali, kai ka cika mantuwa, yanzu da ban kiraka ba ka manta kennan...
Yau zamu fita ni da kai da lawisa mana....
Ya kuma yin shiru dan bai kamo bakin zaren ba har yanzu sai kuma yace...
Ohoooo yaune, hahahaha, ashe yaune na manta...
Zanzo gida bayan magariba insha allahu in dauke ka..
Toh shikenan sai kazo...
Attahir ya kashe wayar ya tambayi kansa shin shaffik ya chanja ra'ayi kenan dan wancen karin da yayi masa magana cewa yayi bazai je ba ai budurwarsa ce ba tasa ba, da kyar ya shawo kansa ya yarda badan son ransa ba, ama yanzu ka jishi harda dariya?
Shaffik na kashe wayar ya yi musu salama ya hau mota ya koma gidan da ya baro...
Yana shigowa yaji ana kiran sallar azahar hakan yasa ya tsaya masalacin kofar gidan su yayi sallah sannan ya shigo gida...
Idan ya tashi shigowa ta kofar da take leading dinshi to dakin sa yake shigowa ama yau sai ya shigo ta main kofa...
Yana shigowa yaga makekem hoton shi shida mummy dinsa a jikin bango hakan ya kara tabatar wa wannan matar itace mahaifiyar sa.
Jin bude kofar da ba'a fiya bude ta ba sasa mummy tayi saurin cewa "waye annan"?
Bayan ya shigo har ya rufe kofar sanban yace mama nine...
Kai wa,,..?
Tayi saurin tasowa...
Sai taji ance nine Ahmad...
Ahmad???
Mama???
Yau shaffik ke kiran kanshi da Ahmad dan ko ita bata kiran shi da ahmad ko da yayi makaranta da shaffik yayi amfani ba da ahmad ba ama yau shi da kanshi ya kira kansa da ahmad🤔
Gashi kuma yau yace mata mama, rabon shi da yace mata mama tun yana dan karamin...
Hakan dai ta boye mamakin ta tace...
Shaffik an dawo kennan?
Yau kaine ta nan?
Yayi murmushi ya kalle ta, kallon da yayi mata yasa ya tuno ta tun tana yar budurwarta kafin ta tsufa haka, ji yayi yayi missing dinta...
Ya tuno da wahalhalun da suka sha a baya...
Duka su din baya ya dawo masa cikin kai...
Hakan yasa yayi saurin hugging dinta tare da fadin i miss you mama, mama kin tsufa yanzu, and you look happy yanzu, nagode allah...
Ta dago shi tare da fadin kai....
Baka da lafiya ne...
A'ah mama lafiya ta lau, am just happy to see you mun dade bamu hadu ba...
Kai bansan sakarcin banza, wane mun dade bamu hadu ba bayan ko awa 5 bakayi ba da barin gidan nan ba...
Yayi murmushi yace yunwa nake ji...
Toh maza kaje kayi wanka ka zansa larai ta kawo maka abincin ka dinning din sama...
A'ah in fara cin abinci tukuna dai mama yunwa nake ji...
Yashiga ya baje a kasa kan carpet, aka kawo masa abinci
Yau bazaka hau table ba, ka taba cin abinci a kasa ne...
Mama yau tuna baya zanyi...
Haka aka baje masa abinci akan carpet, ya bude yaga shinkafa da wake ne da miya, ba shiri yace ai sai an kawo masa mai da yaji, da kuma tumatiri da albasa...
Abun ya fara kai mummy ma kura, cikin fushi tace, kai wai lafiyar ka abun da bakayi ka tsure shi yau, ka taba cin abinci da mai ne sai yau zaka wani ce da mai zaka ci abinci, meke damun ka...
Mamaaaa... dan allah am sorry ama ki barni
Ta sami guri ta zubawa sarautar allah ido ya ci ya koshi ya tashi yayi ya nufi toilet dinta wai zaiyi wanka....
Bata ce masa komai ba ya shiga yayi wanka ya fito ya hau bude mata drower wai shi kaya yake nema...
Ta hasala ya karaso inda yake tace ka bani ajiyar kayan ka ne ko ka taba ajiye kayan ka a daki na... ka je dakin ka mana, ta nuna masa hanyar sama...
Ohh sorry nazata har yanzu waje daga muke ajiye kaya, ya fada kasa kasa.
Ya hau sama ya bude daki...
Dakin yayi masa kyau komai tsaftsaf ko kura daya babu a dakin bare tsinke...
Ya hau bude drawer yana kallon kayayaki na gani na fada, ya dau wannan ya ajiye wannan, ya gwada wannan agogon ya ajiye yasaka Wannan glass din yasaka wanna, har sai da ya hargitsa dakin gaba dayan sa, abun da shaffik yaki jini kennan yaga an bata masa daki.
Chan ya samo wasu kananan kaya ya saka jeans black da maroon shirt ya saka ya kwama agogo, wajen turare kuwa ji yayi babu wanda yayi masa, da kyar ya samu ya fesa wani sannan ya fito...
Yasako yace da mummy ai Attahir ne zai zo zasu fita, bai rufe baki ba sai ga Attahir...
Bayan sun gaisa da mummy sannan suka fita, shima sai a lokacin ya tuno Attahir shine aminin sa da sukayi wasa suna yara. Nan ya saki jiki da shi har sunje bakin kofa ya juyo ya kalle shi tare da fadin, kai meye haka wai wane kaya ne ka saka haka, ya ina yabon ka sallah zaka kasa alwala ne....
Wear something proper mana meye wannan kaya ....
Ya kalli kayan sa yace me kaya na sukayi..
Ni su nake son sawa, sune style dina, kar ka takura mun dama ka saba...
Kaji da shi ni wallahi kunya ma zaka bani..,
Haka dai suka shiga mota suka isa gidan su lawisa suka dauke ta suka wuce restaurant.
Cikin mintina kadan shaffik ya saba da lawisa shi da aka sani muskili, ya cika ta da surutu, shi kadai yake maganar ma, dan Attahir bai ma sami damar magana ba saboda zubar da shaffik yake yi.

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now