Fourteen

196 16 0
                                    

Episode fourteen
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡYau sati biyu kennan, da kwanciyar mado ba lafiya, ciwo ya kama shi da gaske dan yana kwance rai a hannun allah...
cuta ce da shi, wada ta dade tana cin sa bai sani ba, yakan yi ciwo fisha haka ya warke ama  bata taba kwantar da shi haka ba...
Inna Tani hankalinta a tashe yake kamar ta tashi sama , duk inda taji da labarin malami toh tana wajen, ta saida shani wajen hude kennan dan nemawa mado maganin ama har yau jikin jiya iyau.
Kasancewar inna tani cutar mado na kanta, danta kwali daya da take so rak a duniya, hakan yasa nadiya ta sami sauki sosai gurin inna tani dan bata da lokacin yi mata fada ko azaba, dan kullun tana hanyar neman magani.
Sai dai kuma aikin gidan suka kara yi mata yawa sosai dan itace komai na gidan yanzu.
Lamido kuwa gudan dan inna tani shiru shima tun da ya tafi makarantar almajiranta a gabas har yau bai dawo ba.

****************************************************
Shaffik ma yau sati biyu kenan bai sami matsanancin ciwom kai mai sauya masa yanayi ba, hakan yasa yake gudanar da alamuran sa yanda yake so.
Ya dade bai je gero ba dan yau sati biyu kenan rabon sa da gero saidai attahir da salih su gudanar da komai sannan su sanar da shi.
Yau suka kawo masa report din gini ya tsaya da kafafunsa ya kamata ya je yagani, hakan yasa suka dauki hanyar gero susu uku gaba daya.
Cikin awa daya suka isa gero, company yayi kyau masha allah kamar ba shi a gero ba.
Suna jikin wata katuwar bushiya suna tataunawa da takardu a hannun shaffik yana yiwa salih da Attahir bayani yana zana musu a takarda..
Wata yar budurwa tayowajen su, tana kallo su ta gane mallan amadun ta dan birin, dauke take da kwandan sassaken icen dan tamburawa a hannun ta dan magani ne ta debowa mado daga daji.
Cikin fara'a da jin dadin ganin shi ta karasa wajen su tare da fadin
Ahmad dan birin ashe kana duniya, yaushe rabo....
Ganin ya cigaba da magana bai ko dago ya kalle ta ba yasa tace...
Malan ahmadu dan birni....
Attahir ya taboshi tare da fadin da kai fa take...
Ya dago cikin mamaki yanuna kansa da biron hannun sa yace nii?
Tayi sakato tana kallon shi sai kuma cewa tayi baka gane ni ba ne?
Nice fah... nadiya...
Ya dan sauke lumfashi sannan yace yanmata ban sanki ba gaskia...
Ya cigaba daduba takardar sa...
Jiki ba ba kwari jikin ta yayi sanyin kunyatata da ahmad yayi... ta bar wajen
Zuciyar ta kamad ta fito waje azuciyarta tace laifinki ne nadiya, wayace kije inda yake ma, balantana ya kunyata ki, dama yan birnin nan haka suke duk mayaudara ne.

Attahir ya kalli shaffik yace anya kuwa baka san yarinyar nan ba,
Wlh ban santa ba, ban taba ganin ta ba ma , maybe wani tasani mai kama da ni, mai suna ahmadu.
Haka suka kamala abin da zasuyi suka koma.

Washe gari ma sai da ya kuma dawowa gero dan akwai abin da zaiyi clearing, da ya shigo ya gama abin da zaiyi yazo komawa ne yayi yayi motarsa ta tashi taki tashi.
Chan ta nuna alamun over heating tana bukatar ruwa....
Ya kalli geri gabas da yanma kudu da arewa, babu gilmawar kowa a wajen, ga babu masu aikin wajen duk sun tatara kayan su sun rufe sun tafi gida da yake yanmatayi, gari ne da dududu mutanen garin basu fi a kirga ba, hakan yasa da yanma tayi sai dai ka nemi mutane ka rasa kowa ya koma makwancinsa...
Har ya karasa bakin rafi baiga kowa ba, balantana ya roki ruwa daga wajen sa, chan ya hango wata yar budurwa ta dako tulun ta tana tafe tana yan wake waken ta...
Yayi saurin shan gabanta dan ya roke ta ruwa...
Baiwar Al....
Kafin ya karasa maganar ya gane ta...
Sai kuma yace dan allah ruwa zaki temaka mun da shi na zuba a motata...
Ta murguda masa baki ya wurga masa harara tace kai da kake taimako yau kuma kai za'a temakawa...
Bai gane mai take nufi ba chan kuma sai cewa yayi dan allah ki taimaka, ni da kaina zan dawo na debi miki....
Ba cewa kayi baka sanni ba baka taba ganina ba, akan mezan temaka maka nima ban sanka na ban kuma taba ganin ka ba...
Ta bashi haushi, akan me zai dinga bin wannan yar mitsitsiyar yarinyar yana hada ta da allah tana ki, ciki haushi yace
Ban sanki ba, bakuma zan sanki ba, dole ne na san yan matan rugar nan?
Cikin takaici ta juyo dan har ta fara tafiya sannan tace,
Babu dole ahmad, ba dole bane, nice ban fuskanceka ba tun wuri laifi na ne...
Ta sa kai tayi tafiyar ta.
Haka ya tsaya yana binta da kallo yayi tsaki kawai ya koma wajen motar gashi ana kusa salar magariba...
Ya rasa inda zai sa kansa, ko robar ruwa babu a motar sa balantana ya debo da ita, har ya yanke shawarar zuwa yayi salama cikin wani gida ya roki ruwa ya gani wani mai jaki da tankin ruwa a bayan sa, nan ya siyi ruwan sanna ya zuba wa motar tayi cooling down sannan ya tafi gida.

*****************************************************
To be continued  insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now