Sixteen

221 20 3
                                    

Episode sixteen
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Ya kalli jikin shi yaga sanye yake da short da single sport wears, ya jujuya ya ga a sabon guri yake nan ya fara zazagawa, yana kallon gidan, ya ma rasa inda yake hakan yasa ya fito waje, dan yaga ina ne...
Yana fitowa ga ganshi a geron..
Ya kuma sakin murmushi, ba tare da ya rufe gidan ba ya fito a yanda yake yayi wajen company dinsu yaga ashe an kamala komai, da yake mutun ne mai ja da kyau nan da nan ya gano ashe an gama company shi yasa shaffik ya dawo gero dan ya kula da wajen,
Yana tafe yana wa kansa magana yana hakan ma ai girma ne gwara da ya dawo nan din yanda zai dunga ganin nadiya kullun.
Duk wanda ya hadu da shi a hanya sai yayi masa kallon tsaff dan kayan da ke jikin sa, sai dai babu wanda ya tanka masa, ya kusa karasawa ya hadu da wasu yan samari biyu a kasan wata bishiya kusa da gidan sa, ya tsaya suka gaisa duk da suma gaisuwar daidai sukai masa.
Ganin an kusa salar magariba ya sa bai tsaya ya cika su da surutu ba ya shige gida abun sa.
Koda ya shiga gida, ya saka kaya ya kuma fitowa nema masalaci, chan yaga kan ya tsaya neman masalaci sai ya sha uwar tafiya hakan yasa ya koma gida yayi sallah, bayan ya idar ya ji gidan yayi masa fadi da yawa, ya rasa abun da zai yi hakan yasa ya koma sama ya fara buga games din shaffik, har ya gaji bacci ya kwashe shi a wajen.
Tun kan asuba tayi ya tashi ya fara tulawar alqurani, sai da yayi izu biyar sannan aka fara kiran salah yayi sallah , bai tashi daga wajen ba sai da gari yayi haske. Yana tashi yaji cikin shi na kiran yunwa, ya tashi yayi kasa, ya bude fridge yaga kayan abinci, duk abin da yake bukata akwai shi a kitchen din nan ya hau girki, wajen awarsa biyu a kitchen din ya girka wannan ya ajiye wannan, wata macen ma ba zata iya girkin da ahmad ya iya ba.
Sai dai kafin ya gama yayi wa wajen kacha kacha, babu alamar tsafta a wajen Ahmad ko kadan, dan ya hautsina kitchen din gaba dayan sa.
Yana gamawa ya fito ya zauna zauna kan dinning yaci kayan sa sannan ya barsu a wajen ba tare da ya kwashe ba ko ya wanke ba, ya hau yayi wanka, wajen zabar kaya ma sai da aka bata waje sannan ya samu ya saka kaya, zuciyar sa sai zulumin zuwa yaga Nadiya take dan shi babu aiki a tare da shi.

Kai tsaye rafi yayi ama bai ganta ba, ya sha tsayuwar sa dan ya dade hakan yasa yace bara yaje gida ki zaici sa'a ta fito ya ganta.

Har ya kusa kaiwa lungun su ya hango ta tana tafe cikin rangwada da yanga da salo irin na nadiya da katuwar kwarya a kanta da tafi karfinta dan rinjayar ta take.
Da gudu ya karasa wajenta cikin fara'a da murmushi da jin dadin ganin ta ya dauke mata kwaryar kanta dan ya rage mata nauyi, ta dago da sauri dan ganin waye dan ta baya ya dauke mata kwaryar, tana ganin shi suka hada ido tayi saurin dauke kai ta cigaba da tafiyar ta ba tare da tayi masa magana ba.
Yayi turus yana kallon ta ba tare da yace komai ba, sai kuma yabi bayan ta, har suka isa rumfar wani gida basu cewa juna komai ba, ta juyo tace bani kaya na, sai a lokacin yace mata
Nadiya lafiya na miki wani lefi ne, meya same ki, Nadiya....
Nidai ka bani kayana idonta yayi narai narai kamar zatayi kuka, ba shiri ya dora mata akwai ta shige ya bi bayan ta da kallo.
Duk yanda akayi ita da inna tani ne ko mado hakan yasa, ba shiri ya dau kafafun sa ya koma penthouse dinsa.
Yana shiga ya rasa abun yi dan ahmad mutun ne da baya son kadaici shi dai ya ganshi cikin mutane shine farincikin sa, hakan yasa ya kunna Tv ya sha kallon sa yana yi yana kyalkyala dariya kamar cikin sa ya kulle, ya duba agogo yaga duniyar ma ai bata tafiya dan har yanzu karfe sha biyu batayi ba, hakan yasa ya koma daki yayi bacci har azahar.
Bayan ya kamala abun da zai yi ya ci abinci dan ahmad akwai cin abinci ba kamar shaffik ba da abinci bai dame shi ba.
Sai da yaci ya koshi ya dawo fallo din kasa yayi rashe rashe, ya hango computer din shaffiq da ya jona a chaji, ba shiri ya zabura ya dako ta, ya bude yaga yana kan pictures ne ya rufe computer din.
Nan yaga videos din taron bude company da aka yi, gashi shi da Attahir ga kuma mummy, ga kuma mutanen wajen aikin su, yaji an kira shaffik a cikin video din ya tashi yaje ya bada bayanai , ya kalle shi yaga wannan ai shine, toh ya akai bai san anyi ba, wallahi babu ko tantama, shine, sai kuma yace ama ni sunnana ahmad ya akai ya zama shaffik, ba shiri ya hau sama ya dako wayar shaffiq, ya lalubo Attahir ya kira shi...
Attahir na dauka yace
hello nigga ya sabon guri...
Bai bashi amsa ba ya tafi straight yace,
Attahir akwai wani mai kama da ni da ka sani shaffik...
Attahir yayi shiru sai kuma yace..
Kaga wani mai kama da kai ne mai suna shaffik a kauyen...?
A'ah ina tambayar ka ne akwai ko babu...
Chan yayi shiru sai kuma yace toh nidai bansan wani mai kama da kai ba mai sunnan ka kuma ba...
Kasancewar ba abun da yake son ji kennan ba hakan yasa ya kashe wayar kawai.

Ya tashi ya hau sama aguje...
Jakar system dinshi da documents dinsha ya dako ya watsa su akan gado yana dube dube, a dako ipad din shi ya kunna yaga pictures dinshi da mutanen shi, ya duna contacts din wayar sa yaga babu number wanda ya sani banda Attahir da mummy....

Tabassss ba shi bane wannan akwai wani a tare da shi da yake amsa suna shaffik...
Toh waye shaffik?? meyasa suke raba jiki daya da shi?? Shin WAYE SHI???

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now