Twenty five

146 15 0
                                    

Episode twenty five
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Inda shaffiq ke morar Ahmad shine wajen girki, dan idan ahmad ya tashi yin girkin shi bayayi kadan sai yayi da yawa kala kala ya sa a fridge, hakan bazai sa gobe idan ya tashi ya kuma girka wani ba, dan ya bawa abinci wani mahimanci mai karfi shiyasa jikin shi har wani kiba yake yi.
Idan yunwa ta kama shaffiq kai tsaye zai yi kitchen dan bashi da matsala ta wannan ban garen.
Haka suke rayuwa idan shaffiq ya siya kaya ko awani abu mai mahimanci sai ya nana masu takar da na "kar ka taba mun kaya!!!"
Shi kuwa ahmad babu ruwan sa sai dai ya kalla kawai ya girgiza kai ya wuce dan shi bai damu shaffiq ya taba masa nasa kayan ba, komai nasa is available bashi da wata rowa ko nan nan da kaya.
Shi kuwa Attahir tun ran da yabar gero ya gane wa idon sa lamarin shaffiq bai kuma dawowa ba, sai dai waya da Ahmad ke isar sa da shi idan har wani abu ya shige masa duhu ta bangaren aiki da sauran yan uwa toh Attahir zai nema, tun yana dari darin yi masa magana har Attahir ya saki jiki da shi.

Mummy ce har yanzu bata san halin da dan a ke ciki ba, dan Attahir ya dade da korawa ahmad warning din kar ya sake ya bari mummy ta gane shi, ba ma haka ba kada ya bari kowa ya gane.

Hakan yasa bawan allah ahmad ke ta kokari iya bakin kokarin sa, sai dai har yau mama ya kasa fita daga bakin sa.
Idan mummy ta fada wa shaffiq abu tazo ta tambayi Ahmad sai ya kasa tunawa tun da bashi aka gayawa ba, sai dai yayi ta kame kame.
Hakan ke bawa mummy haushi dan wannan mantuwar tasa tayi yawa.
Akwai ranar da ahmad ya taba yi wa mummy zancen Nadiya, ama koda zancen ya kuma tashi ta tambayi shaffiq shaffiq cewa yayi bai san zancen ba.
Nadiya da shaffik kuwa sai dai haduwar hanya shima sai idan hanya ta hada su, idan tayi hanyar office din su, dan saboda tsabar tsoron sa da take ji ko hanyar batayi gudun kar su hadu.

Yau da safe shaffiq na tashi daga bacci yayi mika zai shiga toilet, yaci karo da wasu manyan ledoji bugun company dinsu, ya bude yaga mayuka ne da turaruka da sauran kayan kwaliya na company din su,
Ko bai tambaya ba yasan na waye, ahmad na bashi mamaki wani sa'in, yanzu wadan nan kayan zai kai wa waccan yar kauyen...
Ya ja wani mugun tsaki ya shige toilet.
A toilet yayi tunanin mai zai hana ya dauki kayan nan ya kaiwa Nadiya ko zai ji wani abu daga gurinta, dan gane da Ahmad dan tafi sanin shi akan kowa.
Yana fitowa ya shiga kitchen yaci abinci sannan ya koma ya shirya tsaf cikin yanayi da style irin nasa wanda ya banban ta da na ahmad, ya fito.
Kai tsaye gidan su Nadiya yayi, ya dade a kofar gidan a tsaye, ama babu ko dan aiken da zai aika, kasan cewar yanda garin yake da rashin mutane, shi bai ma san me ya kawo shi ba wannan ai zubar da aji ne a ganshi a kofar gidan nan,
Har zai koma yaji an bude langalangan kofar gidan, ta fito cikin dan karamin hijabinta da yasha tafkeken faci a gaba, fuskarta tasha kwaliya da dige dige irin na fulanin gero, da alama sauri take yi.
Bai taba ganin ta da mayafi ko hijabi ba ko cikin complete riga da zani ba sai yau, ba musu duk da dige digen dake fuskar ta da kuma kayanta da suka kode tayi kyau sosai dan Nadiya yar kyakyawar yarinya ce...
Karon da sukayi da idanu yasa tayi saurin ja baya, zuciyar ta na dukan tara tara....
Idanun da ya kafa mata, yasa tayi saurin kauda kai....
Mai ya kawo shaffiq nan kuma??
Ta fada cikin zuciyar ta....
Lafiya.... ya fada cikin kakaurar muryar sa...
Ta dago ta kalle shi cikin sanyi tace ina wuni tana kokarin kamo nutsuwar ta.
Ya amsa da lafiya lau...
Kin yi mamakin gani na ne?
Har zatace a'ah sai kuma tace eh.....
Ledar ya mika mata tare da daga mata gira alamun ta karba...
Binsa tayi da ido tana mamakin abin da yake nufi da hakan...
Ganin batada niyar karba yace
Karbi mana jikin yanayin zafi....
Ba shiri ta sa hannu ta karba jiki na rawa....
Ahmad ne yace na kawo miki,
Ahmad??
Jin sakon daga wajen sahibinta ne hakan yasa ta danyi murmushin da batasan tayi ba, sai tuntar kanta tayi da cewa angode allah saka da alheri.
Har zata koma ciki yace,
Kinga....sai kuma yayi shiru
Ya sauke ajiyar zuciya yace...
Kinga ina so ki fada mun duk abin da kika sani dangane da Ahmad?
Gyara tsayuwa tayi tare da kallon sa a karo na farko da bata razana ba...
Rasa abun da zatace tayi sai kuma tayi saurin sun kuyar da kai tare da dan ja baya...
Meye tsakanin ku??
Ya kuma jefa mata wannan tambayar...
Ta kuma dagowa ta kalle shi, tayi tsuru tsuru kamar wada aka ce idan bata amsa ba za'a zane ta...
Ganin tana bata masa lokacin ya kuma daka mata tsawa tare da fadin "ke ba magana nake miki ba" !!
A gigice tace wallahi ni babu abun da ke tsakanina da shi sai mutunci,
Mutunci??
Ta gyada masa kai alamun eh...
Kasa resisting temper dinsa yayi da ya ja tsaki kawai ya bar wajen....

Wani mugunun haki ta saki ta fitar da wata iska mai zafi ta tsuguna a wajen ta da dafe kirjinta ji take kamar zuciyar ta tayi tsake ta fito tsabar tsoron sa da take ji.

*****************************************************
To be continued  insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now