Twenty eight

131 15 2
                                    

Episode twenty eight
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Toh fah annan Allah yake ikon sa, dama ance a dare data Allah kanyi bature, wannan haka yake domin kuwa a dare daya komai ya sauya a wajen shaffiq, da ya kulle idon sa murmushi Nadiya ke fadi masa, hoton ta kawai yake gani tana murmushi, bai taba ganin wannan bangaren nata ba,ashe yarinya ce mai nutsuwa, mai tatausan lafazi, ga kyau ga iya magana cikin sanyi ga kunya...

Da yar kalon kallo ke hada su daga nesa, babu abun da ya hada su sai ina wuni da angode, ashe haka take...
""Shiyasa bature yace dont judge a book by its cover""
Da kyar ya samu bacci ya ziyarce shi, ya sa alarm zai tashi da wurwuri dan ya garzaya asibiti.

Da sassafe ya tashi ya kintsa ko breakfast bai yi ba ya baro gero, yana zuwa kofar gidan abba khalid ya kira Attahir ya fito, duk da Attahir na da abun yi haka ya bar schedule dinsa ya bishi suka tafi asibiti...
Har sun dau hanya Attahir ya ce masa toh kai an taba zuwa asibiti haka kawai ba appointment, ba ma haka ba idan munje wajen wane likita zamu...
Ya kalle shi ta side mirror yace wajen likitan mahaukata mana, wa kuwa zai ita dealing da wannan idan ba mahaukaci irina ba..
Attahir yayi dariya yace au likitan mahaukata shima mahaukaci ne...
Yayi smiling shima sannan yace haka ake cewa...
Ka yarda haukan kake yi kaima??
Bai kula shi ba shi dai dan baya son yin maganar ma shi.
Suna cikin tafiya shaffiq ya kalli Attahir yace saura na ji wannan zancen bakin mummy..
Shima bai kula shi ba ya zaro wayarsa ya hau kiran abar kaunar sa Lawisa.

M.H private hospital suka isa, suna zuwa suka nemi appointment da Dr Lattif domin shime kwararen likitan kwakwalwa a asibitin, aka basu takarda aka ce su jira nan da 30 minutes za'a kira shi.
Shidai Attahir sai faman waya yake yi shi kuma shaffiq zuciyar sa sai faman doka wa take yi gudun kar a fada masa abin da zai fi karfin kansa ne ke damun sa...
Sai uban gumi yake hada wa, tsoro duk yabi ya dabai baye shi...
Duk yarinyar da ta gilma ta gaban sa sai ya tuno fuskar Nadiya hakan yasa abun yayi masa yawa.
Chan aka kira shi...
Har ya mike zai shiga yaga Attahir bashi da niyar tashi hakan yasa ya manna masa wata harara tare da fadin me kake nufi ni kadai zan shiga...
Ba shiri Attahir ya kashe wayar suka shiga ciki,
Attahir ya sami kujerar da ke gefen hagu ya zauna shi kuma shaffiq ya zauna a ta dama da take kallin likitan.
Bayan sun gaisa likitan ya ke tambayar su mai ke tafe da su, kuma waye patient din dan ya bai gane ba.
Shaffiq yayi ajiyar zuciya yace nine Dr.
Dr. Ya kalli file din shaffiq yace shaffiq khalid me ke damun ka?
Ya dan yi shiru dan shi bai ma san ta inda zai fara ba, fatan sa kawai likitan nan ya gane abun da zai fada..

Ya kuma sauke ajiyar zuciya yace Dr ba ni kadai bane a tare da ni, ina da wani a tare da ni da muke rayuwa tare.
Jikina komai nawa da shi yake amfani, abun da yake ban ban tamu shine, suna, hali, da kuma mutane.
Sunnan sa Ahmad, kawata kwata halayensa ba irin nawa bane, mutanen sa daban wanda yake ma'amala da su.

Dr lattif ya juya biron hannun sa sanna yace
Uhmm tsawon kwana nawa kennan da gane ba kai kadai kake rayuwa ba??

Wata hudu zuwa biyar kenan..

Toh ya akai kai ka gane hakan??
Toh da farko dai, abun da na fara lura da shi shine, kaya na aka fara lalata mun, idan yana neman kaya ko idan yaci abinci ko yayi girki sai ya haustina waje gaba daya, wanda ba halina bane.
Na biyu mutane, mutane da yawa yanzu a gero da ahmad suke kira na,wajen aiki da dokokin sa ake amfani, da yanda yake ma'ala da mutane duk wanda ba haka nake tafiyar da al'amura na ba.
Style dina da nasa ba iri daya bane, ni ma'abocin sa manyan kaya ne shi kuma yana son sa kananan kaya hakan yasa yaje ya siyo su da yawa yazo ya ajiye mun a gida.

Toh ya ake kake juyewa ka zama shi...???
Kamar yaya Dr??
Ma'ana babu abin da ke faruwa idan zai zama kai ko kai zaka zama kai...
Eh toh, nakan sami matsanan cin ciwon kai mai tsanani na yan sakkanni da baya kai minti daya daga nan kuma bana sake tuna abun da ya faru...
Idan zaka dawo dadidai kuma fa???
Nakan dawo daidai idan yayi bacci, ko kuma idan na sami matsanancin ciwon kai.

Shi ciwon kan hakanan yake zuwa babu abun da ke kawo shi????
Idan na bige haka, ko aka bata mun rai haka, ko kuma duk ramar da na dawo gero, ko kuma haka kawai yakan zo ma....
Yaushe ka fara samun shi wannan ciwon kan...
Ya danyi shiru sannan yace ranar da na fara zuwa gero naje zan duba wata supply din su, anan na fara samun wannan ciwon kan, daga nan ban sake sanin abun da ya faru ba sai ganin kaina nayi a jike alamun fadawa cikin ruwan nayi....

DR lattif yayi ajiyar zuciya ya kalli shaffiq da yayi tsuru tsuru yana bada jawabi hankalinsa daga gani a tashe yake sannan ya janyo takarda yayi rubuce rubucen sa sanna ya dako wani kati ya hada akan takardar ya mikawa shaffiq.

Shaffiq am sorry to say ama ciwon ka babba ne i cant handle it, yana bukatar ka ga babban likita da ya kware a wannan bangaren, dan gskia ban taba ganin mai irin cutar ka ba sai dai a litatafai da muna makaranta.
Saboda haka ga wannan number din da report din History din da ka bani, na rubuta.
Zaka ke ka sami Dr Fauziyya D sulaiman anan asibitin dala na nan kano ranar monday  next week.
Zan mata magana insha allahu, idan yaso idan kaje sai kayi mata bayani kamar yanda kayi mun, insha allahu za'a samu dacewa.
Kar ka damu....

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now