Twenty four

146 13 0
                                    

Episode twenty four
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Cikin yan mintina chef Ahmad ya gama jera musu girki a kan table, sai dai me? Anyi kacha kacha da wajen yanda aka saba, yana yi yana tambaya Attahir budurwasa lawisa, Attahir na bashi ansa daya bayan daya...
Karshe ji yayi kamar mafarki yake yi hakan yasa yayi saurin mikewa yace shi goda zai wuce yana da abun yi....
Yayi yayi da shi ya tsaya yaci abinci ama yaki dan cin abincin aljani ba karamin tashi bane...
Haka ya fito ya bar masa gidan ya karata shi kadai...
******* *************
Saida yaci ya koshi sannan ya sa sauran fridge ya kuma shiryawa cikin shiri sannan ya fito, kai tsaye bai tsaya ko ina ba sai gidan su Nadiya, ko sallama bai yi ba ya kutsa kai cikin gidan.

Tana tsakar gida tana shara, taji sallamar sa akan ta, tayi saurin dagowa suka hada ido, da tayi saurin dauke wa tare da fadin yau kaine har gida....
Jin murya a tsakar gida yasa inna tani ta fito daga rumfarta tana faman gyara zani....
Laaaahhhh
Lalle lalle
Mutanen burni ne ashe barka da zuwa...
Ta rasa sunnan da zata kama
Ganin hakan yasa yayi dariya yace....
Inna Ahmad ne....
Tayi dariya tare da shinfida masa tabarmar kaba tana,
Wanga kama taku wallahi mancewa na kanyi, bana iya tantance ku,
Yayi dariya shima ya kalli Nadiya da take ta sharar ra ta ma manta da zuwan sa...

Bayan sun gaisa yake ce mata ai mai jiki yazo dubawa ya kufan jikin nasa...

Inna tani ta sauke ajiyar zuciya tace ahmadu bamu cewa komai sai Alhmdulillahi, sai kuma gode maka kai da dan uwanka, ama wanga jiki na mado ba wai samun waraka bane, nan ta kwashe dukanin labarin abun da ya faru a asibiti, har salamar su ta fada masa.
Haka dai sukayi ta tataunawa...
Ita kuma Nadiya tana gamawa, ficewa tayi taje bakin motar sa ta tsaya dan kuwa idan yakumbo ta ganta wani aikin zata kuma sata ba tare da ta yi magana da ahmad ba.

Sai da ya gama hira da inna tani har ya bata abun rikewa a hannu sannan ya fito.

Koda ya fito jikin sa ya bashi tana wajen tana jiran shi, hakan kuwa tana bakin motar sa, sai faman duba fuskar ta take yi a jikin mudubin motar tasa....
Yafi munti uku a tsaye a kanta ama sai faman gyara fuska take, da ya gaji yayi mata yar tsawa a kunne da tayi saurin razana har tana neman gudu...
Shi kuma ya kyalkyale da dariya,
Ta dan bata rai ta dan zumbiro baki tare da fadi wallahi he na rama☹️
Ya kalle ta cikin mutauwa, yayi murmushi ya na yaba kyaun yarinyar nan acikin zuciyar sa,
Yayi murmushi tace kin chanza dankwali, kin dan sa hoda, kin dan sa jambaki, duk kafin ki fito....
Tayi saurin rufe fuska tare da juyawa...
Binta yayi inda ta juya ya matso daidai kunnen ta yace, ni kikayiwa ko kuma wajen saurayin ki zaki daga nan tunda naga ma bakya murna da zuwa na...

Bata kulashi ba ya cigaba da yan maganganun sa, indai wajen saurayin ki zaki wallahi yanzu zan shiga in gaya wa inna tani...

Ta juyo ta murguda masa baki tare da yi masa harara cikin salo na yanga...
Yayi murmushi da dariya taso kwace masa yace au bazaki fada mun ba ???
Bara kiga....
Ya juya yayi cikin lungun da saurin sa
Ganin bashi da niyar tsayawa si kara lulawa yake kuma tasan ba karamin aikin sa bane dan zai iya...
Ya juyo a karo na farko, da yayi mata nisa sosai yace
Bazaki fada ba ko....
Ba shiri tace
Kai nayi wa....
Ya sauke lumfashi tare da yin ajiyar zuciya, suka tsaya suna kallon juna cikin nutsuwa, ya fara taku a hankali har ya karaso inda take suna kallon juna, ko wane da abun da yake sakawa a cikin zuciyar su, kai kana gani kasan wannan kallon yana da ma'ana.....

Tayi saurin sun kuyar da kai kasa, har yazo ya tsaya a kanta....
Ta dago a hankali taga murmushi a fuskar sa bakin sa na motsa kin yi kyau sosai...
Murmushi tayi ta kalli kayan da ke jikinta...
Rigar attanfa shudiya ce a jikinta sai zani mai fatsi fatsi kore a jiki, sai bakin dankwalin ta da ta daure shi jelar tayi baya.

Kin kara fari kinyi kyau, duk saboda kin sami saukin mado ko...
Tayi dariya tace a'ah wallahi
Haka yasa ta a gaba yayi ta tsokanar ta, dan halin sa kennan shi, ita kuma sai dariya take tana shi wallahi ya cika wasa..
____________________________________
BAYAN WANI LOKACIN

Haka Ahmad da Nadiya suka cigaba da shakuea dan indai yana nan to yana wajen Nadiya, kowanen su sun sami mazauni a cikin zukatan su, dan kuwa Ahmad bashi da abin da yake faranta masa rai face Nadiya, itama kuma ya zame mata silar wanzuwar farinciki a rayuwar ta, dan kuwa tun ranar da suka hadu kullun cikim farin ciki take.

Yanzu har ta kai ta kawo har gurin inna tani ya sami shiga, dan wata soyyaya ta tsakani da allah ke tsakanin inna tanni da Ahmad, bawai dan abin hannun sa ba, ba kuma dan komai nasa ba, dan da farko Nadiya tayi zaton da kudin sa ko dan yana bata wani abun take son shi, ama sai taga abun ba haka yake ba.
Ahmad mutun ne mai raha da dariya kullun cikin nishadi da jin dadi yake babu abun da ke bata masa rai a duniya, kowa nasa ne kuma.
Duk wata mugunta da zalinci na inna tani idan taga ahmad sai ta tsagaita da ita, domin kunyar sa take ji.
Shima yana son inna tani sosai da idan har yazo sai yasa ta siya masa alalan gwagwani dan mayan alalan gwagwani ne da kwadon rama, duk wata gargajiya to Ahmad ya bita dari bisa dadi.
Yanzu idan yazo idan sun gama gaisawa da inna tani sai ta tashi ta basu guri, ko kuma idan yana son taokanar Nadiya sai yace ai shi ba wurin Nadiya yazo ba wajen ta yazo.
Har yanzu basu taba furtawa juna kalmar so ba, saidai da ka kalli idanun su zaka ga soyayya a cikin kwaryar idon su, ta ruga da ta gama zaga jinin jikin su.
Bashi da wani lokacin sai na Nadiya da ya rikide ya dawo ahmad to babu inda zaki neme shi sai gidan su Nadiya.

A da yakan dauki kwana uku zuwa hudu kafin ya rikida ama yanzu shaffiq baya kwana biyu kwarara a matsayin sa na shaffik, ya zamanto tanzu Ahmad ke yi masa jagoran rayuwar sa.

Ama me? Kowa rayuwar sa yake yi, aikin campany kawai ke hada su, banda haka abokai mutane kowa da nasa, sai kuma kudi da mota da suke amfani da shi tare.

Tun shaffiq yana bala'in kudin sa har ya gaji ya dena, ya zubawa sarautar allah ido.

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now