Twenty-one

151 13 0
                                    

Episode twenty one
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Ya danyi shiru sai kuma ya maze ya juya ya kalli Habubakar da ke bin su daya bayan daya da kallo, yana mamakin wannan yanayi.
Guri ya samu kusa da shi ya zauna tare da fadin Yaya mutumin ya naji kayi shiru,,
Auu ai ma zata ka mata da zama ne,shi yasa nayi maka shiru.
Yayi dariya ya mike tare da fadin Nadiya ya mai jiki....
Ta amsa da da sauki.....
Allh ubangiji ya kara sauri bara na dan zaga nadawo...
Haka ya fita ya barsu a dakin su biyu sai mado da ke kwance
Jin shirun da sukayi yayi yawa hakan yasa tace
Ahmad ba dan dan uwanka ba, da ban san inda zansa kaina ba, dan kuwa da inna tani cewa zatayi ni na kashe mado.
Da na zata kaine sai da kuma naga yanayin sa sannan na gane ba kai bane
Yayi shiru yana kallon ta kamar mai daukar darasi dan kuwa yanda take magana acikin nutsuwa da tauna kalame ke burge shi.
Ta dago ta kalle shi yanda ya kafa mata idanu hakan yasa tayi saurin kauda ido tare da fadin ya kayi shiru?
Kasa cewa komai yayi sai kuma ya mike ya girgiza kai tare da fadin ya kamata na wuce, naga inna ta dan dauki lokacin,
Bai rufe baki ba sai gata ta shigo,
Ta bashi hakuri, yake cemata ai tafiya ma zaiyi, tayi masa godiya sosai takuma ce ya taya ta yin godiya ga danuwansa.
Har bakin kofa ta raki shi sannan ta koma, zuciyar ta fara sal da ita cike da farinciki.

Ganin yanma tayi hakan yasa suna fita hanyar gero suka dauka, zuciyar Ahmad Sai murmushi take sa shi musan man idan ya daga kai ya kalli kansa a mudubi, ga wani uban gudu da yake yi cikin nishadi da farin ciki...
Habubakar ya tambaye shi lafiya, ya juyo ya kalle shi yayi murmushi kawai ya maida idon sa kan titi.
Suna isa ya faka kofar gida Habubakar ya bude masa gate ya shiga da motar sa, bayan ya fito sukayi sallama ya kama gaban sa shi kuma ya shiga ciki.

Yana shiga yayi gado dan bashi da abun yi, da ya rufe ido sai ya ganta tana masa murmushi, kyawawan hakoranta da dan dimple dinta sun bayana, hakan yasa yayi ta wasa da bude idon sa yana rufewa.

Wani irin abu yake ji dan gane da nadiya,da har yanzu ya kasa gane meye shi, ita ta bude masa ji da gani, ita ce macen da ya fara sawa a idon sa ita ce mace ta farko da ya fara jin muryar ta cikin kunuwan sa, ita ce mukulin rayuwa sa dan kuwa itace jigon rayuwar sa dan kuwa rayuwar sa ta fara ne saboda ita zakuma ta cigaba da gudana saboda ita.

Chan kuma ya tafi tunanin meyasa shaffiq ya temaka mata, duk da bai san kowaye shaffiq din ba ai ba hurumin sa bane.
Babu abun da yasani game dashi sai cewa shaffik, sai cewa shaffik mutun ne da suke rayuwa tare a jiki daya.
Toh ama idan har jiki daya suke rabawa meyasa zai dunga rayuwa a matsayin shaffiq hakan bazai yuwuba ya kamata ya dau mataki, yanda shaffiq yake da iko da wannan jikin hakan shima yake da iko shima.

Da sassafe ya tashi ya shirya, ko aiki bai tsaya ba yayi kano, yana isa gida mummy ta ganshi cikin hanzari kamar zai tashi sama, tace masa me ke faruwa, ya tanganshi haka da sassafen nan.
Mama abu nazo dauka, yanzu zam koma, ya hau sama a guje yayi binciken sa ya debi abun da zai deba da takartun da yake bukata ta fito...
Har bakin mota mummy ta bishi tana tambayar sa, ya masu jiki kuwa shaffik...
Ya danyi jim ya akai ta sani sai kuma yace da sauki yanzu ma zan biya ta wajen su kafin na koma.

Yana fita banki ya shiga ya ciri uban kudi daga account din shaffiq da bazai iya dauka ta ATM ba, yana fitowa yayi supermarket ya siya kayan tea, katan din lemuka da ruwa da sauran abun da mara lafiya da masu jinya suke bukata, aka sa masa a mota ya wuce city hospital.
Anan ya sami wanda zai taimaka masa suka shiga da kayan ciki.
Ko da ya shiga inna tani kadai ce nadiya ta fita.
Cikin fara'a da girmawa ya gaishe ta, ita kuma ganin sai faman shigowa ake da abun duniya ya rufe mata ido sai washe baki take, tana fara'a ta amsa gaisuwa tasa tana ta shi masa albarkaci,
Cikin kokonto tace ahmadu ne???
Ya amsa da nine was Inna....
Ya dan sosa keya tare da fadin kamar takuce tabarkala sai da tambaya....
Yayi murmushi....
Angode angode ahmad kwarai da gaske ku yayan albarka ne haka dan uwanka ma yazo ya cika mu da abun arziki allah yayi muku albarka ya saka da alheri...
Daidai lokacin da Nadiya ta shigo kenanan,har gabanta ya fadi ta zata mutumin ta ne shaffiq yana juyowa ta kalle shi, kallo daya tayi ta gane ba shi bane,
Ya mike tare da fadin toh inna allah ya kara sauki ni zan wuce...
Ta bishi da godiya dan kuwa ban taba ganin inna cikin farin ciki haka ba, har ya fita Nadiya na bakin kofa ta bishi da kallo,
Inna ta tura ta tare da fadin shegiyar yarin yar nan ke baki san abun arziki ba wuce kije ki raka shi,
Turin da tayi mata har tana shirin faduwa,
Ta kara da shegiya tatabara

Bayan sa take bi a hankali har ya jiyo sautin tafiyar ta ya juya ya kalle ta, tsayawa yayi chak yace gskia bazaki bini a baya ba,
Ya dan yi taku biyu baya suka jera tare yace mata nazata bazaki rako ni ba.
Toh ai gashi na rako ka....
Ta danyi shiru...
Shima yana leka fuskar ta dan kanta na kasa...
Ama ni inna bata yi mun kama da me fada ba...
Ta dago ta kalle shi tare da fadin, dama ya za'ayi tayi maka,,,,,
Me kike nufi.....
Ta kalle shi tace, ai bata yiwa masu kudi, yan birni, wanda suke cika ta da kayan arziki.
Yayi dariya yace toh waye dan birnin annan kinsan na fada miki ni dan Gero ne....?
Tayi dariya tace kai matsalar ka wasa....
Ya biye mata suka yi dariya har suka kai bakin mota, tayi masa godiya sosai ta koma ciki.

Tana shiga inna tani ta sauke ta da
Ke dan uban ki yau sai kin gaya mun ina kika samo waddan nan mutane, bin maza kika fara yi, naji ance yan birninsun fara shigowa gero ashe su kike zuwa kina like wa ko??????

*****************************************************
To be continued insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora