Five

274 24 3
                                    


Episode five
WAYE SHI(shaffik ko Ahmad)
Na: Bintnagz (Hasna mansur nagoda)
Wattpad @bintnagz

""Da sunnan allah mai rahama mai jin qai
Ya ubangiji duk wanda ka bawa ikon karanta wannan littafi karanta nawa allah ka tabatar da albarka a gareshi da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na duniya,shedan,aljanu da maqiya....
Ka kuma sa ya karu da wani abu daga cikin wannan littafi.
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ
Bayan shekara hudu....
Yau shekara shaffik biyar a duniya, ya girma yayi wayo dan har ya shiga makaranta, da abba khalid zaisa dansa makaranta Attahir tare yazo yadau shaffik ya saka su tare dayake tsiran su kwana daya ne hakan yasa ake ce musu yan biyu, ga sunnan abba khalid suke amfani da shi duk su biyun, da yake ta ruga tayi rantsuwa shaffik bazai yi amfani da sunnan mahaifin sa ba..
Hakan yasa suke amfani da Attahir khalid
Da kuma shaffik khalid.
Zancen uban sa kuwa bai san ubansa ba dan shi a zaton sa abba khalid shine ubansa.
Yau shekara biyu kennan babu Ibrahim babu labarin sa, abba khalid yayi yayi da ita a raba auren ama taki, ita kanta ta rasa dalilin yin haka, ama kawai aranta bata son yin hakan, ko da taje gidan su Ibrahim babu wanda zatayi wa magana sai baban su domin kuwa innarsu tana ta tabin kwakwalwa bata da hankali sosai. Baban kuwa babu abun da zaice sai dai tayi hakuri tayi hakuri allah yana tare da masu hakuri, ita a zuciyar ta takan ce toh wai yaushe zata ga karshen wannan hakuri da ake bata...
Ta tatara komai ta watsar, ta cigaba da rayuwar ta sabuwa cikin walwala tunda yazu babu Ibrahim bale ya takura mata,ta sami sana'ar saro mangyada ta na bayar wa a shaguna kanana na cikin unguwa, har gida ma ake biyota a siya, hakan yasa kudi ya zauna mata, Alhmdulillah ga kuma abin da abba khalid ke bata.

Wata rana suna kwance tskar gida tana korewa shaffik sauro dan yayi bacci, tana sauraron radio, taji motsin kofa...
Kamar wanda aka jefo daga sama ya shigo, yayo kanta duk a yamutse kamar wanda karnuka suka biyo, yana hakin yace
ke bani abinci!
Tayi banza kamar batasan da iskarsa ba...
Ke ki ban abunci nace....❗️
Ta dago a fusace tace kasha wani abune?
Ta dago kai ta laleshi
tana dagowa taga sai layi yakeyi ga warin sholi da ya dunkule a tsunma, daya hannun kuma sugari ce yake zuka,
Tayi saurin toshe hanci tana ta'awizi da neman tsari daga gare shi.
Ki ban abunci nace malama...ko bakyajine...
Babu!!!! Ta fada a hasale
Ka siyo ka ajiye ne, kaje can idan kake ci da kaci mana, ni zaka zo ka tambaya abinci bayan ka shekara uku zabona da ganin ka, akan wane dalili zan dau abinci in baka,allah ya kiyaye!
Ke kin karo wulakanci fah, ya fada cikin yanayin maye...
Ba shiri ya zaro belt ya bita da shi har daki,
Shaffik ya farka a furgice yayi dakin yaga ummansa na neman temako, shima kuka ya fashe da shi ya je ya dukunkune ta....
Sabi da tsabar rashin imani na Ibrahim har shi ya hada ya lafta iya son ransa , yana gamawa ya sakar musu amai a wajen kuwa.
Nan habiba taga lamarin ya karfafa hakan yasa ta tsaida sallah da rokon ubangiji, dare da rana bata da aiki sai bautar allah da ibada.
Cikin rokon allah, Aka ci sa'a kuwa sai allah ya tsaida hankalinsa waje daya, kullun yana gida, idan ya fita ma toh komai dare zai dawo.
Mai yakon abu yayi sauki ama abun kara tabarewa yake yi dan yanzu suna zama waje daya abu kadan ya hau zage zage da masifa , da gori, kuma idan ya tashi a gaban shaffik yake cin zarafinta ya kuma zage ta iya san ransa idan ta kama ma harda duka zai mata a gaban shi watarana har da shi yake hadawa.
Watarana shaffik ya dawo daga makaranta tun a bakin kofa ya jiyo ihun maman sa ya shigo a guje dan taimaka mata, yana shigowa kuwa ya ga tiyo din ruwa da aka yanka a kasa ya dauka a shiga cikin da shi, ya tarar da su tsakar gida, Ibrahim ya hau ruwan cikin ta sai lafta yake ba, shaffik ya zuciya yayi wani uban ihu, ba shiri ya hau zabga wa uban yana ka sakar mun umma ta, ka dena dukan umma ta, uncle din mu yace ba'a dukan mata, uncle dinmu yace ba'a dukan mata, da shaffik ya zubawa ibrahim daya a keya ya zabura a fusace ya dago ya hanka da shi yana dan uwarka ni sa'an kane
Luuuuuuu, shaffik jiri ya debe shi yayi losing control da balance sai timmmmmmm kake ji ya hada kansa da bango...
Kan kuce mai jini ya malale wajen,,,,,,,
Habiba ta yo kansa da gudu tana ihu, shima Ibrahim yana ganin haka sai ya fice a guje....
Shaffik shaffik !!!!!!!!!!!abbana lafiyar ka, inalillahi waina ilaihi rajiun abbana dan allah ka bude idon ka....
Ta dago kansa taga jini kawai ke bulbula hakan yasa ta dau hijabi tayi waje a guje, taje shago ta ari waya ta kira abban khalid ta sanar da shi maike faruwa....
Cikin mintina sai ga abban khalid, bai ko jira jin mai zata ce ba ya dau yaron sai asibiti....
Yaron ya zubar da jini over dan kan aje asibiti jikin habiba yayi shagab da jini...
Suna zuwa aka duba shi likitan yace emergency surgery zasu shiga da shi dan bayan da jinin da yake zuba wani ya taru a kwakwalwarsa da idan ba'a bude ba zata iya dena aiki....
Cikin gagawa suka kira likitocinsu da sauran ma'aikata aka bude kwakwalwa shaffik akayi draining wannan jinin.
Awa hudu aikin ya dauka aka fito da shi, har yanzu baya hayacin sa, tun da aka shiga da shi habiba ta bude sabon babin kuka, tana tsinewa ibrahim, abba khalid kuwa fada ya hauta da shi yana duk da ta yarda an raba auren nan tun farko da hakan bata faru ba, da basu yi wa dansu illa ba, idan har Ibrahim nada laifi toh itama tana da laifin biye masa da takeyi suyi fadan har da zaice zai dake ta, auren irin waddan nan mutanen ai ba aure bane idan bai mata illa ba to gashi sunwa dansu illa.
Kuka dai kuka dai babu kakautawa, ta dau alwashi ko duniya zata nade bazata koma gidan Ibrahim ba.
Kwanan su biyu kenan a asibiti babu ibrahim babu labarin sa, abba khalid ke ta dawainiya da su, kudin asibiti kudin magani da abinci duk shi da matarsa suke kawo musu.
Tana zane kusa da shi tana dan mamotsa masa jikin sa ta ga ya fara motsi da yan yatsun kafarsa, wani dadi ya ziyarci zuciyar ta, sai chan kuma ya soma bude idonsa...
Cikin murna ta fita ta kira likita yana zuwa suka kara yi masa wasu alurai sannan sukace zai dawo a hankali, yanzu farfadowa kawai yayi ama ba lalle ya gane ta ba bale yayi magana.

*****************************************************
To be continued on Saturday insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now